← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 134

Sashe 76

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin motsin an buɗe ƙofa ya sanya shi ɗaga kai ya ga me shigowar, babu tsammani ya ga safiyya, tana sanye da doguwar riga straight gown, sai mayafinta a kafaɗa da jakarta, ta shigo bakinta ɗauke da sallama.

Ya amsa mata tare da mayar da kansa ya kifa.

"Yaya raihan, barka da rana?"

"Yauwwa sannu"

Ta nemi wuri ta zauna ta ce  "Gidan su wata ƙawata na je, a nan tsukin ne, na ce bari na biyo mu gaisa"

Yayi shiru bai ce mata komai ba.

"Are you ok?" Tayi maganar tana kai hannu goshinsa, ganin yana gumi duk da akwai sanyi a office É—in.

Rau ta ji goshin nasa ya É—au zafi, ta ce "Subhanallah, yaya raihan baka da lafiya ne? Jikinka zafi"

Ya ɗago a hankali ya ce "Safiya, ki tafi gida Please, ki ƙyale ni"

"Amma ya zan tafi na barka a wannan halin?"

Kallonta yake yi, yana tunanin dama ummi ce a zaune a gabansa take yi masa magana yanzu.

"Ki tafi na ce" yayi maganar a ɗan hasale, tare da jin haushin yadda ya ta tsare shi da ido, saɓanin ummi da ba ta iya ƙura masa ido haka, sai tana yi tana kawar da kai.

Safiyya ba ta fi shekaru goma sha tara ba, ummi ta girmeta sosai, sai dai shegen iyayi da rawar kai, duk in da ta zauna ba ta da aiki sai hira da samari a waya, ga shegiyar kwalliya kamar Æ´ar tsana.

Ta razana da tsawar da yayi mata, ta tashi da sauri, har ta kusa fita ya ce "Kar ki sake biyo ni office, office wurin aikina ne ba shirme ba" tayi sauri ta fice tana waiwayensa.

Ummi kuwa ta galabaita a ranar, dan bayan screening, aka ce su jira aka tura musu waÉ—anda suka yi nasara a waya, ciki har da ita, aka ce su jira ayi musu interview.

KuÉ—in hannun ummi ba zasu kai ta ci abinci ba, ga yunwa ta isheta, haka nan suka cigaba da jira.

Ba a zo kan ummi ba, sai kusan biyar na yamma, da farko bayan shigarta studion aka fara yi mata interview, a É—an tsorace take, ga yunwa tana ji, É—aya daga cikin masu interview yana cewa masha Allah muryarta mai daÉ—i.

ÆŠayan ya ce "Jin ta ya fi ganinta, wannan da radio ce irin su ne masu sauraro ke É—okin gani"

Shugaban wurin ne ya shigo, ma'aikatan suka din ga gaishe shi, yana hura hanci, ya dubi ummi ya ce "Wannan fa?"

"Sir tana cikin wanda suka tsallake screening, interview ake yi mata"

"Wannan É—in?"

"Eh sir"

"Dan Allah ku zaɓo wanda za su yi attracting ɗin mutane, ba wanda sai mun yi ta faman sanya filter muna fafutuka kan mu haska su ba, wannan shirin talabijin ne, ba na gidan rediyo ba!"

Tsit mutanen wurin suka yi, ba wannan ne karo na farko ba, amma a duk lokacin da aka yi mata, jin abun take kamar sabo, sum-sum, ta tattara kayanta, tayi waje, duk suka tsaya suna kallon ummi, shi kuma ko a jikinsa ya cigaba da maganar sa.

Ita ba ta san ma yadda aka yi ta isa gida ba, abubuwa daban-daban cunkus a ranta, ta ɗaukko gajiya da baƙin ciki, tana zuwa gida farida ta dira mata nata tashin hankalin.

"Raihan ka gani ko?, ka kori wanda zai aureni, kaima ka tafi ka bar ni, komai yayi mini zafi"

Tayi kuka-kuka iya yin ta, har ta gaji tayi shiru.

Ta wuni da yunwa, haka ta kwana da wata.

Kwanaki huɗu rabon raihan da ummi, yayi ƙoƙarin sanya abun da ta gaya masa a matsayin hujjar da za ta rabu da shi, amma shi sam bai ji hakan a matsayin hujja ba, dan damuwa yake ƙara shiga na rashin ta, ya zuba mata ido ya ga iya gudun ruwan ta, ko za ta neme shi, amma ya ji shiru.

Hakan ya sanya ya fara zargin anya ba da gaske take ba ta son sa ba, tun da ta iya gaya masa cewar su rabu, kwanaki huÉ—u amma ba ta sake nemansa ba, dan haka tsoro ya sake shiga zuciyar sa, ummi ba ta son sa.

Ƙasan zuciyarsa yana mamakin yadda ta ce masa ta taɓa aure, shi ba auren ta ne ya dame shi ba, meya kashe auren? A yadda ummi take har ace namiji ya sake ta?.

Daurewa yayi, ya sake bawa ummi kwana É—aya, ya zamana kwanaki biyar, amma shiru ba ta neme shi ba.

Kwana na biyar, da yamma ya koma gidansu ummi, sai dai ya kira wayarta amma ba ta shiga.

Yana tsaye sai ga motar dr. Raihan ya risuna ya gaishe shi, dr. Ya amsa masa, yayi parking a waje, ya shiga cikin gida.

Raihan ya dudduba, mai gadin gidan ma baya nan, yayi ta kiran lambarta amma shiru ba ta shiga.

Ya samu wuri ya zauna a ƙofar gidan, yana cigaba da dannan wayarsa.

Dr. Ya sake fitowa,  ya ga raihan, ya kalli raihan ya ce "Yarona wa ka ke nema ne? Ko wurin Abdul ka zo?"

Raihan ya ce "A'a Abba, wurin Ummi na zo"

Dr. Ya ce "Too, ummi kuma lafiya dai ko?"

"Eh lafiya ƙalau, wurinta dai na zo, na kira wayarta ba ta shiga ne"

"Amma wani abun tayi maka ne?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, ba ta yi mini komai ba"

Dr. Ya jinjina kai ya ce "Yaron kirki, ai babu lallai ummi ta tsaya ta saurareka, a yanzu mijin aure ne ya dace ya zo wurinta, ba wanda za a yi soyayya ba kawai, wannan idan ba ku yi sa'anni ba, ba zaka girmeta da yawa ba.
Ka yi haƙuri ka ji ɗana.

Cikin girmamawa raihan ya ce "Abba ummi ta sanni, akwai alaƙa tsakani na da ita, wallahi abba ba ɓata mata lokaci zan yi ba, aurenta zai yi, ina son ta wallahi".

Dr. Yayi shiru yana kallonsa, sannan ya yi murmushi ya ce "Meye matakin karatunka?"

"Na yi degree a ɓangaren Business administration, a ATBU"

"Idan da gaske ka ke zaka aureta, ranar lahadi ka turo mini mahaifinka mu yi magana da shi"

Raihan ya washe baki ya ce "To Abba, in sha Allah zan gaya masa, na gode sosai da sosai"

Dr. Yayi murmushi yayi gaba, a tunaninsa yayi maganin raihan, dan ya zata irin yaran nan ne marasa ji, amma duk da haka nutsuwa da kamalar raihan É—in.

Raihan tafiya yayi yana murmushi, yana ganin abun kamar a mafarki, yau ya tsinci dami a kala, abun kamar a shirin film, wai ya tura Alhajinsa a nema masa aure? Kai tsaye gida ya tafi.

Sai dai ƙasan zuciyarsa yana tunanin, ummi za ta amince ko kuwa za ta cigaba da gardama ne? Dan ya ga kamar ta raina shi ne a matsayin mijin aure, yayi mata ƙanƙanta.

Yana zuwa ya tafi sashin Alhaji, dan kwanakin nan kusan kullum Alhajin yana gida, ya daki sa'a shikaÉ—ai ya tarar a sashin nasa.

Alhaji Tahir ya gyara zaman tabaran sa, ya ce "Ya aka yi ne? Yanayin farinciki haÉ—e da damuwa a fuskar babban mutum"

Raihan ya je ya zauna a kusa da shi, ya ce "Kowanne akwai Alhaji"

"Bani labari"

Ya ciro wayarsa, ya nemo hoton ummi da yayi mata, lokacin da suka sayo dogwayen riguna, ya ce "Alhaji ka ga wannan"

Alhaji ya karɓi wayar, ya ƙare wa hoton kallo ya ce "Na gani, meyafaru?"

"Alhaji tana da kyau?"

Ya ce "Masha Allah, very beautiful kuwa, da gani kuma tana da kunya"

"Ita nake son aura Alhaji, zaka nema mini aurenta?"

Alhaji Tahir ya kalli raihan yayi murmushi ya ce "Babban mutum wannan ai matar manyan ce, anya ba ka yi tsaurin ido ba kuwa?"

"A'a Alhaji, ai nima babban mutum ne, dan Allah tayi? Wallahi mutuniyar kirki ce"

Alhaji ya yi shiru ya ce "Ai ni kallon sani nake yi mata ma"

Raihan ya ce "Eh, ƙawar maryam ce, amma ita ba ta girme ni ba, shekrunmu ɗaya da ita, kuma mutuniyar kirki ce ka tambayi Hajiya ma ka ji"

Alhaji Tahir ya dafa kafaÉ—ar raihan ya ce "Easy my dear, in dai kana son ta tayi mini, za a nemi aurenta in dai za a bamu"

Raihan ya washe baki ya ce "Babanta ya ce ranar Sunday wai ka je ku yi magana, gani yake yi kamar ba aurenta zan yi ba, Alhaji tana bani shawarari masu kyau, tana da kirki sosai"

"Allah ya kaimu lahadin, zan je in sha Allah, ko a lokacin suka ce sai a É—aura, Ubangiji Allah ya sa abokiyar zama ta gari ce"

Raihan ya sosa kai ya ce "Alhaji saura abu É—aya"

"Ok to ina jinka"

Raihan ya ce "Dan Allah kar ka gaya wa mami sai maganar ta faɗa, ban san yadda za ta karɓi maganar ba.
I really have to marry her, Alhaji rayuwar ummi akwai ƙalubale da ban tausayi, dan Allah ka tsaya mini"

Alhaji Tahir ya jinjina kai ya ce "In dai ni ne ka san baka da matsala da ni, ko tsohuwa ka ce kana so, zan wuce maka gaba in dai tana da tarbiyya, kuma ko a hoto, ni yarinyar ban ga aibunta ba, ko ta girmeka in dai kana son ta shikenan, ai soyayya ba ƙarya ba ce raihan, mune muke barin al'ada na rage mana jin daɗin abun da addini ya halatta mana. Allah ya sanya alkhairi ango"

Raihan ya sunkuyar da kai yana murmushi, wani irin farinciki na ratsa zuciyarsa.

Dr. Ya manta da batun haɗuwarsa da raihan, dan ko ummi ma bai nema da maganar ba, sai dai ya rage ganin gilmawarta ko a gidan, ya bar hakan a wataƙila takurar farida ce ta saka ta ƙara takura kanta.

Washegari raihan ya tafi wurin aikin Ummi, amma manager ya ce "Ai ummi yau kusan kwana uku ba ta zo ba, ni ban sani ba, ba ta da lafiya ne ko ya aka yi ban sani ba, kawai ta ce mini za ta je screening, tun ranar ba ta sake zuwa ba, na zata ma ko ba ta gama ba ne ba".

Raihan ya yi shiru ya ce "kira ta a waya ka ce ko ta dawo aiki, ko zaka koreta".
Chapter 76 · 0% Book details