Sashe 131
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su farida kuwa an kai ruwa rana, da su da mijin rahama a wurin Æ´an sanda, dan kuwa Æ´ar kwananta goma sha É—aya ta mutu, kasancewar uwarsa tana da kuÉ—i, sai kaiwa ta ke tana komowa a kan lallai sai an sake shi.
Ana wannan ƙadamin, su Alhaji Tahir suka kai kuɗin auren noor, aka saka watanni tara watan da za ta kammala karatun sakandare, za a yi bikinta da Salim.
Tun da aka saka auren nan, ummi ta dage wa noor da addu'a, tare da yi mata nasiha sosai a kan zamantakewa.
"Noor, bani da burin rabaki da anty farida mahaifiyarki ce, kuma komai ta yi miki, mahaifiyar ki ce. Abun da nake so ki sani shi ne, kar ki yadda wani ya É—auki wani abu na tsafi ya ce miki ki yi wa mijinki.
Daga zarar abun ya karye, za ki ji kunya, kuma sai mushen kare ya fi ki daraja a wurinsa.
Noor Allah bai halicci namiji dan ya bi mace ba, mace ita ce a ƙarƙashin namiji, gwargwadon biyayyarki, gwargwadon mallakarki. Idan ki ka kwantar da kai, ki ka yi addu'a ki ka miƙa lamarinki ga Allah ki nemi aljannar ki da gaske, zaki juya namiji yadda ki ke so. Wasu abubuwan sai lokacin auren yayi zan gaya miki, babu ruwanki da ɗaukar shirmen ƙawaye su gaya miki abun da ba zai amfane ki ba.
Babu ke babu yi wa miji asiri noor, asiri ba ya tasiri, ko yayi na lokaci kaÉ—an ne.
Namiji kullum shi ne a gaba, dan haka ban da É—aga masa murya, kuma ki fara yi muku addu'a samun zaman lafiya tun yanzu".
Noor ta jinjinawa ummi kai.
Hajiya kamar ta taka rawa, ganin a wannan karon Salim ya yadda zai yi aure. Kuma ta ji daɗin zaɓar noor da yayi, ko ba komai ta ga misali a kan ummi, ahalin gidan dr. Suna da tarbiyya.
Dr. Ya je gagarawa, ya duba Iya, sai dai aka tabattar masa da spinal code ɗin ta ya taɓu, ba zata ƙara takawa ba, komai sai dai ayi mata.
Dr. Ya tsorata da yanayin da ya ga Iya a ciki sosai da sosai.
Gashi babu wata cikakkiyar kulawa ta a zo a gani.
Bayan ya koma gida, ya tarar an dawo da rahama gidansa, a nan za ta yi jinya, da kamar ya ce bai yadda ba, kawai ya ƙyale su.
Ummi ta na ta Alla-Alla tayi arba'in, tana son ta je ta duba rahama, kuma ta duba jikin iya.
Sai dai shi Yallaɓai MD, lissafinsa kawai tayi ta koma turaka.
Da dr. Ya gaya wa Farida batun karɓar kuɗin noor, bala'i ta hau bala'i taƙi nutsuwa yayi mata bayani balle ta ji waye.
Hankalin kausar yayi mummunan tashi, jin an karɓi kuɗin auren noor, ita kuma ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko.
Ummi tana jikin raihan, tana ta zuba shagwaɓa, ta kalli fuskar sa tana ƙoƙarin tashi ta ce "Malam cikani na tashi, yarana jarirai ne, ba zaka haɗa ni da ƙajaga ba ban gama warkewa ba, ka sakani konika"
Yayi dariya ya ce "Ke matar so ita ce ke konika, ki yi wa duniya proving É—in ke É—in matar so ce ga raihan"
"Ni zaka yi wa wayo? Ai na riga na gama yi wa duniya proving ni É—in É—aya ce a zuciyar mijina"
"Wallahi faɗi ki ƙara faɗa, ni kyautar da Alhaji yayi miki ni na so yi miki ita, wata gigitacciyar kyauta nake son yi miki".
"Ni ba na son kowace kyauta, wuri nake son ka ƙara gyara mini a zuciyarka na miƙe ƙafata"
Raihan ya ce "Kin samu, ba kowa a ciki sai ke Salmana, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, ya ƙaro miki lafiya, ki yi ta haifo mini ƴaƴa"
Riƙe hannunsa tayi tana dariya ta ce "Ni zaka yi wa wayo, wai ba zuwa ka yi kana cewa ba ka da lafiya ba?"
Ya kwashe da dariya ya ce "Duk cikin neman hanyar tsira ne, bani da lafiya idan har ba tare da ke nake tare ba, ni a idona duk wata mace idan ba Salmana ba ba zata taɓa zama ɗaya da ke ba. Ke daban ce a kowane fanni".
Kalaman jinjina da girmamawae da yake yi mata, ya sanyata jin kamar ta fi kowace mace sa'a a rayuwarta.
***
Idris da sasassafe yana ta shirin fita zuwa karɓar wani kuɗi, sai faɗa suke yi da hindu suna zage-zage kamar ƴan tasha a kan kuɗin cefane.
Sallama aka yi a waje ya fita, ya tarar da Æ´ansanda a tsaye, ba su yi wata-wata ba suka cafke shi suka tafi da shi. Babu wanda ya san in da yake, dan babu wanda ya san kama shi.
Sai da aka je wurin Æ´an sanda, wai ana tuhumarsa da yi wa wata yarinya fyaÉ—e, an tsinci yarinyar a hanyar makarantar islamiyyar su, an yi mata fyaÉ—e an kasheta, wai shi ake zargi saboda hanyar wucewarsa ce, kuma an san halinsa na biye-biye yaran mutane.
Farida na tsaka da jinyar rahama, ɗakin da take ƙonuwa sai wari take yi, duk da yadda ake kula da ita sosai.
Inteesar ta shigo falon gidan, fuska duk a kumbure, idanunta sun yi jawur.
"Ke inteesar lafiya meyafaru?" Ta miƙa wa farida takarda, tana kuka ta ce "Hajiyar sa ta saka ya sakeni, wai sun gaji da ciyar da ni sai dai na yi kashi babu haihuwa, alhalin ɗanta ne silar komai!"
*Ina baku haƙuri, na san ina laifi rashin posting, ayyuka da bukukuwa ne suka yi yawa, ayi haƙuri dan Allah ina godiya da kulawa jama'ata ko in ce na ummi😡*
Ayshercool
08081012143
CUTARWA!
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
50
Jikin farida na tsuma, ta karɓi takardar ta duba, ga saki nan rangaɗa-rangaɗa guda biyu.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai meyasa duk maza halinsu ɗaya ne? Butulci kawai suka sani? Ita ma uwar ta sa shegiya mummuna mai baƙin hali. Ɗaukko mini wayata maza na kira babanku, na shiga uku ni farida wannan masifa hawa-hawa" ta kira wayar dr. Amma bai ɗaga ba.
Ta dungurar da wayar ta ce "Ai na sani, ba zai É—aga ba yana tare da wannan mahaukaciyar, na shiga uku ni farida".
Dr. Kuwa sallama yayi ya dawo daga salla, mariya ta shirya masa abinci, ya lumshe ido ya ce "ƙamshin abincin kawai ya sa na ji na ƙoshi" tayi murmushi ta ce "Ka dai fara ci tukuna"
Ta zuba masa faten wake doya, yana ci ya ce "Yauwwa, noor ta dawo ta zo ki fara koya mata irin abincin nan, kar tayi aure ba ta iya girki ba"
"Waye ya ce maka ba ta iya girki ba? Idan ta zo gidan nan tana yi ai, noor É—ina ta iya girki sosai ta ce a wurin ummi ta koya"
Dr. Ya ce "Ai tun da ummi tayi aure, na yi kewar abinci mai daÉ—i"
"Son kai, saboda Æ´ar ka ce ko?" Yayi dariya yana kashe mata ido É—aya.
"Yauwwa ga wayarka, an kira ban É—aga ba"
Ba tare da ya karɓa ba ya ce "Ki na tsoron kar ki ɗaga ki ji budurwa ta ce ko?"
Tayi dariya ta ce "Haba dai, ko ma budurwar ce na san ba za ta wuce maman ummi ba, maybe ko tana buƙatar wani abun ne, idan ka gama kar ka manta ka kira ta" ya ɗan ƙura mata ido. Ita har cikin zuciyarta tsakani da Allah take son su zauna lafiya da farida, wai ko ba komai ta riƙe mata ummi, daga baya ta haƙura ganin faridan ba haka ne abun a wurinta.
Ya gama cin abincin, ta kawar da kwanukan, ta zauna tana matsa masa ƙafa ya lumshe idonsa.
Ta ce "Baban ummi, ba ka ce mini komai ba a kan zuwa maiduguri"
"A'a" ya faɗa a taƙaice.
Ta sunkuyar da kai ta cigaba da abun da take yi masa.
Ya ɗago haɓarta ya ce "Kin yi fushi ne?"
"A'a, amma in anjima ma zan kuma tambayar ka, dan Allah baban ummi, ka san menene?"
Ya ce "A'a sai kin faÉ—a"
"Taron family aka shirya mana, wai an binciko tun farkon asalinmu, an gayyato mutane da dama da muke da alaƙa, ba tare da mun san mu ƴan uwa ba ne, dan Allah baban ummi"
Ya É—an yi murmushi ya ce "Na ji, amma ni kin ga bani da lokacin kai ki, bana son kuma ki hau motar haya, kin ga kina da juna biyu kar ki wahala"
"Ai zan gaya wa ummi, idan ya barta sai mu tafi da Abdul da noor, dan Allah kar ka ce a'a" yanayin yadda ta kwantar da kai take lallaɓa shi ya sanya shi jin daɗi a ransa tare da jin kansa eh shi ne maigida. Saɓanin yadda farida ke yi masa magana gatse-gatse, wani lokacin ma sai ta yi abun da take so yake sani.
"Shikenan, Allah ya kaimu lokacin, za ki je in sha Allah"
FaÉ—aÉ—a murmushinta ta yi tana yi masa godiya.
Sai magariba ya je gidan farida, dan duba su.
Sai dai ta fara da yi masa ƙorafi, da zazzaga masa masifa, sannan ta miƙa masa takardar da inteesar ta zo da ita.
Ya karɓa ya karanta, sannan ya kalleta ya ce "Na gani, me zan ce?"
"Kamar yaya me zaka ce? Ba zaka kira shi ba a kan abun da ya aikata, ya wulakanta Æ´ar ka"
Dr. Ya ce "Ƴar ki dai, ki nema mata wani uban da zai tsaya mata, ni da ban isheku kallo ba ke da su, ai na yi zaton wani uban ki ka canza musu, kuma ba wani abu da zan kira mijinta na ce masa, tun da ya riga ya saketa, in dai irin halin da ki ke yi, ta je tana yi dole a korota, yayi haƙuri ma. Idan baki riƙe tawa ƴar bazawara karo biyu ba, ga zaurawa biyu nan har da ƙarin budurwa Allah ya haɗa miki, kuma dolenki ki riƙe" ya fice ya bar mata gidan.
Inteesar ta ɗora hannu a ka ta din ga rusa kuka, can gefe ma rahama kuka take yi, dan an saki mijinta, ya ƙwace mata sauran yaran, bayan aiko mata da tata takardar sakinta.
Farida ta koma kamar mahaukaciya, ta rasa in da zata saka ranta.