← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 134

Sashe 59

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

25

Cikin murna ummi ta ce "Ban manta ba, in sha Allah zamu je, nima ina son mu je".

"To kin zaɓi in da zaki kai ni ɗin?".

"A'a ai ni ban san wuraren ba, ko ina ne ma kawai sai mu je"

Yayi dariya ya ce "To shikenan, amma dai dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi bacci a nutse kar ki kasa bacci saboda 15k, you are not É—angote yet, kar ki kasa bacci saboda 15k dan Allah"

Ummi cikin halinta na yanga da ita ba ta gani ta ce "Kar ka dameni fa, ce maka aka yi ba zan iya bacci ba, kuma ko naira goma ce tunda ita ce gumina ai ita ce arzikina dole na yi murna"

"Ahaaf, ai na san ba iya bacci zaki yi ba saboda dubu sha biyar, to dai ki nutsu da Æ´ar 15k É—inki kin kasa rufe baki".

"Ai kuma sai ka yi, ba kula ka zan cigaba da yi ba"

Sosai yake yi mata dariya, noor ce ta shigo ɗakin ta ƙure ummi da take dariya da ido.
Cikin diriricewa ta ce "Raihan sai da safe".

"Akwai matsala ne?"

Ta ce "A'a zan yi wani abu ne" ta katse wayar tana kallon noor.

Noor ta ƙarasa ta zauna ta ce "Yaya ummi da wa ki ke waya ne?"

Ummi ta ce "Amm É—an ajinmu ne"

Noor ta waro ido ta ce "Ke fa ki ka ce Æ´an ajinku ba sa kulaki, kuma ba kin daina zuwa makarantar "

"Kai maman ƙarya nake yi kenan?"

Noor ta ce "A'a, to amma me ku ke cewa na ga kina dariya, ban taɓa ganin kina waya kina dariya haka ba, ko kema saurayin ki ka yi?" Da sauri ummi ta girgiza mata kai alamar a'a.

"To me ku ka ce a wayar"

Ummi ta ce "Noor kin fa isheni, magana muke za a bani salary ne, shi ne nake dariya, ai kiwa yana son kuÉ—i, ko ke ba kya so?"

Noor ta ce "Ina so mana, zamu ci daÉ—i ashe"

"Sosai ma" ummi ta yi maganar tana murmushi.

"Kin san me yaya ummi?"

Ummi ta ce "Sai kin faÉ—a maman"

"Inteesar ce ta zo fa yanzu" ummi ta ɗan waro ido, ta kalli agogon wayarta ƙarfe goma da rabi na dare.

Ta basar ta ce "Inteesar kawai ko? Ba na hanaki ba, ba zaki ce mata anty inteesar ba?"

"Kema ai ummi take ce miki, kamar fa kuka take yi, sun shige É—aki ita da maama, na je in ji meyafaru wai in fita har da ce mini munafuka".

Ummi ta kwantar da noor ta ce "Shhh maza yi bacci, kar in sake jin bakinki, hakan gulma kenan kuma haramun ne babu kyau"

Noor zata sake magana, ummi ta riƙe mata baki, tayi murmushi ta lumshe idonta kamar zata yi baccin.

Ummi ta kashe musu fitila, ita ma ta kwanta, amma noor ta tashi ta lallaɓa kunnen ummi ta ce "Wai mijinta ne zai auro mata kishiya, uncle sagir" ta sauka daga kan katifar ummi ta fita da gudu.

Sai da gaban ummi ya faÉ—i, ta san akwai tashin hankali kenan, tun da aka ce za a yi wa Æ´ar gwal kishiya, tayi saurin kawar da tunanin daga ranta dan ba huruminta bane ba.

Maganar raihan ta tuna, wai kar ta kasa bacci, saboda dubu goma sha biyar.

Dariya abun ya bata, ta gyara kwanciyarta ta shiga karanto addu'oin kwanciya bacci.

Aikuwa da safe da ta tashi, ta ga inteesar a gida, idanuwanta sun kumbura alamar ta sha kuka, kuma ba ta samu isasshen bacci ba.

Ummi ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama.

Daga haka ummi ba ta sake shiga sabgarsu ba, dan ta ga alamar ƙiris suke jira tayi wani abu, su huce a kanta, dan haka ta kama kanta, ko sallama ba ta yi musu ba ta fice.

ÆŠan halak yana in da suka saba haÉ—uwa yana jiranta.

"Ina kwana" ta gaishe shi, sai dai maimakon ya amsa ya ce "Inye ka ga attajirar garin nan, ke fa yau jin kanki ki ke yi daidai da kowa, saboda kina da 15K"

Ummi ta ce "Ka cigaba, tuwo ne yau a cikin flask É—in nan, wannan kuma kunun tsamiya, ka cigaba da tsokanata ba zan baka ba"

Ya kwashe da dariya ya ce "Aikuwa sai na ci abincin nan, kuma ba zan daina tsokanar ki ba"

"Sai ka ci in gani ai"

Raihan ya kunna motar ya ce "Girmata fa ki ka yi, ba fin ƙarfina ki ka yi ba, ƙwace abincin nan ba wahala zai bani ba".

Ummi ta ce "Idan ya zube shikenan ba".

"Kar dai ki manta kuÉ—inki account É—ina za a tura su, attajirar duk duniya".

Ummi tayi dariya tana kallon window.

Suna zuwa wurin aikin ummi, raihan ya ce a wurin zai ci abincin, idan ya tafi da shi ba zai ƙoshi ba.

Suna shiga wurin bayan sun gaisa manager ya ce "Ummi, an saka miki kuÉ—in nan fa"

Raihan ya ce "Eh, sun shigo sai ka ce wasu kuɗin kirki, gaskiya manager a ƙara kuɗin nan, haba 15k yafi ta sai man shafawa da cingam".

Ummi ta kalli raihan ta girgiza masa kai ta ce "Manager na gode sosai da sosai, Allah ya ƙaro mana coustomers, dan Allah kar ka damu da abun da raihan yake faɗa, Allah ya sanya musu albarka ka san yaro ne, sai a hankali" tayi maganar tana kawar da kanta gefe tana dariya.

Manager ya kwashe da dariya ya ce "Ai shiyasa bana biye masa, baƙinciki yake yi miki, shi yana zaman banza, wallahi ko kati kar ki saka masa".

Kallon ummi raihan yayi ya ce "Me ki ka ce mini yanzu?"

Juyawa ta yi tana dariya, ta nufi wurin da take zama, tayi aiki.

Aikuwa ya bi bayanta, yana sake cewa "Maimaita me ki ka ce mini yanzu?"

Ta ce "Na yi magana ne?"

Ya É—an tsuke fuska ya ce "Ki maimaita".

Ummi ta kalli raihan ta ce "Yaro, ko ba yaron bane?" ta sake maganar tana yi masa dariya.

Kyau ya ga tayi masa dariyar da take yi, haƙoran nan sun haska fuskarta sosai, ga laɓɓanta pink shar, dimples hagu da dama a kumatunta.

Yadda ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta zata, ko haushin yaron da ta ce ya ji, dan haka ta sake cewa "Lokacin da ka ke tsokanata, daÉ—i ka ke ji ai, nima yanzu is my turn".

Yayi wani irin murmushi ya ce "Wai shekara nawa ki ka bani ne? Na san dai maryam ta girmeki".

"Ba za a lissafa ba, koma dai yane kawai na girmi mutum, kuma idan kana son ka yi albarka ka din ga yi mini biyayya ka daina tsokanata"

Ya ja kujera ya zauna, har cikin ransa yake jin daɗi idan ya ga ummi ta sake da shi tana dariya, saɓanin da da kullum kamar a tsorace take da mutane, da farkon haɗuwarsu ne, ko haɗa ido ba za ta iya yi da shi ba, amma yanzu da confidence take gaya masa abu.
A ransa ya ce 'Irin wannan confidence É—in nake son ki samu, a cikin mutane"

Manager ya ce "Kai raihan, ka wani je ka gurfana a gabanta, zaka kalallame ta ka cinye mata kuÉ—i, to ahir É—inka"

Raihan ya ce "Manager, idan na waiwayo kanka ba zaka ji daɗi ba, yau ka sa an kirani da yaro, duk girman nan nawa, the whole me aka ce mini yaro, ke kuma ai shikenan ban abincina in ci, shima dan ba zan iya fushi da abincinki ba, da yasin ba zan ci ba" yayi maganar cikin sigar shagwaɓa.

Ummi ta yi ƙasa da murya tana kallonsa ta ce "Haba kar aji kanmu ayi mana dariya, ci abincinka ko manager kar ka yi wa bisimillah"

"Dama shi ya isa?"

Ummi ta tashi tana ta  ɗawainiya da coustomers, raihan yana cin abinci, suna yi suna faɗa da manager.

A hanya ummi take yi masa faɗa kuma ta haɗe rai kamar wata babarsa "Raihan, ka ce Alhaji ya baka aiki, amma sai ka zo wurina ka yi zamanka ka ƙi yi masa aikin, ko office ɗin fa baka zuwa, meyasa?".

"Haka aka ce miki bana zuwa?"

"To yau ka je ne? Zama fa kawai ka yi a wurin aikina, yakamata ka kammala yi masa aikin nan on time, sai shiririta ka ke yi"

Raihan ya ce "Nifa ba shiririta nake yi ba"

"To aikin ka ke yi? Banda surutun ƙwallo, me ku ka yi kai da manager? Gobe in Allah ya kaimu ka je office ka yi aiki, idan ba haka ba, ni da kai ne, ba zan kai ka shopping ɗin ba, kuma na daina bin ka mu tafi aikin tare"
Chapter 59 · 0% Book details