Sashe 112
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kalli iya ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Iya ni kuma? Yaushe? Ban san zancen ba fa sai da na nuna miki ina son auren ummi, ki ka gaya mini cewar ragowa ce, an taɓa yi mata fyaɗe tana yarinya, na ce ina son ta a haka, tun da tana yarinya ne, ki ka ce ba ki yarda ba. Nayi-Nayi ki gaya mini waye yayi mata ki ka ƙi, za ki aura mata idris na ce ki gaya masa abun da ki ka gaya mini, ki ka ce idan na faɗa zaki tsine mini, sai da zaki aurawa Idris ita na ce bai kamata ba ki ka ce dama shi yayi mata, amma ki zagaye ki ce mata ni na yi mata fyaɗe tana yarinya, duk saboda ki kare wanda yayi? Baki yi mini adalci ba, tsawon shekaru ummi kallon macuci take yi mini kenan?"
Iya ta ce "Ni fa ba haka na ce mata ba, na gaya mata hakan ne dan ta yarda da auren Idris a karo na biyu, kar ta auri wanda za ta aura amma kuma taƙi, kuma na yi haka ne dan Idris ya samu dama ta biyu a daidaita zumunci"
Hashim ya ce "Kuma ki ka ce mata ni na yi mata fyaɗe Iya, amma an yi abu ba ta sani ba har ki ka gaya mata? Wace ribar ki ka samu a kan hakan? Kawai ki cuce ni ki ɓata ni a idon yarinya saboda ki kare Idris? Iya meye dalilinki na fifita wani sashe a kan wani a cikin iyalanki ne?" Tuni idonsa yayi jawur, ya jefar da takardar sammacin ya ce "Ku je ku san yadda zaku yi ni ba ruwana"
Kawu Ilyasu ya ce "Idan ka tafi gidan ubanwa zamu koma? Yaya zamu yi da wannan abun? Ta ina za a fara rabon gadon shekara talatin da wani abu baya?"
"Wallahi baba ba saka hannuna, ba zan shiga maganar ba" yayi ficewarsa.
"Iya baki yi mini adalci ba, kin rarraba mini kan yarana kamar yadda ki ka rarraba kan naki yaran saboda son rai, ƙiri-ƙiri babu jituwa tsakanin Idris da magaji saboda ke, ashe wanda ki ke zaluntar da yawa, gashi kin zo kin sake damalmala lamari" cewar babar su Idris.
Kawu Ilyasu ya daka mata tsawa ya ce "Rufe mana baki, da can baki ga hakan ba sai yanzu? Uwar ta mu zaki ci wa mutunci "
"Na faɗa ɗin, tsawon shekaru muna yi mata biyayya ashe cutar mu take yi, ƙiri-ƙiri ta din ga muzgunawa mariya da ƴar ta muna ganin mu take so da ƴaƴanmu ashe zumuncinmu take yi wa illa tana kassaramu, ba ayi mini adalci ba" haka gida ya kacame da hayaniya kamar za a bawa hammata iska.
4YEARS BACK (SHEKARU HUÆŠU DA SUKA GABATA)
Iya ta kalli ummi ta yatsuna fuska ta ce "Au ke yanzu a yadda ki ke ɗin nan, har wani zaɓi ne da ke? Kin san dai mutum a hayyacinsa ba zai ce zai aureki ba, dan mazan yanzu fararen mata suke so kyawawa"
Ummi da kanta yake sunkuye ta yi shiru ba ta ce komai ba.
"Hmm ai duk da Idris ya ce ba abun da ya taɓa haɗa ku, ai ba a canzawa tuwo suna, kuma Idiris ɗin da ki ka guda shi ne rufin asirin ki, dan yadda ki ke ganin cewa an zalunceki da ki ka aure shi ai shi aka zalunta ya rufa miki asiri, tun da fanko aka kai masa, gaki fanko ga larura, duk namijin da zai aure ki ko dai a bazawara ko wadda ta zubar da mutuncinta tun a waje" ummi ta ɗaga kai tana kallon iya.
"Eh mana, ai ba ki kai budurci gidan Idris ba, tun kina shekara uku da watanni aka kawar da shi, dan an ƙetare ki"
Gaban ummi yayi mummunar faÉ—uwa, jikinta na tsuma ta ce "FyaÉ—e kenan?"
"Ƙwarai fa, da ki ka fara tasawa ma ai cigaba da biye-biyenki ki ka yi, Idris shi ne wanda ya rufa miki asiri, amma an buɗe ki tuni, dan haka wani zaɓe² ba naki bane, kuma dole a wannan karon ki sake auren Idris"
Ummi ta kalli iya cikin ƙunar zuciya, Idris ɗin da ya kwatsawa duniya cewar ba budruwa ba ce ita, ga kuma ciwon sanyi ya cinye ta, kenan shi tuntuni ya san an yi mata fyaɗe. Sai a lokacin ta tabattar da cewa mafarkin da take yawan yi gaskiya ne.
Tana kwance tana bacci a ɗaki, fitilar ƙwai na ci a cikin ɗakin, jin motsin wani abu ya sa ta buɗe ido, ba ta iya ganin fuskar waye, ya rage hasken fitilar ɗakin, daga nan ba ta iya tuna komai sai muryar iya tana cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, duk wanda ya tona wannan sirrin Allah ya isa ban yafe ba, ɗan uwanta idan ba a rufa masa asiri ba, zumunci sai ya lalace.
Ummi cikin wani irin gigitaccen kuka ta ce "Iya dama a gaske abun ya faru, ba Idris É—in ne ba dai, ina ganin abun a bacci, kuma na yi biye-biye na bi wa?"
Iya ta yi mata wani irin mugun kallo ta ce "Uban waye ya ce miki Idris ne? Shekara uku da rabi ki ke a duniya lokacin, uban me zaki tuna?"
Ummi ta yi shiru sannan ta ce "DauÉ—ar gora ciki ka sha ta, duk wanda ya tona wannan sirrin ban yafe masa ba, ba haka ki ka ce ba a lokacin? Mama ta din ga kuka a lokacin da daddare, Idris ne mana iya"
Iya ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, dama na daɗe ina faɗar kina da alaƙa da maita, tayaya zaki tuna abun da ya faru kina shekara uku da rabi? To ba Idris bane ba magaji ne"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a Iya Idris ne, dan haryanzu ban manta irin barazanar da yake yi mini ba, da ƙoƙarin sake haike mini, yaya magaji ne yake ƙwatata"
"Sai kuma ki yi, Idris godiya yakamata ki yi masa, dan taimakon ki yayi"
Ummi ta yi kuka kamar ranta zai fita, ta ji zafi da baƙin cikin mummunan labarin da iya ta gaya mata, daga Idris ɗin har hashim wata irin tsanarsu ta shiga ranta, amma ƙasan zuciyarta ya kasa amince mata da yaya magaji zai aikata haka, ta yi ƙoƙari ta din tuna alkhairin sa, hakan ya sanya yin ƙoƙarin ɓoye masa abun da yake ranta game da shi.
Gashi babu wanda za ta tattauna Maganar da shi, dan haka ita kaɗai tayi kukanta ta sha baƙin cikinta, haka zalika maganganun iya ba su yi tasiri a zuciyarta ba, ta ji za ta iya yafewa Idiris zaluncin da ya yi mata ba.
Iya ta faÉ—a mata haka ne, saboda zafin rashin amincewa da auren Idris a karo na biyu, da kuma yadda Hashim yake ta son nuna shi yake son ya auri ummi lokacin da suka je saukar.
Sai dai hakan bai yi tasiri a zuciyarta ta ji zata sake iya auren Idris ba, shi ne zuwan da suka yi har dr. Ya ce sai an nemi iznin ummi.
Ummi ta ɓata darare da dama tana kuka, tana tunanin babu wani abu mai kama da farinciki da zata samu a rayuwa. Yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ta ƙara tsananta gudun Raihan.
CIGABAN LABARI.
Raihan kamar zai zare saboda neman ummi, duk iya tunaninsa yayi amma ya rasa ina ta shiga.
Gagarawa kuwa Abdul suka kira suka sanar masa da halin da ake ciki, wai sun nemi lambar dr. Sun rasa su zo su kawo musu ɗauki, ummi ta kai ƙarar su kotu.
Abun ya bawa Abdul mamaki, Abdul ya tambayi ina ummin take, suka sanar masa ai ta bar gidan ba su san in da ta koma ba, ya cigaba da matsawa da bincike, dan ya san ummi ba zata aikata irin wannan É—anyen aikin ba, ya kira Yaya magaji, magaji ya ce an yi haka, amma Iya ce ta kori ummi.
Ya tambaye shi ko ya san in da ummin ta koma, ya ce masa bai sani ba.
Abdul ya tabattar da lallai an kai ummi bango da har ta fara da irin wannan hukunci mai girma.
Kawu Saminu ya din ga nanatawa Abdul, lallai ya sanar da dr. Kan ranar da za a fara shari'ar domin, a kashe maganar.
Abdul ya ce "Kawu ka manta baya ƙasar, babu abun da zai iya yi a kai, kuma yanzu a fara mayar da hankali a samo in da take tukuna, sai a yi wa tufkar hanci, tun da in dai ba ita ta janye ƙarar ba, ba zai yiwu a kashe maganar ba"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma wannan yarinyar an yi sheÉ—aniyar mara mutunci, maimakon iya mu ta gaya mana ta ce a raba gadonta a bata, sai ta kaimu kotu?"
Ummi kuwa ana gobe za ta bar gidan su Iya, ta karɓi aron wayar amaryar kawu Ilyasu, ta aika nana ta sayo mata kati ta kira yaya magaji.
Suka gaisa ya ce "Ummi layi ki ka canza ne?"
"A'a yaya, akwai matsala ne, ina so ka taimaka mini ina gagarawa yanzu haka"
"Subhanallah, matsalar me kuma?"
Ummi ta ce "Aurena ne ya samu matsala, can gidanmu anty farida ta ce ba zan zauna ba, nan ma Iya ta ce sai na tafi"
Hashim ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mutuwa auren yayi?"
"Eh, mamansa ce ta saka ya sake ni, ba na son zuwa maiduguri in É—ora musu nauyi daga yin aurena, ga dr. Ba ya gari"
"Kin san menene, ni yanzu ina dutse ni da matata, ki saurara da kyau, zan yi miki kwatancen gidana, akwai mukulli a maƙwabta, zan kira su su baki, ki buɗe ki shiga ki zauna, ki bani account number ki in turo miki kuɗi, ko zaki buƙaci wani abun, amma Abdul ya kirani ana nemanki, basu san in da ki ke ba, ai ban san kina gagarawa ba".
Ummi ta ce "Dan girman Allah ko ya sake kiranka kar ka gaya wa kowa ina gagarawa, kuma ba wanda zan gayawa ina gidanka, dan Allah kar ka gayawa kowa idan ku ka dawo zan yi maka bayanin komai"
Ya ce "To shikenan, ki turo mini account number"