Sashe 125
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu dare ba rana, ta miƙe da yawan tasbihi da bayar da sadaka, tare da tawasalli da ayyukan alkhairin ta, tana roƙon Allah idan auren Raihan da alkhairi Allah ya tabattar ya rage mata kishi, idan babu kuma, Allah ya rusa abun, ya musanya da mafi alkhairi, yayi mata maganin duk wani abu da zai tayar mata da hankali, ko kawo cikas ga rayuwar aurenta.
Sannan ta tsananta addu'a, a kan Allah ya ƙara qa raihan son ta, da ƙaunarta ita kuma Allah ya bata ikon yi masa biyayya.
A hankali ta ji zafin kishin yana raguwa, bayan auren mamanta da dr. Ta din ga istigfari a kan ɗagawa raihan hankali a kan maganar auren sa, wataƙila da ta cigaba da matsawa, da ba ayi na mamanta ba.
Lokaci É—aya mami ta daina kira tana É—agawa raihan hankali a kan auren nan a gabanta, kuma ta daina zuwa ci mata mutunci, dama tuni ta saka lambar maryam a blacklist.
Gidansu raihan kuwa, rana tsaka babu notice, Hajiya Aisha ta dira a gidan Alhaji Tahir.
Sai da yayi mamkin ganinta, ya ce "Ke hajjaju, zuwa ba sanarwa matan gidan babu wanda ya sanar mini zaki zo ai".
"Ina na ga ta tsayawa jiran notice, ashe raihan zai ƙara aure, kuma daga ɓangaren uwarsa, haba Tahir, kuma kana kallo, yaushe yayi auren farin zaku ɗora masa ɗawainiyar auren matan biyu?"
Alhaji ya ce "Ke daɗina da ke, ba kya ɗaukar abu da sauƙi a kan raihan, babarsa ce take son ya ƙara"
"A'a ban lamunta ba, yanzun ma ba dan Salim ya gaya mini ba, ba zan sani ba kenan? Kuma a rasa wa zai aura sai wannan dangin masifa da bala'in, ashe har ƙarya yayi muku bashi da lafiya dan ku ƙyale shi, amma abu kamar bala'i, kuma saboda tumasanci irin na bilki har da sakawa ya saki ƴar mutane, to mu ba haka muke ba, ko da muka yi bore da ka aure ta, ka juyawa ƴar mu baya, bamu ce ka saketa ba, dan haka da kaina na zo na yi wa tufkar hanci, ba zai auri ƴar rakiyar ba".
Alhaji ya ce "Ke ki daina yi mini faÉ—a kamar wani É—anki mana, har kuÉ—i fa an kai".
"Amma ai ya ce ba ya so, dole na yi maka faɗa, ba fa kowane lokaci yakamata ka din ga biye wa matanka da yaranka suna abun da suke so ba. Wallahi muddin ta ce sai yayi auren nan, sai dai ta nema masa wata sana'ar ta kafa shi, ya bar shugabancin kasuwancin ka, dan na san da shi take taƙama, idan ba zaka iya cewa an fasa ba, zan je na yi wa ita rakiyar magana, dama ni da ita kar ta san kar ne ai.
Su riƙe kuɗin an bar musu, amma ƙara aure ba yanzu ba". Tana tsaka da masifar, Hajiya ta kawo mata abinci, ita ma ta rufeta da faɗa a kan, meyasa ba a gaya mata abun da yake faruwa ba, dan haka ta je ta kirawo mata bilki, kuma a kirawo mata Salim, dan ta tabattar mata shi ya gaya mata ba Raihan ba.
Aikuwa ranar mami ta ga ta kanta, dan cin mutuncin da hajiya Aisha ta yi mata sai da ta yi kuka, sannan ta ɗora da cewa "Ke ma ki ji idan da daɗi abun da ki ke yi wa taki sirikar, saura maryam dan ubanta, zan iya wanke ƙafa na je har fatakol ɗin, ba a barikin soja ba, idan a cikin bindiga take na je na ci ubanta a kan matar raihan. Raihan ɗin sai ka ce wani ɗan gwal da ake ta wannan tsiyar a kansa, ita ba uwa ce tayi naƙuda ta haifeta ba? Da ki ke mata iƙrarin munin ke halitta ki ke yi, da hancinki kamar pipe ɗin ruwa. Mu danginmu bamu sabawa yi wa sirikai rashin daraja ba, dan haka ba zaki fara ba. Tun wuri ki samu rakiyar ki yi mata bayani, idan kuma ki ka bari na yi mata abun ba zai yi muku daɗi ba".
Duk da haka sai da suka yi faɗa da Alhaji, yayi mata ƙorafin za ta mayar da su ƙanan mutane.
Bayan su hajiya sun tafi ta ce masa "Yarinyar nake yi wa gata, na lura matar raihan irin matan nan ne da ba kowace irin mace za ta iya gogayya da su ba a kishi, ai ko ba ƙarara ba yana faɗa, kai ka sani, idan aka yi masa auren dole matar wahala kawai za ta sha, shi wannan dai da ake yi wa kallon mummuna ita ce tayi masa, da azo ya auri ƴar mutane ta wahala a banza ai gara ba ayi ba".
Ya ce "Na nuna wa bilkin haka, amma taƙi ganewa, kuma uwar yarinyar ce take zigata, amma tun da ke tana tsoranki, ƙila ta ji.
***
Dr. Kuwa kwanansu uku a uganda, dama akwai abokinsa da yake zaune a can yake lecturing, kasancewar babban gida ne sosai da gwamnatin ƙasar ta bashi, a wani sashe na gidan dr. Yake zaune.
Kamar wanda ya auri yarinya ƙarama, haka yake jin kansa, ya tuna abun da farida ta ce na ba uwar da za ta tsinana masa, amma ya ga abun da bai yi tsammani ba.
Tun ranar da suka je, take mugun jin kunyarsa, ko kallonsa ba ta iya yi, da safe idan ta gaishe shi, komai zai ce mata sai dai ta bashi amsa da ka, amma ba zata yi magana ba, kamar ya auri budurwar ƙauye.
Shi gaba ɗaya ma dariya take bashi, jin sa yake hankalinsa a kwance ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, saɓanin idan yana tare da farida, da wani lokacin rashin mutuncinta ba ya motsawa, sai yana buƙatar ta, sai ta tsiro da na ta buƙatun, sai ya yadda zai yi, koma ya yi mata sannan ta yadda da shi, kamar masu zaman dadiro ba aure ba.
Ya zuba mata ido, ta koma gefen kujera tana ta sinne kai, ya É—aukko wayarsa ya duba ummi na online, ya kirata voice call.
Mariya na jin muryar ummi, ta tattara hankalinta a kansa.
Suka gaisa da dr., Yake tambayar ta ko sun je duba Iya, ta ce masa a'a sai cikin satin.
Mariya ta ƙura masa ido, ya ce "Ko in baki ku gaisa?" Ta jinjina masa kai da sauri.
Ta matsa kusa da shi ta karɓi wayar, ta saka a kunnenta ta ce "Ƴar baƙa kyakykyawa"
Ummi ta yi dariya ta ce "Mama Amarya"
Ta É—an tsuke fuska ta ce "Zan ci gidanku"
Ummi ta yi murmushi ta ce "To ya ugandan? Kin fara jin yaren su"
Ta ce "A'a ni ban taɓa fita ba ma, amma daga nan gidanki ba nisa ko? Ai zan iya zuwa"
Ummi ta ce "Haba mama, ba fa Nigeria ba ce ba, ba ki ga sai da ku ka hau jirgi ba"
Ta ce "Eh to haka ne, to ya cikin naki ashe kin kusa haihuwa"
Ummi ta yi sauri ta kashe wayar dan kunya, tun da mama tazo manyan riguna take sakawa da hijjabi, dan kar ta ga cikin, kuma har ta gama kwanakinta ba ta nuna mata ta ga cikin ba sai yanzu.
Ta kalli dr. Ta ce "Ka ga na daina jin ta, É—an dubo mini ita"
Yayi dariya ya ce "Kunya ki ka bata ta kashe wayar, ina ruwanki da cikinta" yayi maganar yana matsawa daf da ita.
"Ni mamaki ma nake yi, har ummi ce da ciki, ohh kwanci tashi asarar mai rai. Aka yi ta cewa ba zata yi aure ba, gashi ma har za ta haihu"
Dr. Ya ce "Eh haka lamarin Allah yake, amma dai dan Allah ki daina guduna, ni ba dodo bane ba, yanzu saboda maganar ummi ce shi ne ki ka kula ni, bayan tun safe kin ƙi kulani"
Ta sunkuyar da kai kamar ta yi layar zana ta ɓace.
Ya ɗago haɓarta, amma ta ƙi kallonsa.
Yayi murmushi ya ce "Zo mu tattaka, mu je kasuwa ki ga garin" ya riƙe hannunta ta tashi tsaye, suka nufi bedroom.
Kusan kwana huÉ—u, da Abdul ya tura kuÉ—i, kawu Ilyasu ya kira Abdul yana tambayar sa, wai shiru fa ba su ga kuÉ—i ba, jikin Iya yana tsamari, za a sallame su ma saboda rashin kuÉ—in.
Abdul ya ce "Ai tun a ranar na tura dubu tamanin, dr. Bai hau jirgi ba sai da ya tura mini kuɗin, ni kuma na ƙara na tura".
"To ya haka? Idris ya ce ba su shigo ba".
Abdul ya ce "A'a dai, ya sake bincikawa, dan ta application na tura kuÉ—in"
Ya din ga mamaki, ya duba wayarsa har da receipt kuÉ—i sun fita.
Washegari tun da safe suka shirya, raihan ya je Abuja, noor da Abdul sai ummi suka tafi Jigawa duba Iya.
Sai dai da suka je asibitin, sai da ummu ta ɗan tsorata, Iyan duk ta zama abun tsoro, fatarta ta yamushe, gashi an aske gashi, duk an liƙe kan da bandeji, hannunta da ƙafrta ma haka, idonta yayi ja saboda azabar ciwon kai, ba ayi hoton ƙwaƙwalwa ba, balle a san menene yake faruwa.
Noor ta ce "Kai na ga iya ta koma kamar simigul"
Abdul ya galla mata harara, ummi ta ce "Sannu iya ya jiki?" Iya ba baki sai kallon ummi da take yi.
Ta kalli amaryar kawu Ilyasu ta ce "Ga abinci mun zo da shi a bata, amma kunu ai ba zai riƙe ta ba".
Suna nan zaune su kawu Sagir suka zo, aka gaggaisa, ake sake mayar da yadda aka yi, kuma ummi ta yi musu kwarjinin da suka kasa yi mata zancen auren dr., Sai magana suke yi mata da girmamawa.
Ummi ta ce "To shi Auwwalun an kama shi an hukunta shi, ko kuwa?"
Amarya ta ce "A'a ya gudu"
Ummi ta ce "Kodayeke ba hurumina bane ba, tun da dauÉ—ar gora ciki ka sha ta, da na saka an nemo shi, wannan dauÉ—ar yakamata iya ta shanye ta, a rufa masa asiri ai É—an so ne "
Aka rasa wanda zai yi magana, Idris yayi sallama, suka amsa, sai dai hankalinsa ya tashi ganin su ummi.