← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 134

Sashe 44

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam ba ta tsaya saurarar ummi ba, ta sayi anko ta bawa ummi duk kyauta, sai dai da ƙyar farida ta bar ummi ta je rana ɗaya bikin, shi ma da ta je kasa sakewa tayi, dan wareta ƴan makarantar ma suka din ga yi, dan haka nan da nan ta koma gida ta bar wurin.

Satin Maryam biyu a gidanta, mijin ya tafi da ita can wurin aikinsa, kasancewar soja ne babba.

***
Kwanci tashi asarar mai rai, iyayen hindu suka din ga tatsar su Iya kuÉ—i, har sai da ta yi watanni shida cif a gida, sannan aka É—aura auren Idris da hindu, saboda babanta dagewa yayi a kan sai an kai kuÉ—in aure da duk wani abu na al'ada da ake yi.

Tare da cigaba da yi musu barazanar cewa, zasu dawo musu da Æ´ar su.

Abun kunya dai da ake gudu, ya riga ya gama watsuwa a cikin gagarawa, na abun kunyar da jikan Iya ya tabka.

Gidan da ummi ta zauna, aka sake kama haya, kansancewar ba kowa a ciki, aka ƙara gyara gidan, aka kai hindu da jaririyarta.

Ko kallo hindu ba ta ishi idris ba, haka ita ma ba ta kansa ta bi ba, ta cigaba da sabgoginta da Æ´ar ta, sai dai cikin dare yarinyar nan ta tashi, ta din ga tsala ihu kamar za ta shiÉ—e.

A fusace ya tashi ya ce "Dalla malama ki É—auki Æ´ar ki saka tayi shiru, ta cika wa mutane kunne da kukan banza".

"To kai mai zai hana ka saka tayi shirun, na ga kaima Æ´ar ka ce"

"Ƴar gaba da fatihar? Kar ki sake haɗani da ita".

"Ko Æ´ar gaba da meye uban waye yayi cikinta, ai ba ita tayi kanta ba, ka ga wallahi ka ce zaka takura mini, ko ka É—aga mini hankali sai na koma gida na gaya musu. Kai ba ma ka da kunya, ni ka ke gayawa Æ´ar gaba da fatiha ce, uban waye ya lalata ni?".

"Iyayenki dai suka ja miki, da ba aurenki zan yi ba, suka hana ni".

Hindu ta yi shewa ta ce "To uban wa ye zai baka auren Æ´a? Kana É—an iska?"

"Eh ina ɗan iskan amma ai gashi an liƙa mini ke"

"Oho kai ka sani dai"

Ta dubi Æ´ar da ke ta tsala ihu ta ce "Ke hajara tsohuwar banza, ubanki ya ce ki yi masa shiru, Æ´ar gaba da fatiha"

Idiris ya ce "Tsohuwar banza, kakata ki ke zagi kenan?"

"Eh to, idan ka tsargu hakan ne" haka suka din ga faɗa kamar kaji, a tsakiyar daren nan maƙwabta na jin su.

Abdul ne yayi sallama a kitchen, ummi na girki, suna ta tilawar Alqur'ani ita da noor.
Raino ummi take yi wa noor da kulawa, bacci ne kawai yake raba su, baccin ma wataran a É—akinta take yi.
Tun kan noor ta shiga makaranta, ta iya azkar da karatun Alqur'ani, dan ba ta yi pre nursery ba, kai tsaye nursery 1 aka kaita, saboda ta har rubutu ta fara iyawa.

Sai dai noor masifaffiya ce, ba ta taɓuwa a wurin yayyenta, dan baki ne da ita sosai da sosai.
Ba ta jin maganar farida, kamar yadda take jin maganar ummi, fitsara da rashin kunya kuwa ba a magana, ummi da Abdul kawai take ɗagawa ƙafa, ƴar mitsitsiya da ita ga azabar taurin kai, ummi ce kawai take iya sarrafa ta yadda take so, dan haka ba wani shiga shirgin noor suke yi ba, tayi maka rashin kunya ka jibgeta ba za ta yi kuka ba.
Ummi tayi ta mata faÉ—a, dan ita kanta tana mamakin rashin kunyar noor.

"Yaya ummi" Abdul ya kira sunanta.

Cikin haÉ—a baki ita da noor suka ce "Na'am yaya Abdul"

Abdul ya tsuke fuska ya ce "Da ke nake?" Ta girgiza masa kai tana É—an murguÉ—a baki.

Ummi ta kalli Abdul ta ce "Yaya Abdul yaya ake ciki? Ka dubo mini"

Ya miƙo mata envelope ya ce "Eh to, congratulations you got nine credits including maths and English, i know you can do it ai"

A take ummi tayi sujjadar godiya ga Allah, noor ma ta durƙusa tayi, ummi ta ɗago tana Alhamdilillah.

Noor ta ce "Wai menene? Me aka yi?"

Abdul ya ce "Yaya ummi ta ci jarrabawa, dan haka ita ma very soon zata shiga jami'a"

Tsalle noor ta din ga yi tana ihu, ba tare da ta san ma menene cikakken bayanin ba.

Kausar ta shigo kitchen É—in tana tambayar lafiya.

Noor ta ce "Yaya ummi ta ci jarrabawa, za ta shiga jami'a".

Tsaki kausar ta yi ta ce "Shi ne kuma ki ke yi mana ihu?"

"Eh É—in, yeeee yaya ummi ta ci jarrabawa " tayi maganar tana tsalle ta fita daga kitchen É—in.

Kausar ta yi tsaki ta fice, Abdul ya ce "Yaya Ummi, kina zaune an haifi mai tare miki faÉ—a"

Ummi ta ce "Ni mamana saliha ce, amma mama ƙarama ta fiye tsiwa" suka yi dariya, ummi na sake godewa Allah a kan wannan gagarumar nasara da ta samu.

Takanas saboda ummi dr. Ya dawo gari, saboda shirye-shiryen nema mata admission, Abdul yana level 2 a BUK yana karantar Agric.

"Dr. Wai ya na ganka a gida a tsakiyar sati haka? Kuma na ga baka daÉ—e da tafiya ba".

"Abdul yayi mini magana a kan waec ɗin ummi, ina son in ƙarasa mata abubuwan da yakamata kar ayi mini ba dai-dai ba".

"Shi ne ba zaka wakilta wani ba, sai ka dawo da kanka?"

"Ki na da damuwa da hakan ne?".

Haushi ne yakamata tayi masa banza, duk iya ƙoƙarin ta a kan cire hankalinsa daga kan ummi, ta kasa nasara ɗari bisa ɗari.

Ta sake kallonsa ta ce "Wai ni dr. Zuwa yaushe zan cigaba da jerawa da ummi a gidan nan, intee tana gama secondary, nake son a aurar da ita, yaron ya matsa, ita kuma tana nan shirin tafiya jami'a ma take yi, gaskiya ina son privacy a gidana, ba zan cigaba da jerawa da gandamemiyar budurwa ba".

"Intee ke ki ka takura a karɓi kuɗin aurenta, ba dole na yi muku ba, ni kuma a ƙyale mini ƴa tayi karatu. Guda nawa ummin take da ki ke wani zancen gandamemiyar budurwa, yanzu fa za ta shiga jami'ar".

"To wai ina uwarta, a mayar da ita wurinta mana".

A fusace ya ce "Wai a kan ki ummin nan take ne?".

Muryar noor ce ta katse shi, tun daga wajen ɗakin take ƙwala masa kira.

Ya ce "Na'am shalelena"

"Kalli littafina, uncle ya saka mini 10 over 10, assignment É—in da anty ummi ta koya mini".

Ya ce "Wow masha Allah, congratulations baby".

"Thank you " ta faÉ—a cikin iyayi sannan ta ce "To nima tunda na ci jarrabawar, zan shiga University?"

Ya kwashe da dariya ya ce "From primary one to university?"

"Eh, ba anty ummi ma ta ci jarrabawa zata shiga university ba?"

Yayi dariya, ya biye mata ta gama shirmen ta, ta tafi, sannan ya kalli farida ya ce "Farida wai zuwa yaushe zaki daina planing É—in nan, noor tayi girma yakamata ace kin sake haihuwa, 4yrs fa".

Farida ta yamutsa fuska ta ce "Nifa na gama haihuwa, yaushe Allah ya amfana guda huÉ—un".

"Amma da bani da yadda zan yi na riƙe ne, sai ki faɗi haka, Allah ya yassare mini yadda zan kula da yarana, meyasa zaki ce kin daina haihuwa?".

Ta miƙe tsaye ta ce "Ka auri ummi ta haifa maka!".

Wani irin damm ƙirjinsa yayi, ya bita da kallo, saboda munin maganar da ta faɗa.

Ya girgiza kai kawai, domin ba shi da abun da zai faÉ—a gaba É—aya.

Iya ƙoƙari kawu yahaya ya yi wa ummi, a kan harkar makarantar ta, dan ma farida na ta yi mata mugunta a kan wasu abubuwan.
Yayi mata komai sai dai ɓangaren sutura ummi na fuskantar barazana, domin kuwa ummi ba ta da suturar kirki, duk da ma'abociyar hijjabai ce, su kansu hijjaban nata duk sun mutu su yi haske.

(Kowane ƙalubale ummi za ta fuskanta a jami'a? Bright pens na godiya sosai 🙏)

Whats app only please.
Ayshercool
08081012143
   *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P20

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

20

Ummi ganin al'amuran take yi kamar a mafarki, duk da tsanani da matsi, haɗi da ƙalubale daban-daban yau ga ta a makarantar jami'a, lallai lokaci yana sauri.
Chapter 44 · 0% Book details