← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 134

Sashe 123

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Auwwalu kuwa cikin maye yake ta masifa "Sai da na gaya mata ba ruwanta da ni, amma taƙi ji, dama a ƙule nake da ita ta zagi babarmu jiya, duk ta tsane ni saboda bana ba ta kuɗi, ina kallo har kazata ta mara dan tana jin haushina, wallahi wiwina ta fiye mini wannan tsohuwar banzar" yana gama maganar ya juya yana tangaɗi ya fice.

Da gudu amarya ta fita tana kururwar neman agaji, mutanen gidan suka fara shigowa, Iya na kwance ko motsi ba ta iya yi.

Da ƙyar aka samo abun hawa, aka tafi da ita asibiti, daga can asibitin suka ce sai dai su je babban asibiti, ba zasu iya dubata ba.

***
Can garin kanon dabo kuwa, ummi kamar ta taka rawa, saboda ranar dr. Zai É—aukko mata mama daga Maiduguri, ita da noor sai aiki suke yi, ummi cikinta ya fito sosai ganin tudunsa a rigarta.

Dr. Kuwa tun sassafe ya tafi maiduguri, domin É—aukko mariya, da shi da abokinsa.

Can Maidugurin ma, an shirya musu kayan abinci, an yi wa mariya lalle, ta sha gyaran jiki kai ba ka ce ta haifi ummi ba, ana gobe dr. Zai je suka É—an gayyaci mutane da Æ´an uwa aka yi walima a can maidugurin.

Anty maryam ta kalli mariya ta ce "Wai duk murnar ganin angon ce haka? Bakinki ya ƙi rufuwa"

Ta ce "Haba Anty Maryam, kin saka na ji kunya, kawai zan ga ummina ne, nake ta jin daÉ—i"

"Kai mariya, ke sam ba ki da alkunya,  ƴar fari ce fa"

Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shekarar mu nawa ba ma tare, sai in din ga jin tamkar ta koma ƴar karamarta, ƴar baƙar ƴa ta mai kyau, na gyara duk wasu abubuwa marasa kyau da suka faru da rayuwar ƴa ta, wallahi anty maryam haryanzu ina jin tausayin ummi, rayuwar da ta yi ya kasa zama tarihi a wurina, kuma zuwan da ta yi na ƙarshen nan, kamar akwai wata damuwa da take ɓoyewa, fatana Allah ya sa ba wata matsalar ce a gidan auren nata ba, Allah ya sa ta daina shan wahala" kan ta kai maganar gaba ɗaya hawaye ya wanke mata fuska.

Mama ta ce "Mariya, ba zaki daina É—orawa ranki damuwar abun da ya wuce ba ko? Ga bawan Allahn nam sun zo, ai sai su zata ko son shi ne ba kya yi"

Sallama dr. Yayi tare da abokinsa, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa.

Suka shiga É—akin da aka saba saukarsu, ya kalli maman ummi, ya tuna maganar Farida, ta yi shar da ita, sai dai yayi mamaki ganin tana kuka.

Ya kalli mama ya ce "Mama lafiya kuwa take kuka?"

Anty maryam ta ce "Daga yin zancen ummi, ta hau kuka ta ƙi ta bar abu ya wuce, kullum ta tuna rayuwar ummi sai ta yi kuka, abu ya riga ya zama tarihi"

Mariya ta ce "Anty Maryam, tun tana kan cinya fa, aka ƙwace mini ita, kuma fa itakaɗai ce da ni"

Mama ta ce "To da mutuwa ta yi ya zaki yi?"

Da sauri ta ce "A'a ummi ba zata mutu ba, babanta ya mutu, ƙaninta ya mutu, idan ta mutu ya zan yi?"

Dr. Ya fuskanci jikinta haryanzu da saura, kuma tuna rayuwar ummi, ke saka jikin ya motsa mafi akasari, dan haka ya ce "Shikenan ya isa haka, ke da zaki koma kano ma, duk lokacin da ki ke so zaki ganta, ku koma kusa da juna"

Kamar ƙaramar yarinya take goge hawayenta ta ce "Ni sonake ta koma ƴar ƙarama kamar lokacin da iya ta ƙwace mini ita, in din ga goyata, idan na yi mata wanka na yi mata kwalliya, amma kawai iya ta ƙwace mini ita, ga zafin mutuwar mijina"

Ya ɗan ƙura mata ido, ba a ƙasa ummi ta ɗaukko shagwaɓa ba, duk da ummi ta ninka mariya shagwaɓa nesa ba kusa ba.

Ya kalli su Anty Maryam ya ce su É—an basu wuri.

Bayan sun fita ya matsa gabanta ya ce "Haba maman ummi, idan mijinki ya mutu yanzu ba gani ba".

Ta kalleshi ta ce "Kai ba bashir bane, yaya yahaya ne, ba na so kai ma iya ta ce na kashe ka, wai iya ta ce ni na kashe baban ummi, ya za ayi na kashe shi?" Tayi maganar hawaye na cigaba da zuba.

"Ki manta da maganar iya, yakamata ace memorynki, yana tuna abubuwa masu daɗi, idan baby ki ke so ki yi addu'a Allah ya kawo miki ƙannen ummi, ki yi ta goyawa ita yanzu ummi tana da mai goyata"

Ta É—an yi shiru kamar wadda ta farka daga bacci ta ce "Kai, ummi fa ta yi aure, kuma nima sai na haihu?"

Yayi murmushi, ganin kamar tunaninta ya dawo.

Ya ce "Idan ki ka cigaba da kuka, da tuna abun da ya wuce, ba zan tafi da ke ki ganta ba".

Haka yayi ta rarrashin ta, dama tuni su mama sun haÉ—a mata kayanta, suka raka su har mota, suka kama hanyar kano.

Gidan ummi, bayan sun gama aiki, noor ta É—auki wayar ummi ta tafi É—aki tana game.
Ummi kuma na falo tana kallo, sai ga Farida ta zo gidan, gidan da tun da ummi tayi aure, kusan shekara ba ta taɓa takowa ba.

Sai dai duk yadda ake kwatanta mata haÉ—uwar gidan ummi, sai yanzu ta tabattar da idonta ya gane mata.

Kamar babu komai ummi ta tashi cikin fara'a, kamar babu wani abu a ƙasa tana "Oyoyo, yau na yi babbar baƙuwa, sannu da zuwa anty" wani irin mugun kallo take yi wa ummi, da mamakin iskanci ne ko rainin hankali ya sa take wannan washe mata bakin.

"Ke saurara bana son karuwanci da iskanci, ni zaki yi wa bariki kina wani washe baki kamar bakin buhu?"

Ummi ta shafa bakinta, a iya saninta dai ba ta da ƙaton baki, ji ta yi kamar ta yi dariya amma ta maze ta ce "Ai baƙonka annabinka anty, kuma akwai hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da yake cewa wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya girmama baƙonsa. Ki zauna bari na kawo miki ruwa".

"Ki yi mini shiru ko na ɓarar da ke, ba ki da abun da zaki bani, ke da aka kawo mini ke cikin dauɗa da ƙazanta babu ko suturar kirki, har ke ki ke da abin bani, dan kin auri mai kuɗin da uwarsa ba ƙaunarki take yi ba, auren abun kunya, auren yaro ƙarami? Butulallaiya mara mutunci, wato abun da ki ka yi wa wancan ƴan ƙauyen shi ne nima ya biyo ta kaina, ki ka saka dr. Ya auri babarki, mahaukaciya da ba ta san ciwon kanta ba?"

Ummi ta ce "A'a fa, ni ban bayar da shawarar hakan ba, dr. Ya zo mini da maganar na goyi bayansa É—ari bisa É—ari, ko ba komai na yi ramuwar gayya, kuma ba fata ba ko aurena ne ya mutu, ko wani abu ya faru ina da wurin zuwa.
Da ki ke iƙirarin an kawo ni cikin dauɗa da ƙazanta, ai ba ke ki ka kula da ni ba, wan ubana ne, dan haka ke bai kamata a ji wannan gorin daga bakinki ba, ba ki isa ki yi mini gori ba a kan wannan, ko kin manta irin riƙon da ki ka yi mini?" Ummi ta ɗaga rigarta, gefen cibiyarta ya ɗan yi shati, ta ce "Na san wataƙila ke kin manta, kuma an yi sa'a jikina ba ya riƙe tabo, wannan ne kawai yayi saura kuma da shi zan koma ga Allah, har azaba da wuta ku ka yi mini ke da ƙanwar ki, wallahi da ramuwar gayya zan yi a kan ki, sai kin bar gidan dr. Kuma Alhamdilillah a yanzu dai Allah ya yi mini sutura da rufin asirin da ba kwa so, kuma wallahi ni Salma ina da abun da zan baki.
Amma ba wannan ba, na zata bayan na yi aure komai zai wuce, na yafe komai ya wuce, amma na fuskanci hali zanen duste ne, ba zaki canza ba, tun bayan da ki ka yi mini korar kare da na je gida aurena ya samu matsala, dan haka mun saka ƙafar wando ɗaya da ke, za ki ga mahaukaciya ganin idonki, yadda na ke shimfiɗa mulkina ba boka ba malam a gidan mijina, sai uwata mahaukaciya ta shimfiɗa na ta mulkin ba yadda ki ka iya, zaɓi ya rage naki, ko ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ko kuma ki shirya yin fito na fito da ni, tsakanina da ke babu ɗaga ƙafa, kuma ki gaya wa rahama, idan har muna raye sai Allah ya jarabceta da wuta, kamar yadda ku ka yi mini azaba da iata, dan wallahi ban yafe ba! Ko zan yafe muku komai, banda wannan"

Tirƙashi! Ummi ta shayar da farida ruwan mamaki, gani take kamar daga wani wurin maganar ke fitowa ba bakin ummi ba.

Cikin dakiya farida ta ce "Yaushe aka yi daren, da har gari zai waye, ki ke iƙirarin shimfiɗa mulki a gidan miji? Ɗa namiji ne fa da bashi da tabbas".

Ummi ta yi murmushi ta ce "Anty farida, ai daren yayi tsayi, ke ce ba ki farga ba, sai da garin ya waye. Duk da kina iƙirarin uwata ba ta da hankali, amma a hakan ta din ga yi mini nasihar, jin tsoron Allah, riƙe addu'a da biyayya a aure, idan har tsoron Allah, addu'a da yi wa miji biyayya na saka a ci ribar aure, da yardar Allah ni da uwata mun fi ƙarfin masu bin ƴan tsubbu, kuma zamu zauna dai-dai a gidan miji, namiji ba shi da tabbas, ya danganta da yadda ki ka ɗauke shi ne, nawa yana da tabbas, haka babana dr., Ke ce baki iya tattalinsa ba ki ke ganin ƴan tsubbu sun mallake miki shi, shiyasa ki ka ga bashi da tabbas".
Chapter 123 · 0% Book details