← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 134

Sashe 114

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sosa kai ya ce "Ai kawai muna zaune ne da salman, magani nake nema"

"Amma ba dawowarku aka ce tayi ɓari ba?" Tayi maganar a hasale.

Ya ce "Eh, amma bani da lafiya, dan Allah idan ba asirina ki ke son ya tonu ba, dan Allah mami ki bar maganar auren nan na samu magani"

Yadda raihan ke tsara maganar kawai Alhaji ya san ƙarya yake yi, yayi wani irin ƙasaitaccen murmushi na manya ya ce "This is serious, dole a jinkirta maganar nan, dan wannan ba issue ne ƙarami ba"

Ba tare da mami ta ce komai ba, ta hau zancen zuci, da ƙoƙarin gane ƙarya raihan yake yi, ko kuma da gaske? To me za ta cewa su Safiyya? Amma ba shi da lafiya ummi ta yi ɓari".

"Kin ga bilki, ki tashi ki je zamu yi magana da shi" Ummi ta yi wa raihan wani mugun kallo, amma yaƙi kallonta.

Bayan ta fita Alhaji ya yi ƴar dariya ya girgiza kai ya ce "Ɗan zamani da uwar zamani, tashi ka je Allah ya shiryeka babban mutum" ko a jikinsa ya tashi ya bar falon, dan dama haka yake so, kuma ya ƙudirce idan mami ta cigaba da uzzura masa sai ya gaya wa safiyya da Yaya rakiya ba shi da lafiyar da zai auri safiyya ummi ma rufa masa asiri take yi.

Ganin ya kwantar da tarzomar wannan maganar, ya sanya ya sake tatara hankalinsa a kan neman ummi.

Ya ɗauki wayarta yana duddubawa, ya tarar da gmail a wayarta, wani babban gidan talabijin na jamus, suna son bawa ummi aiki. Idan tana da buƙata ta tura takardunta ayi interview da ita. Tsaki yayi ya ajiye wayar ya dafe kansa yana tunani, ko a gidan ubanwa ma suka san ummi oho.

Managern su ne ya faÉ—o masa, dan ya gaya masa yadda ummi ta É—auki hankalin mutane.

Ranar da aka fara shari'ar su ummi, ba ta je kotu ba sai lawyernta, kasancewar ATM É—in ta na hannunta, kuma raihan yana saka kuÉ—i a cikin account É—in ta, ya sanya ta saki kuÉ—i.

Alƙali ya bi komai tiryan-tiryan, tare da neman a kawo duk wani abu da aininhin kakan su ummi ya mallaka, da yayyensa suka hau suka turmushe, a zama na gaba.

Su kawu Ilyasu suka cigaba da kururwar neman agaji, suna kiran Abdul a waya, ya ce shi ba abun da zai iya yi, tun da ba a san in da take ba.

Sati É—aya aka koma kotu, Aka je da komai na kakansu ummi. Gidan da suke ciki, aka ce ba zai rabu ba, saboda wasu sun rasu sai Æ´aÆ´ansu, wasu duk sun ja wuri sun yi gini a ciki, sai dai a yi wa gida kuÉ—i, a raba a fitar da gadon ummi, da tumunin mahaifiyarta, sai su biya su.

Duk wannan abun, ƙarƙashin jagorancin lawyern ummi ake yin sa, dan ko sau ɗaya ba ta je kotun ba.

Aka shafe wata guda da sati biyu, ba ummi babu labarinta, har Abdul sai da hankalinsa ya tashi, wurin neman ina ummi take?.

Mami ta ce zata saka raihan a gaba ta nema masa magani, ya ce mata shi yana zuwa wurin likita ana duba shi, dan ta san komai za ta yi ba zai sha maganin hausa ba.

Amma duk da haka ba ta haƙura ba, ta cigaba da saka pressure sai da aka kai kuɗin nan!

Raihan duk yayi baƙi ya lalace, gashi kwatsam! Dr. Yayi masa magana a what's app cewar ba ya samun ummi a waya, shi ma tasa wayar ce ta lalace amma kwana biyu ba ta gaishe shi ba.

Raihan ya yi masa ƙaryar ita ma ta ta wayar ta lalace amma zai haɗa su.

Duk wannan abun, Salim bai kuma tsoma baki a kan lamarin raihan da ummi ba, gashi bin ƙwƙƙwafin da Alhaji yake yi, yana daf da gano ummi ba ta nan, dan kuwa yana ta cewa raihan kwana biyu fa bai kawo sirikarsa sun gaisa ba

Gagarawa kuwa, da ummi da mariya aka yi ƙiyasin suna da naira miliyan uku da rabi a gidan, dan haka Alƙali ya ce  ko su kawo wannan kuɗin su fitar da ummi da mahaifiyar ta, ko Alƙali ya saka gida a kasuwa a sayar, a sallame su, kuma aka basu wa'adin sati biyu.

Sun san ko giyar wake suka sha, ba su da wannan kuɗin, ga kotu ta saka an yi wa sauran gonakin su kuɗi, za a cire gadon bashir, sannan a cire na ummi da mariya. Alƙali ya ce su haɗa su biya su ummi, sai su riƙe gida da gonaki.

Raihan yana office baya gane komai, wayarsa ta fara ringing, ya É—aga a hankali ya kara a kunnensa.

"Barka da rana" tayi maganar cikin sassanyar muryarta. A zabure ya tashi tsaye yana faÉ—in "Ummi, kina ina? Ina ki ka shiga haka?"

"Ina nan cikin ƙoshin lafiya" ta bashi amsa.

"Haba Salma, kin san yadda ki ka tayar mini da hankali kuwa? Kina ina ki tsaya na zo na É—auke ki".

Ummi ta ce "Ka zo ka kawo mini takarda ta dai. Dan Allah wani abu nake son ka yi mini, family house É—inmu na gagarawa kotu za ta saka a kasuwa nan da sati biyu, dan Allah da an saka a kasuwa idan kana da hali, ka sai gidan ka basu short notice su tashi, da k yi haka zan gaya maka in da nake a Maiduguri ka zo ka kawo mini takardata, kar kuma kayi tracking É—ina, sannan bana gidan mama, naira miliyan goma sha huÉ—u aka yi masa kuÉ—i burina kawai ka sayi gidan ka tashe su!"

Turus raihan ya yi yana kallon wayar, me zai saka ummi ta yi haka? Lallai akwai wani abu a ɓoye, amma idan har zai ganta kuɗi ko na Alhaji ne zai ɗiba ya sai gidan kamar yadda ta buƙata, duk da bai san dalilinta na yin hakan ba!

Ayshercool
08081012143.

I hit the jackpot with PalmPay! Join PalmPay with my link or my code 'XWPK6722' within 72 hours to help me get my gift! >>https://link.palmpay.com/uwyy6

Team Ummi wanda ba su taɓa cike palmpay ba, dan Allah ga refaral ɗina a bi link a cike mini.

Ayshercool.
08081012143

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

                      *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

44

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
44

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Amma meyasa ki ka yanke wannan hukuncin?"

Cikin nutsuwa ta ce "Saboda na zama abun da ake so na zama"

"Me kenan?"

"Zaka ji daga baya" ta bashi amsa.

"Zan saya, amma dan Allah ummi kina ina, duk hankalina a tashe, Alhaji na daf da gano gaskiya ba ma tare, idan ya gano ina cikin matsala dan girman Allah kina ina?".

Ummi ta ce "Kai da zaka yi sabon aure, meye na damuwa da ni? Idan komai ya kammala ka tabatta ka taho mini da takardata, da zan nuna wa dr. Shaida, sannan ban ce ka gaya wa kowa mun yi waya ba, ka yi shiru da bakinka"

"Ummi.... Ta kaste wayar ta sakata a flight mode, dan kar ma ya sake kiranta.

Ta ƙurawa wayar ido, tabbas tana kewar raihan ɗin ta nesa ba kusa ba, ji tayi kamar ta yi kuka wannan abun da ta yi masa, gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi amma dole ta ƙaurace masa dan samun cikakkiyar nutsuwa dan ta san da ya lallaɓata shikenan ba zata iya taɓuka komai ba.

Raihan yayi ƙoƙarin bin ummi, amma ta ƙi shiga wayar. Ya zubawa wayar ido yana lumshe ido, a hankali ya furta "Alhamdilillah, tun da kina lafiya"

Su kawu Ilyasu hankali ya ƙi kwanciya, saboda kuɗi babu su babu dalilinsu, gashi ba su san in da ummi take ba, balle a lallaɓata a rarrasheta su bata haƙuri, ba su taɓa zaton zata aikata abu makamancin wannan ba, yarinyar da suke wa kallon ko yatsa aka saka mata a baki, ba za ta iya cizawa ba.

Iya kuwa ta tsinewa ummi da mariya babu adadi, ta zageta har ta gaji, ba tare da ta ji alamar ta huce daga takaicin da ummin ta sanya su ba, ba ta taɓa tunanin ummi za ta aikata haka ba.
Chapter 114 · 0% Book details