Sashe 31
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shikenan, amma kar ki kuskura ki zo kina ce mini an yi miki kaza an yi miki kaza"
"Na ji wacece waccan yarinyar da ka haÉ—a mini da yara?"
"Dama na san ba saninta zaki yi ba, tun da ba zuwa ki ke yi ba, Ƴar wurin marigayi ce bashir?"
"To me zata yi a nan É—in?"
Ya gyara zamansa ya ce "Eh, na ɗaukko riƙonta ne na dawo da shi hannuna, a nan za ta zauna da mu"
A fusace ta ce "Amma yaya zaka yi mini haka, ya zaka ɗaukko yarinya ban sani ba ba shawarata kawai ka ce in riƙe? Saboda me? Abba meye amfanin kawo bare ka haɗa a cikin iyalinka".
"Ƴar ɗan uwan nawa ce bare kuma?"
"Bare ce mana, ki ka haifeta? Naga ai ba cikinku ɗaya da ubanta ba, gaskiya ban yarda ba, ka mayar da ita in da ta fito wallahi ba zan iya ba, dama dinginku sun tsane ni, shi ne aka haɗoka da ita ta zo ta saka mini ido, wallahi ba zan riƙe ba".
Ya dubeta ya ce"Well, ummi bare ce, amma ko ba komai ƴa ce a wurina, idan har ummi za ta bar gidan nan, ki tabattar rahama ma sai ta bar mini gida, dan bani da wata alaƙa da ita, dan ina aurenki ba dole ne na riƙe ki na riƙe ƙanwarki ba, tun da baki san mutunci ba, a gobe in Allah ya kaimu rahama ta bar mini gida na gaya miki".
"Yahaya, ni ka ke gayawa ƙanwata ta bar gidan nan?"
"Tun da ki ka iya kallona ki ka ce, ƴa ta ta bar gidan nan, to rahama ma sai ta bar gidan nan tun da ko ban riƙeta ba, bani da laifi a wurin Allah, ummi kuwa dole ne riƙonta a kaina" ya tashi fuuu ya nufi ɗakin su intisar.
Ummi na zaune a ƙasa rungume da kayanta, tana kallonsu, suna zaune a kan gadonsu, sun sakata a gaba suna ta dariya, saboda yanayin ƙauyanci da yake tare da ita da kuma baƙar fatarta.
Sallamar babansu ce ta sanya su tashi a razane, suka daina dariyar.
"Ina ruwan wankan da na ce a bata?"
Intee ta ce "Anty rahama ba ta haÉ—a ba"
"Wannan ban isa da ita ba, ku na isa da ku, ki haÉ—a mata ruwa ki nuna mata yadda ake amfani da toilet É—in"
Ta jinjina kai, ya juya ya fita dan tafiya masallaci sallar isha'i.
Cikin ƙyama take nunawa ummi banɗakin, ƴar ƙarama da ita, amma ta iya wulaƙanci.
Ta cewa ummi kar ta kuskura ta taɓa musu sosunan wankansu, ta je ta ɗaukkowa ummi sabulun wanki, ta bata wai tayi wankan da shi, ta kuma nuna mata iya in da zata tsaya, tayi wakan.
Ummi ta jinjina mata kai, sai dai ta tsaya tana kallon banɗakin yadda ya ƙawatu.
"Rahama kina ina, wai ni yahaya ya ɗaukkowa ƴa a ƙauye na riƙe, wai idan ba zan riƙe ba kema ki bar masa gida"
Rahama ta kalleta ta ce "In bar gidan nan wai? To me ki ka ce masa".
"Wallahi ba zan riƙe ba, kuma ba in da zaki je, shi ya isa ma, wallahi yayi kaɗan, zai gane kuskurensa".
Rahama ta ce "Anty ke da ki ke neman ƴar aiki? Gashi kin samu a ɓagas, ba dai gida ne ba, ta zauna mana iya ka idan bala'i ya isheta ta gaji ta bar gidan nan, ki rabu da shi, sai dai karki saurara mata wallahi, idan ma sa ido aka turo ta ki ci ubanta, ki rabu da shi kawai"
Ta ce "Kuma fa haka ne rahama, haka za ayi, ɗakin mai aiki kawai zata koma, na samu baiwa zata ci ubanta kuwa, sai ta koma in da ta fito dan ba zan zauna da ita ba wallahi. Nifa gaba ɗaya ban yarda da yarinyar nan ba, lokacin da muka je gaisuwar babanta, ina jin kakarta na ta ce mata kamar mayya, ke kin ganta baƙa ƙirin ƙwayar idonta kamar mage".
Raham ta ce "Idan ma mayyar ce ta ci kanta, dan wallahi mun fi ƙarfinta, to ma ina uwarta da za a kawo miki ita? Gaskiya baban Abdul yana da matsala wallahi".
"Oho masa, sai ta bar mini gida dai wallahi, amma na san yadda zan yi da shi".
Ayshercool
08081012143
             *CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
(Ku garzaya YouTube channel ɗina na COOL HAUSA NOVELS, KU YI SUBSCRIBING, AN FARA ƊORA LITTAFIN ƘANWAR MAZA NA SAURARO)
P14
Har kawu yahaya ya dawo daga sallar isha'i, suna tattaunawa ita da rahama, suka gama ƙulle-ƙullensu, sannan farida ta baro ɗakin rahama.
Yahaya ya tafi ɗakin yaransa, in da suke ta tsalle-tsalle a ɗakin, ummi kuma na ta gyangyaɗi a zaune a ƙasa.
Suna ganinsa suka tsagaita da tsallen da suke yi, ya kalli babbar ya ce "Ke intee, ku yi squating da kausar a kan gadonki, yaya ummi ta kwana a kan É—aya gadon.
Turus suka yi suna bin mahaifinsu da kallo, cikin tsawa ya ce "Ba ku ji me na ce ba ne?".
Intee ta ce "To" ya kalli ummi da ta buÉ—e ido ya ce "Ummana, ga gado nan tashi ki kwanta kin ji"
Ummi ta ce "To na gode"
Ta tashi ta hau gadon nan ta kwanta, wani irin laushi, ga ƙamshin room freshner mai daɗi kayan shimfiɗar suke yi, tun kan ya bar ɗakin bacci ya fara kwasarta.
Inteesar ta kwashe wa da kausar da dariya ta ce "Shikenan bedsheet ɗin ki zai kwashi baƙi, kamar an ciro a buhun gawayi".
Kwaɓe fuska kausar tayi za ta yi kuka, intee ta cigaba da dariya, ganin kausar ta fara kuka ya sanyata cewa "Bari idan abba ya daɗe da tafiya, sai mu tashe ta, ta saukko".
Haka kuwa aka yi, intee har da leƙawa, ta tabattar da ya tafi, sannan ta dawo, ta hau dukan ummi a ƙafa.
Ummi ta buÉ—e idonta tana kallonsu.
"Saukko mana daga kan gado, kausar zata kwanta"
Kasa magana tayi ta cigaba da bin su da kallo.
"Ki saukko zata kwanta, dan ba zata kwana a gadona ta matseni ba" babu musu ummi ta saukko, ta koma ƙasa ta sake tada kai da kayanta.
Kausar ta watso kayan kan gadon nata, har bedsheet É—in da komai, wai saboda ummi ta kwanta a kai.
Wajen ƙarfe ɗaya na dare, ummi ta ji ana haurinta da ƙafa, ta tashi firgigit, dan ji tayi kamar a gidan idris za ta buɗe ido ta ganta, dan shi yake yi mata irin wannan wulaƙancin, na haurinta da ƙafa.
"Tashi malama, in nuna miki in da zaki din ga kwana, dan ba zaki kwanar mini a cikin yara ba, ban san irinki ba"
Kai ka ce sokuwa, haka ta tashi, ta É—aukko jakar kayanta, ta bi bayan farida.
ÆŠakin Æ´ar aiki da yake farkon falon, ta nuna mata ta ce ta shiga a nan zata kwana. Ba ta damu da a yaya É—akin yake ba, ta je ta kwanta, saboda yanayin jikinta ga rashin lafiya ga gajiyar tafiya, dan haka duk a gajiye take.
Washegari da safe, kowa ya fito falo, rahama ce ta haÉ—a breakfast, yaran duk sun shirya cikin uniform na makarantar boko.
Abba ya fito ya kallesu É—aya bayan É—aya babu ummi, rahama ta gaishe shi ya amsa sama-sama.
Ya kalli farida ya ce "Kawo mini abincina nan"
Haushi ne ya kama ta, yana ganin yadda take fama da ciki, amma ya sakata aiki, bayan ta kai masa kayan abincin É—aki.
Bayan ta tafi É—aukkowa, ya kalli intee ya ce "Kirawo mini ummana" intee tayi saroro tana kallon shi.
Ya ce "Ummi nake nufi"
Tunawa tayi da safen nan, ta ji maama da anty rahama suna zancen a É—akin mai aiki ta kwana, har take gaya musu abun da suka yi mata jiya da daddare suka din ga dariya.
A zaune ta tarar da ummi, ita ummi ɗakin ba ƙaramin kyau yayi mata ba.
Duk da ba wani abu a ciki na burgewa, amma É—akin ya yi mata kyau.
"Ki zo in ji abba" yarinyar ta faÉ—a cikin fitsara.
Ummi ta tashi ta bi bayan ta, sai dai farida na ganin ummi kamar taga kashi, ta haÉ—e rai.
Daga in da suka fito falon, ya fuskanci a in da ummin ta kwana.
Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Abba ina kwana?"
"Lafiya ƙalau ummana, ya jikin naki, ina fatan baki kwana da zazzaɓin ba?"
Ta ce "Eh da sauƙi".
Ya ce "Masha Allah, baki gaisa da maman naki ba, gata nan sunan ta farida, yara na kiranta maama, kema zaki iya kiranta da hakan, ga ƙanwarta nan anty rahama, ga Abdurrahman Abdul, ga inteesar, ga kausar, sai kuma muna jiran unborn baby da maama zata haifa mana. Abdul, intee, kausar kamar yadda na gaya muku jiya, yayarku ce, duk da kai Abdul ka girmeta, amma ku girmamata, ku zauna lafiya. Ummina duk abun da ki ke buƙata, ki sanar da ni, ko maama gidanku ne ki yi zamanki ki kwantar da hankalinki".
Cikin ladabi ummi ta ce "To Abba" ta kalli farida ta ce "Ina kwana" banza tayi da ummi kamar ba ta ji abun da ta ce ba, ba ta damu ba ta kalli rahama ta ce "Anty ina kwana"
Ba yabo ba fallasa rahama ta amsa mata, abun da farida tayi, ba ƙaramin ƙular da shi tayi ba, bai ce komai ba da kansa ya haɗa wa ummi abun breakfast a abincinsa, ya bata.
Wanda hakan ba ƙaramin tunzura farida yayi ba, cikin ƙulewa take tuna masa yara zasu makara a makaranta, amma ya kada baki ya ce "Ƴaƴanki ne ai ki tarar musu abun hawa ya kai su, ƴa ta zan kai asibiti"
Tsit suka yi suna kallonsa, aka rasa mai magana, ya jira ummi ta gama, ya sakata a gaba suka fice.
Sai da ta kusa kuka, abun ka da mai ciki dama ga zuciya a kusa.
"Rahama ki na kallo daga kawo yarinyar nan, ni zai yi wa wannan wulaƙancin, ya fifita bare a kan yaransa".
"Kema anty farida you over react, a gabansa ta gaishe ki, ki ka shareta, ai kisan mummuƙe zaki yi mata".