← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 134

Sashe 87

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tuno lokacin da ya ɗaukkota daga gagarwa a wahale, ba sutura ga ciwo, ko ba komai ta samu alkhairi a dalilin riƙonta da yayi

A ranta ta ce "Allah sarki kawuna, baba ya tafi amma ya bar mini Allah, Allah kuma ya bani kai, Allah ya kula da kai da zuriyarka".

Duk da ba ga saba baccin mota ba, gajiya ta sanya wani irin nannauyan bacci yin awon gaba da ita.

"Mamana tashi mun zo" a hankali ummi ta motsa tare da buÉ—e idonta, har suka fito daga cikin motar, ba ta iya cewa komai ba, sai bin wurin da kallo.

Ƙofar wani gida suka tsaya, dr. Ya ciro wayarsa ya ɗan daddana ya kara a kunnensa ya ce "Gamu mun zo"

Wani matashin saurayi ya leƙo ya durƙusa ya gaida dr. Sannan ya ce su shiga.

Suka shiga cikin gidan, ummi ta zubawa dattijon da suka tarar a tsakar ido, yana zaune a kan buzu, da Alƙur'ani bugun warshi a gabansa.

Dattijon ya miƙe tsaye yana yi musu maraba, tare da bin ummi da kallo, ba ta ɗaga niƙabin fuskarta ba, sai dai ta shagala da kallon sa ta san shi, amma a ina? Ta kasa tunawa.

Yayi musu jagora har wani matsakaicin falo, yana ta yi musu sannu da zuwa.

Suka gaisa da dr. Ummi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa, sai dai bai tambayi wacece ba, kuma ya kasa daina kallonta.

Dr. Ya ce "Ina mutuniyar kuwa?"

"Wai sun fita barka a nan bayan layi, jikin ne ma ya É—an motsa, amma Alhamdilillah mun gode Allah, bari azo a É—ora muku girki, ai bamu san zaku zo ba"

Dr. Ya ce "Ai alƙawarin da na ɗauka na zo cikawa, zuwan babu cikekken shiri, bari mu yi salla kafin su dawo".

Ya ja dr. Suka fita, bayan nuna wa ummi banÉ—aki, tayi alwala ta yi salla, ta nemi wuri ta kashingiÉ—a tana hutawa, saboda gajiyar da tayi.

Ummi ta É—an jima a zaune, sannan dr. Ya shigo, shigowar ta sa yayi daidai da shigowar matashin da ya yi musu iso, ya kawo musu nono mai sanyin gaske, da nama fal malam ya ce a kawo musu da ruwa, dan azo a É—ora sanwa.

Ummi dai ta kasa sakewa ta ci, dr. Kuma sai hira suke yi da malam.

Dr. Ya ce "Malam ba ka ganni da baƙuwa ba ne? Baka tambayeni wacece ba"

Malam yayi murmushi ya ce "Tun da baka gaya mini ba, bai kamata na yi shishshigi ba ai, na ma zata ko mai ɗakinka ce, shiyasa ban yi magana ba, kuma na ganta sanye da niƙabi"

Dr. Yayi murmushi ya ce "Aishikenan, mama malam ne fa, baki gane shi ba?"

Ummi ta ce "Na sanshi amma na manta a ina?"

"To ki cire niƙabin ko zai gane ki"

Ummi ta jinjina kai tana ƙoƙarin cirewa, aka  yi sallama.

Bayan matar farko ta biyun ma tayi, a nan take ummi ta daskare, ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ta ji tamkar numfashin ta zai bar ƙirjinta, wata irin tsuma ta ji ta fara yi, amma ta gaza motsawa.

Malam ya ce "Daga zuwa barka kun yi zamanku, gashi kun yi baƙi tafiyayyu daga kano"

Ta ce "Baban ummi ne?"

Malam ya ce "Eh shi ne, tun da shikaÉ—ai ki ka sani a kanon ba"

Shigowa suka yi tare, tana riƙe da mayafinta a hannu, hannunta kamar amarya an yi mata lalle yayi jawur.

Ba ta kalli baban ummi ba, kai tsaye ummi ta zubawa ido, yayin da ummin ma ta zuba mata ido, tana jin yadda ƙirjinta ke lugude. Gaba ɗaya suka zuba musu ido, kai tsaye ta nufi ummi ta zauna a gabanta, tana cigaba da kallon ummi ta niƙabinta.

Ta miƙa hannu a hankali ta ɗaga niƙabin ummin, tayi tozali da fuskar ummin da a duniya bata ganin kyan komai, kamar yadda take ganin kyawun wannan fuskar.

A gigice ummi ta yi mata wata irin runguma ta fashe da matsanancin kuka, saroro mariya tayi, ta kasa taɓa ummi sai hawaye da ya fara zuba daga idonta.

Mama ta miƙa hannu tana faɗin "Ki yi mata a hankali ba ta da cikakkiyar lafiya"

Mariya ta buge hannun maman da ƙarfi, ta ruƙunƙume ummi, tana wata irin ajiyar zuciya kamar za ta fita daga hayyacinta.

Ta miƙa hannu ta warware mayafinta, ta lulluɓe da ummi da shi, ta ɗaukko mafici kuma tana yi mata fifita tana kuka.

Sai a yanzu suka gane wacece, malam ya sunkuyar da kai yana hawayen tausayin Æ´ar sa.

Ya zura hannu a aljihunsa ya É—aukko wayarsa, ya kira Maryam a waya da kuma yaya É—an lami.

"Ummina, kina cin abinci kuwa? Naga duk kin rame, iya tana yi miki wanka? Ko dai zazzaɓi ne a jikinki?" Tayi maganar tana ɗora hannu a goshin ummi.

Wasu irin jijiyoyi suka ɗaɗɗaga a goshin ummi, wani irin riƙo take yi wa mariya, tana jin kamar an sanyata a wata ni'ima.

Sun fi mintuna talatin a haka, sun ƙi sakin juna, mariya sai kakkare ummi take yi, kar wani ya taɓa mata ita.

Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Yau na cika alƙawari ko?"

Ta jinjina masa kai, tana kuka ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafe wa iya ba, Allah ya saka mini zaluncin da ta yi mini, ta ƙwace mini ummi bayan ba son ta take yi ba, ta ce ni na kashe mata ɗa, kalli yadda duk ummi ta rame, haka zan kwanta in yi ta mafarkin ummi tana kuka, tana cewa na zo na tafi da ita"

Ta ɗago ummi tana goge mata hawaye ta ce "Ki daina kuka kin ji ummana, ba zan sake bari a mayar da ke wurin iya ba, na san ba ta sonki ba ta ƙaunarki, ban san me ki ka yi mata ba, wallahi ba zan yafe mata ba, yaya ɗan lami yaƙi dagewa ya karɓo mini ƴa ta, kullum sai na yi kuka saboda ummi, yaya maryam ma ta hantare rannan wai kamar nikaɗai ce me ƴa, ki daina kuka kin ji ummina, da kaina zan din ga yi miki wanka, ina baki abinci, katifata zata ishemu mu din ga kwana tare, ba zan sake bari a kai ki wurin iya ba kin ji mamana"

Ummi ta ƙura mata ido, yadda mama ke wannan surutan daga wannan zuwa wancan tare da kasa gane ummi ta girma yanzu, ya tabbatar wa da ummi cewar mariya bata da lafiyr ƙwaƙwalwa.

Ta miƙa hannu ta ɗaukko ledar pure water, ta buɗeta ta saka wa ummi a baki tana faɗin "Na san ƙishirwa ki ke ji ummi, sha ruwa kin ji"

Babu wanda tausayin ummi da mariya bai kama a wurin ba, uwa kenan duk da ciwon ya motsa ba ta hayyacinta, amma hakan bai hanata gane Æ´ar ta ba, duk da shekarun da suka shafe basu haÉ—u ba.

Dr. Yayi gyaran murya ya ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na gode Allah da ya sanya ummi da mahaifiyar ta suka haÉ—u, ba tare da ta Allah ta kasance ba. Ummi na yi miki laifi, kuma na yi muku duk da ina godiya da fahimta ta da ku ka yi.
Ummi ban ƙi sada ki da mahaifiyarki dan baƙanta miki ba, a lokacin da na ganota, tana cikin halin larura sosai, ba komai take ganewa ba, na yi fargabar haɗuwarku ba za ta yi daɗi ba, idan ku ka haɗu ta kasa gane ki, abu na gaba kuma ina tsoron halin da ki ke ciki, ya sanya ki ƙi zama ki dawo wurinta, alhalin kina tsaka da karatu, dan duk wanda yake ruwa, ko takobi aka miƙa masa zai kama, dan haka a matsin nan da ki ke, duk da kasancewar ki mai biyayya, zaki iya bujirewa ki zaɓi dawo wa gaban mahaifiyarki, ba tare da kin yi acheiving wani abu ba.
Wanda a lokacin babban burina da fatana, ki samu nagartaccen ilimi, da zaki iya tsayawa da ƙafafuwanki, ina fatan zaki yafe mini daga ke har mahaifiyar ki" yayi maganar a sanyaye.

"Ai dama kai na yafe maka, baka cuceni ba, amma iya iya iya, ban san me na yi mata ba, amma za ta maimaita a gaban Allah, amma wallahi ba zan yafe ba, na ji labarin azabtar mini da ummi ta yi, amma yaya ɗan lami ka ƙi dagewa ka karɓo mini ummina"

Dr. Ya ce "Haba maman ummi, ki yi haƙuri abun da ya wuce ai ya riga ya wuce, ki yi haƙuri dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa.

"Ai kai na ce na yafe maka, tun da ka kawo mini ummi, kuma kana saya mini magani da abun da nake so, har yaya ɗan lami na yafe muku, amma ban da iya da wanda suka ci zalin ummina, bani da abun da zan gani na tuna da bashir sai ummi, amma ta ƙwace mini ita dan ta wulaƙanta ni"

Dr. Ya ce "Ba gani a gabanki kina kallona ba?"

"Yaya Yahaya ne fa ba Bashir ba, na gane ka yau" yayi murmushi ya fahimci memoryn na ta yana yi yana seizing ne.

Sun sha mamakin yadda ummi ta girma, ummi kuma kallon mamanta take yi, kamar ba ita ta haifeta ba, haryanzu shar da ita, gashi gaba ɗaya ba sa kama, sai kaɗan, kamar ya da ƙanwa ba uwa da ƴa ba.

Dangin mama kamar su cinye ummi, a yamamcin nan suka din ga zaryar ganin ummi, sai dai ta ɓoye ummi a bayanta, kowa ya zo sai dai ya hango ummi daga nesa wai kar a ɗauketa a mayar da ita wurin Iya.

Ummi ta ga ƙauna da soyayya, mariya ta din ga zuba mata hira, wata tana ganewa, wata ba ta ganewa, ummi space take son samu, ta kira raihan a waya ta sanar masa.

***

Raihan yana zaune a falon hajiya Aisha yana kaɗa ƙafa, yana danna wayarsa cikin damuwa, ya kasa samun ummi a waya.

Falon ta shigo cikin takunta na ƙasaita, ta samu wuri ta zauna ta kalli raihan ta ce "Kai, babanka ya kasa samunka a waya, yana ta ƴar murya a lallaɓoka ka koma fa"
Chapter 87 · 0% Book details