Sashe 2
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ohh, Ummi Allah ya shirya mini ke, an girma amma ke ba kya girma, kamar ba ƴan mata ba" gaba ɗaya ummi hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai da sosai, sai dai kasancewar ita kan ta mariyar yarinya ce, shekarunta sha takwas, a zaton ta kawai rigima ce, kasancewar ummi, yarinya mai azabar ƙyuya da miskilanci.
A nan tsakar gida ta yasar da biskit ɗin, ta je ta rirriƙe mahaifiyarta, ana daf da sallar magariba, mahaifin ummi ya dawo, ya ɗauke ta yana juyi da ita a tsakar gida, yana faɗin "Ummi, waye ya taɓa ni ƴa ɗaya tilo, na ga kamar kin sha kuka? Ko dai kin daketa ne?" Yayi maganar yana kallon mariya.
"A'a wallahi, ƙyuya ce kawai, ba zata yi wasa a cikin yara ba, ta maƙalƙaleni, dan idris ya ɗauke ta take kuka".
"Ki daina ƙyuyar nan dan Allah, na zo miki da alewa daga kasuwa, da yalo ai kina ci ko?".
But iya ta fito daga ɗakin ta, "Balarabe wannan ƴar ka sunkuta ka ke shillawa sama, sai ƙirjinka yayi ciwo tukuna ko?"
Yayi murmushi ya ce "Iya guda nawa ummin take"
"Ajiyeta dan Allah, duk a haka ku ke sangarta ta, tayi ta taɓara tana iskanci, ƴa sai ka ce teba" cikin jin nauyin mahaifiyar sa, ya ajiye ummi, yana murmushin yaƙe.
"Ina alewa da yalon da na ji ka ce ka zo da su? Bani nan a rabawa sauran yaran gidan, ai ba ita kaÉ—ai ce Æ´a ba, nan idirs yanzu ya fita da ita ya kaso mata uban kuÉ—i, amma kai sai ka zo da abu ka hana sauran yaran? Saboda ka haifi gwal?"
"A'a Inna, ina sayo da su suma, gani na yi ita ce ƙarama, kuma yau kasuwar sai godiyar Allah, tun da ba ranar kasuwa ba ce ba, ɗan kaɗan ne na zo da su ba yawa" yayi maganar yana nuna mata ƴar ledar hannunsa.
Ta ƙaraso ta fizge ledar "To tun da ba ciniki, sai ƴar taka ta haƙura, kai dai balarabe kamar a kan ka, aka yi wahayin talauci, kullum kasuwa ba cigaba, kana kallon yadda ƴan uwanka suke ƙoƙari kowa da abun arzikin sa, kai kuwa ba ka ajiye komai ba, sai son mace da wannan mummunar yarinyar, daɗi aure ba zaka zage ka nemi arziki ba" shiru yayi ya sunkuyar da kansa, dan ba shi da abun cewa.
Mariya kuwa ta mayar da hankali wurin kwashe tuwo, roba-roba.
Malam Hashimu dodo, shi ne mijin iya, gidansu babban gida ne, da aka yi ittifaƙin babu gidan da ya kai su yawa.
Da yayi aure ya ja nasa ɓangaren a cikin gidan su. Kasancewar gidan babba ne sosai, dan kusan duk garin babu mai girman gidan.
Kowa ya san su, saboda galibi ƴan gidan manoma ne, sai masu taɓa kasuwanci, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado.
A hankali wasu suka din ga samun rufin asiri, suna watsewa daga gidan, malam hashimu yana sake shigar da wasu sassan nasa sashin.
Daga baya ya auri iya, bayan matarsa ta ladan noma wato salamatu. Malam Hashimu mutum ne mai hidimtawa iyali, a lokacin boko ba ta yawaita ba, sai karatun allo, dan haka da shi da Æ´an uwansa suna da ilimin soro.
Bayan wani lokaci, salamtu ta mutu, ta bar yaranta huɗu, biyu mata biyu maza, iya ta cigaba da riƙon su, da nata ƴaƴan.
Sai dai iya macece me shegen son abun duniya, tamkar ta yi ƙwace, ga ta da iya fuska biyu, a waje ta nuna ta Allah ce, amma na cikin gidan, su suka san gashin da suke sha.
Ba Æ´aÆ´an da aka bar mata ba, har facalolinta, da suke cikin gidan iya na azabtar da su, gwargwadon abun hannunka, da abun da ka ke bata, gwargwadon mutuncinka a idonta.
Aka aurar da Æ´aÆ´an salamatu mata, É—ayan kuma Yahaya, ya ce shi karatun boko yake so. Iya tayi ta sukar abun, amma malam Hashimu da suke kira da baba ya bashi goyon ba.
Ƙaninsa kuma Ilyas, yana zaune a nan ƙauye, amma yana taɓa kasuwanci, nan da nan ya fara tara kuɗi, yayi wuf yayi aurensa, shima ya tare a cikin gidan.
Yaran iya su biyar, biyu mata Shafa da zaliha, uku maza, Sagir, Saminu, sai Bashir wato balarabe. Duk wanda yake da kuÉ—i shi ne nata, hatta a jikokinta bambanci take nunawa muraran, sagir ne babba shine baban Idris da kuma Hashim suna ce masa magaji, saboda sunan malam ne da shi.
Akwai tarin Æ´aÆ´a da jikoki a gidan, bayan rasuwar iya ita ke tafiyar da gidan, saboda azabar faÉ—anta da iya masifa, hatta Æ´an uwan malam tsoron ta suke ji, abun da ta dama shi ake sha.
Saboda balarabe ba shi da kuÉ—i, wato baban ummi, duk gidan shi ne samunsa ba mai yawa ba, dan dako yake yi a kasuwa da Æ´an buge-buge dan haka samun nasa galibi sai damina idan yayi noma, hakan ya sanya duk wata É—awainiyar gidan ta wahala, iya ta sa matarsa mariya ce ke yi, wadda asalinta Æ´ar Maiduguri ce babarbariya ce, sun zo garin biki suka haÉ—u, har Allah ya sa suka yi aure.
Tun da mariya tayi haihuwa ɗaya ta haifi, yarinyarta aka saka mata sunan mahaifiyarta, wanda yayi dai-dai da sunan uwar gidan malam, wato Salma ba ta sake haihuwa ba, tsawon shekaru uku kenan, iya ta ɗorawa yarinyar nan Ummi ƙahon zuƙa, da ba'a da cin mutunci, wai ta haifi wata halitta daban, da babu irinta a danginsu.
Ba ita ba har yaran gidan, da sauran mutanen gidan, na yawan kushe halittar ummi, tare da tsokanarta, gashi ayi ta tankata, saboda baƙinta, da kuma ƙibar ta, ga kuma kalar idonta, sai dai kuma mutane na mamakin irin gashin kanta, dam idan mariya na gyara mata kai, ruf gashi yake rufe mata fuska, tamkar na larabawa.
Allah ya albarkaci gidan malam Hashimu, da yawan yara maza a jikokinsa da Æ´aÆ´ansa, mata sam ba su da yawa, kuma da sun tasa ake aurar da su.
Dan haka kusan ummi, ita kaɗai ce yarinya mace ƙarama a cikinsu, sai dai hakan ya zame mata babbar barazana ga rayuwarta!!!
08081012143
           *CUTARWA!*
Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube Cool hausa novels
What's app 08081012143
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
P2
Yawan kyara da hantara, haɗi da kushe halittar ummi, ya sanya ta zama yarinya mara karsashi ko a cikin sa'aninta. Dan wasu har iƙrari suke ko mayya ce, saboda launin ƙwayar idonta da ta sha banban da ta sauran mutane.
Wasu lokutan mariya duk sha'anin da za ayi na taron mutane, ta kan iya haƙura da zuwa saboda ummi, ba ta son mutane.
Abubuwan da wasu daga samarin gidan suke yi mata ne, ya sanya ta sake tsorata da lamarin mutane, ta fara ganin tamkar ita ta ta duniyar daban take, dan idris ne kawai yake amfani da ita wurin biyan buƙatar sa ba.
Mariya bata taɓa fuskanta ba, wasu lokutan har tsoron nuna wa ummi kulawa take yi, a gaban iya, saboda yanzu zata hau masifa da faɗa, wai tana nuna wa ƴar fari soyayya saboda ba ta da kunya. Ko yaya ummi ta ɗan sake a cikin yara, sai su fara cin zalinta, ko su din ga jan dogon gashin ta, ko jan kumatunta da suke tamkar doughnut ya ji yeast, ko yi mata dariya da ihun baƙar tukunya mai ƙyalli.
Takurar yara ya takureta a gida, a gidan ma iya sashinsu, shi ma fitowa tsakar gida idan ba tare da mamanta ba, ba ta fitowa saboda hantarar da kyarar da iya take yi mata.
Haka rayuwar gidansu ummi ta cigaba da garawa, iya kullum tana cikin haba-haba da Æ´aÆ´a da jikokinta, masu kawo mata abun duniya.
Yayin da ta tattara cin kashinta, a kan balarabe da iyalin sa, tamkar ba ita ta haife shi ba.
Ummi ta ɗan ƙara tasawa, kusan kullum sai ta tambayi babanta, yaushe za a kaita makaranta.
Ganin ta ɗan tasa, kuma idan tana tare da mahaifinta, ko mahaifiyarta, ta kan yi hira da su. Sai dai da tayi yinƙurin gaya musu, abun da su Idris ke yi mata, sai ta kasa ta tsorata idan ta tuna suna cewa za su yankata.
Babanta yana bata lokacin sa, yayi wasanni da ita, har da Æ´ar tsere a tsakar gida. Da iya ta ganshi kuwa ranar ya shiga uku, da masifa da gori.
Kasancewar garin sun É—an samu cigaba da wayewa, yanzu ana yin karatu sosai, akwai makarantu, ya sanya balarabe ya kai Ummi makarantar gwamnati, aka saka ta a ECC.
Ta din ga murna ganin an saka mata sabon uniform, fari da kore, ga jakarta baba na gode, an saya mata sababbin litattafai, sai washe fararen haƙoranta take yi cike da yarinta.
Tun sha ɗaya da rabi, mariya ta cewa iya zata je ɗaukar ummi a makaranta, iya ta ce "Mariya wai meyasa ba ki da ta ido ne? Ni zan ƙarasa girkin kenan, ki bari ta biyo yara, ko idan su Auwwalu sun dawo sa ɗaukkota. Ni kaita makarantar ma, Allah ya sa ba asarar kuɗi ba ne ba, kar aje yadda fuskarta take haka ƙwaƙwalwar take, ayi biyu babu".
Wani abu mai ɗaci ummi ta haɗiye, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ta faki idon iya, ta ɗau mayafi ta fice ɗaukko ummi, duk da babu tazara sosai, amma yarinya ce ƙarama, ba ta san hanya ba.
Sai dai da ta je É—aukar ta, ba ta ganta tana wannan murnar kamar lokacin da za a kaita makarantar ba.
Tayi zaton kawai ta gaji ne, dan da yawa yara na É—okin makaranta, sai an kai su kuma, su ga ba abun da suke so ba, su ce ba sa so daga baya.
Mariya tana cire mata uniform ta ce "Mamana, me aka koya miki a makarantar yau?"
Cike da yarinta ta ce "Lemo aka zana mana"
Tayi murmushi ta ce "sai kuma me?".
"Bana son makaranta, ba zan sake zuwa ba?"
"Subhanallah, ummina meyasa?" Ta yi maganar cikin kulawa.
"Yala cu na ce mini baka" (Yara suna ce mini baƙa)
Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kar ki kula su Yarinyar kirki, ki din ga mayar da hankali a kan abun da malama take koya muku"
"Ni bana son ana cewa baka"