← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 134

Sashe 62

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Au tambayata ma ka ke yi? kamar ba yanzu ka gama hantarata ba, daga gaya maka gaskiya, dama ina cikin wata damuwar ka ƙara mini wata" tayi maganar a shagwaɓe tana kai hannunta fuskarta, ya zata da wasa take yi, kawai ya ga ta fara zubar da hawaye.

Da sauri ya ƙarasa gaban ta, ya kai hannu zai sauke mata hannunta yana faɗin "Am sorry please, let me explain..

Ta ja da baya ta ce "Kar ka sake taɓa ni, ni tafiya zan yi"

"To shikenan, na yi kuskure amma dan Allah ki yi haƙuri".

Ummi ta sauke hannunta ta ce "Na ji, amma ka mayar da ni"

Raihan ya ce "Dan Allah ki zauna ummi, mu yi magana ki yi haƙuri Please "

Yadda yake ta marairaicewa ne ya sanya ta ga idan ta cigaba da yi masa musu, ba ta kyauta ba, dan haka ta zauna, shima ya ja kujera ya zauna.

Ya kalleta ya ce "Am sorry ummi, this is the raihan you don't know, ina da haƙuri amma idan aka ƙure ni bani da kyau, mutum ne ni mai zafin zuciya da fushi, amma da wuri nake sauka.

Yaya Sagir da Salim, su ne manya, kuma mahaifinmu yayi iya ƙoƙarin sa a kan inganta rayuwarmu, sai dai sun ƙi makaranta, sun ƙi sana'a kullum sai ɓarnar kuɗi a kan mata da shaye-shaye.

Ban taɓa tunanin haka mahaifinmu ke shan wahala a kan dukiyarsa ba sai yanzu, a haka ma fa aikin da ya sakani iya gida Nigeria ne, yadda yake zirga-zirga sai kin tausaya masa.

Sana'arsa ba ɗaya ba ce ba, mutum ne mai nasibi a harkar kasuwanci, muna shigo da kayan gini daga ƙasashen ƙetare, ana bamu kwangilar kayan gini, na ofisoshi, manyan ma'aikatu na gwamanti da na ƴan kasuwa, kuma muna rarraba wa kamfanoni da yawa kayanmu a Nigeria da ƙasashen maƙwabta.

Ya kunna system ɗin gabansa, ya shiga nuna mata kayayyakin da suke sayarwa, kama daga ƙofofi, furnitures, kayan banɗaki, da sauran kayan alfarma na ƙawata gini.

"Ɓangare guda, mahaifinmu babban dealer ne na shige da ficen kayan masarufi, sai dai an fi saninsa da harkar kayan gine-gine, iya kano muna da shaguna sun kai goma sha biyu a wurare daban daban ban da sauran garuruwa. Mahaifinmu duk shi yake kula da ayyukan kasuwancin sa, sai ma'aikatansa wasu lokutan a cuce shi a karkatar da kuɗaɗen sa, babu mai taimakonsa a cikinmu sai dai ya nemo mu kashe.

Wannan shi ne babban ofishinmu na ƙasa, duk da ya ce zai mayar da shi Abuja, duk da haka mukan tafka asara wasu lokutan, amma hakan ba ya sanya mahaifinmu shiga hakkin ma'aikatansa, idan an samu riba da yawa kuma, ya kan ƙara musu domin farincikin su da mu baki ɗaya, to kuma duk da wannan abun sai azo da son zuciya mu ƴaƴa cikinsa mu din ga cutarsa duk ƙoƙarin da yake yi mana?"

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Raihan, na ji duk abubuwan da ka faÉ—a, ka na da gaskiya, amma still ka yi kuskure, ba dan Allah ya fi sonka ya sanya ka zama shiryayye ba har Alhaji yake janka cikin al'amuransa ba.

Yayyenka na buƙatar kulawarka da tausayawa, a wannan halin suna sama da kai, amma ace sai ka yarje musu yin wani abu, ka yi tunanin yaya za su ji? Ka na da gaskiya, amma kamata yayi ace ka yi ƙoƙarin dannewa kun rabu lafiya, abun da ka yi masa bai kyautu ba gaba ɗaya.

Raihan komai lokaci ne, ina sake jaddada maka, ranar da ba sa doron duniya sai ka din ga ina ma ace, ni ba gani ba, sha'awa ku ke bani, mahaifina ya rasu, mahaifiyata ban san in da take ba, bani da wa, ba ni da ƙani, haka nan kawai dai rayuwa nake yi. Duk da ka ce yayyenka basa ji, but they are blessing to you idan ka kallesu ƴan uwanka ne, ban ce ka ƙyale su su yi abun da bai kamata ba, amma gaba suke da kai, su yakamata ace a wannan position ɗin, amma Allah ya ƙaddara kai ne ba su ba, haba Raihan, why are you kind to me, amma brother's ɗin ka ka yi musu haka?"

Gaba ɗaya jikin raihan yayi sanyi ya ce "Haka ne, na yi kuskure kuma na fahimce ki, in sha Allah zan kiyaye gaba ba zan sake ba, raina ne ya ɓaci sosai, kuma na yi ƙoƙarin dannewa amma yayi pressing ɗin na"

"Yauwwa dan Allah ka daina, ba ka ' sanin muhimmancin wasu abubuwan a rayuwa, sai ranar da ka rasa su, wani rashin idan ka yi sai ya tafi ya barka da rauni mai raɗaɗin da har ka koma ga Allah ba zai goge ba, kamar dai ni da na rasa babban masoyina babana, da barinsa duniya ya yi wa rayuwata giɓi" tayi maganar hawaye na kwararowa daga idonta, har jijiyar goshinta ta tashi.

Raihan ya matsa kusa da ita ya ce "Ummi, dan Allah ki daina koke-koken nan haka, Addu'a ita ce abun da mahaifinki ya fi buƙatar mu yi masa".

Ta jinjina masa kai tana share hawayen ta, ya ce "Ga lemo na sayo mana, na san is hardly idan kin karya, yau ba ki zo mana da abinci ba"

"Na ƙoshi, ba zan iya cin komai ba"

Cikin damuwa raihan ya ce "Ni gaya mini menene ya saka ki kuka ma tun farko, kin ce zaki gaya mini"

Ta É—an yi shiru sannan ta ce "A bar wannan zancen kawai"

"Ba za a bar shi ba, sai mun yi shi, ai alƙawari ki ka yi mini"

"Ai ba zaka gane ba".

Raihan ya ce "Zan gane, ko ta ina ne yi mini bayani, ina cin maths a aji ai" yayi maganar yana É—an murmushi.

Ta ɗan tsura masa ido, har cikin zuciyarta take jin yardar da ta yi wa raihan, ba ƙarama ba ce ba, saboda sosai take jin sa a ranta, mutumin da yake ta ƙoƙarin fuskantar matsalolin ta.

"Ina ƙarama mahaifina ya rasu, kakata ta karɓi riƙona daga hannun babata, nikaɗai kuma suka haifa, mama ta koma garinsu, ƴan uwanta suka yi ta zuwa a basu ni, amma kakata ta hanasu ni, aka ce mamana ta haihu ɗan babu rai, ga damuwar rabamu, ta samu larurar ƙwaƙwalwa, amma aka hana su ni, har ƴan uwan mama suka yi fushi, basu sake zuwa sun ce a basu ni ba.
Abubuwa suka ɗan faffaru, har kawu yahaya, ya ɗaukkoni daga gagarawa ya dawo da ni nan, tun da ya kawo ni, ake ta samun issues da family ɗin sa, Allah dai yayi sai na zauna a gidan, yanzu ma dai wata rigimar ce ta taso, matar kawuna ta ce zan bar gidan na koma ƙauye, ni kuma bana son komawa garin nan wallahi, mamana nake son gani, wallahi ko ba ta warke ba ko bola take bi, zan bita bolar mu rayu tare da dai in koma wannan garin da ko sunansa bana son ji, Raihan aƙalla na kai shekaru goma sha takwas rabona da mama, kuma ban ji labarin ta rasu ba, kowa yaƙi gaya mini sunan garinsu abun da na sani kawai a Maiduguri take.
Ba wanda yake kulani, duk wanda na raɓa sai ya tsangwameni, an ce mini mummuna, an ce mini mayya, an aibata ni, to wai ya zan yi nema? zuciyata ta kusa fara ciwo, ban ma san ina na dosa a rayuwata ba, tun a kan cinyar mama nake ganin bala'i da tashin hankali, raihan tafiya kawai nake yi amma na san zuciyata na ciwo, ƙwaƙwalwa ta kuma kamar  na haukace nima, abubuwa suna damuna, ba wanda yake zama na gaya masa ya zan yi?" Wata irin karkarwa ummi take yi, tana magana ba comma babu full stop, wani ɓoyayyen abu ne da yake cin zuciyarta da ba ta taɓa zama ta faɗe shi ba, once in her life, yau ta samu chance.

Babu tsammani ta durƙushe a ƙasa daga kan kujerar, tana kuka mai sautin gaske.

Raihan bai san lokacin da ya durƙusa, duk da dauriya da dakiya irin ta raihan, yau da aka zo gaɓar da yake jira a zo, ya ji wacece ummi, ya ji sai dai zuciyarsa ta gaza ɗauka, zuciyarsa ta karye, ashe da ba tausayinta yake ji ba, kallonta kawai yake yi bai san meye a ƙunshe a zuciyarta ba, a hakan ma ba wai buɗa masa rayuwar ta tayi ba.

Shekara sha takwas, ba ta sanya mahaifiyarta a idonta ba, alhalin duk suna raye, bama ta san in da take ba.

Ya sanya hannun sa cikin tattausan hannunta, yana murzawa a hankali amma ya kasa magana, sai saurara sautin kukanta, da yake ƙara bugun zuciyarsa.

Danƙe hannunsa tayi sosai a cikin nata, tana ƙara pressure kukanta.

"Is ok salma, ya isa haka" ta girgiza masa kai ta ce "Allow me, idan na yi kuka ina jin sauƙi".

Ya É—ora hannunsa É—aya a kafaÉ—arta, amma ya kasa magana.

Ganin kukan nata ba mai ƙarewa bane, ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen da suke ta kwarara ya ɗan tura baki ya ce "Nima kin sani kuka, ya isa haka please" yayi maganar yana cigaba da goge mata hawayen.

Kallon raihan take yi, da girmanta ko Abdul bai taɓa kai hannu jikinta haka ba, tana da taka tsantsan da kanta, wa ma ya damu da ita balle yayi yinƙurin kai hannunsa jikinta? Amma rarrashin nan da Raihan yake yi mata, ji take yi kamar ɗan uwanta da suke ciki ɗaya ne yake yi mata.

"Waye ya ce ke mummuna ce?"

Ta É—an ja numfashi ta ce "Mutane" tayi maganar cikin tura baki

Hannunsa a kan fuskarta, yana goge mata hawayen ya ce "Kuma kin yarda?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.
Chapter 62 · 0% Book details