Sashe 36
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kar ki damu, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana ummana"
Murmushi ummi tayi, tana so ta ji ya kirata da ummana ko ummina, hakan yana yi mata daÉ—i, kuma yana tuna mata da maman da babanta.
Ya ce "Au, na manta ban gaya miki ba, mun kusa komawa sabon gida fa, bamu taɓa zuwa kin gani ba ko"
Ta faÉ—aÉ—a murmushin ta ta ce "Allah ya nuna mana, wannan wa za a barwa, na ga shima mai kyau ne"
"To ko in bar miki, tun da kin fi son nan?"
Murmushi ta yi ta ce "Ai ni macece ba zan iya zama a gida nikaÉ—ai ba, amma ina son gidan nan"
"Can yafi kyau ai, idan muka koma zaki gani"
"To Allah ya sanya albarka, to nan su iya ne za su dawo su zauna?"
Sai da ya ƙara kallonta da sauri, ya ce "Su iya kuma?"
Ta ce "Eh, su baro ƙauye su shiga makarantar islamiyya, makarantar mu har da matan aure da tsofaffi suna zuwa asabar da lahadi"
Bakomai a ranta ta faÉ—i hakan, kawu yahaya yayi murmushi saboda magana tayi cikin magana mai ma'ana, ba zaka san ummi na magana ba, sai ka zauna da ita, a haka kamar ba ta magana.
Sai kuma ta sake cewa "Kawu, kaga da ka san in da mama take ita ma zaka É—aukkota ka dawo da ita nan? Sai mu zauna ni da ita a gidan nan sai ku koma sabon gida"
Tausayin ummi ya kama shi, ya ce "Ki na kewarta ko?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"In sha Allah zan nemo in da take, zan haÉ—a ki da ita, sai dai ba zan so na kawo ta nan ita ma ta din ga shan wahala kamar yadda ki ke sha ba"
"To ai ba zan bari ta sha wahala ba, ni zan din ga yin duk wani aiki, idan na iya sana'a na din ga saya mata abubuwa, idan ka gano ta dan Allah kar ka kai ta wurin Iya, Iya ta ce ba ta son ta, wai mama mayya ce..."
"Ummi ya isa haka, ki daina tuna abubuwan da suka shuɗe wanda za su dinga ɓata miki rai, ki yi karatu sosai yadda maman idan ta gan ki za ta yi alfahari da ke"
Ta gyaɗa masa kai ta ce "In sha Allah" kai da ganin yadda ta ɗan kwaɓe fuska, ka san akwai tarin abubuwa cunkushe a zuciyarta da take burin amayar da su, sai dai babu wanda zai tsaya ya saurareta, to wa ma ya damu da ya zauna da ita balle aji matsalarta.
Cikin son kawar mata da wancan tunanin, ya yi murmushi ya ce "Ki na buƙatar wani abu ne ummana?"
"A'a bana son komai"
Ya ajiye mata ɗari bibbiyu guda biyar, ya ce "Gashi idan kina buƙatar wani abun ki yi amfani da shi".
Kallon kuÉ—in ummi take yi dan da yawa a wurinta, kan tayi magana ya tashi ya fita, zuciyarsa na yi masa zafi.
ÆŠakin farida ya wuce kai tsaye, ya tarar da ita tana saka kaya a gaban mudubi, ta É—ago ta kalleshi ta ce "Ya dai?"
A take ya nemi karsashinsa da zafin zuciyar da ya zo da ita ya rasa, duk yadda ya so yi mata magana a kan ummi, sai ya kasa kawai ya tsaya yana kallonta.
"Kana buƙatar wani abu ne?" Kawai ya girgiza mata kai ya juya ya fice, yana jin baƙin cikin kasa yi mata magana a kan cin zarafin da ta yi wa ummi.
Duk da ƙonuwar cikin ummi, haka ta cigaba da yin aikace-aikacen gidan, kuma muddin ta fito ƴan uwan farida suka ganta, sai sun ci zalinta, ko sun aibata ta.
Hatta makarantar boko, kawu ya hanata zuwa, ya ce sai ta samu sauƙi tukuna.
Dan haka, a hakan take naɗe rigar ta, ta bar wurin ƙunar a waje tana shan iska, tana aikinta.
Abdul ne kawai yake tausaya mata yake yi mata sannu, dan shi har ga Allah yake jin matuƙar tausayinta.
Mopping kuwa a rana a gidan nan, sai tayi sama da sau sha biyar, wanke-wanke kamar gidan da ake rabon sadaka, banda ɗorawa da saukewa da kula da yaran baƙi, tana yi ana zaginta.
Wani lokacin haka zata fama ƙunar tayi ta kuka.
Kawu yahaya ya din ga kai ta dressing, Allah ya taimake ta ƙuna ta fara warkewa. Tana matuƙar son ta ɗauki jaririyar da antyn ta haifa, sai dai an ƙi bata damar hakan, daga nesa take hangen ƴar, zuciyarta har raya mata take ta ce a bata ta ɗauketa, amma da ta tuna hakan na iya haifar mata da cin mutunci, sai ta haƙura.
Farida ta je ta tarar da mijinta a bedroom É—in sa, yana ta aikin takardu.
Ta zauna tana cika tana batsewa ta ce "Dr. Wurinka na zo"
Ba tare da ya É—ago ba ya ce "Ina jin ki"
Ta ɗan taɓe baki ta ce "Jibi in Allah ya kaimu ne fa suna, haryanzu baka ce mini komai ba, baka bayar da kuɗin hidimar suna ba, kuma wuri nake so a kama ka sani, amma ka ƙi magana".
"A wannan karon babu suna, sauran ukun da aka yi Allah ya amfana, idan Allah ya kawo wata a gaba ayi".
A fusace ta ce "Ban fahimta ba?"
"To ki jira daga lokacin da ki ka fahimta, sai ki tashi ki bani wuri"
Ta miƙe tsaye ta ce "Yahaya ni zaka wulaƙant, na gama gaya wa mutane da taron suna ka ce ba za ayi ba"
"Hakika kawai zan yi, za a kawo raguna biyu manya, ayi hakika na sanyawa yarinya mariya, sai ki koma ki gaya wa mutanen babu suna"
"Mariya kuma? Wace irin mariya ana zaune ƙalau, sunan uwar waye mariyar da zaka sanya wa ƴa ta, haka muka yi da kai? To ba gara Salman da na ce bana so ba, a kan wata mariya, kamar dattijuwa"
Ya É—aga kai ya kalleta ya ce "To ki koma ki bibiyi tarihin fiyayyen halitta, zaki gane suna ne mai daraja da ma'ana".
Aikuwa ta hau ta din ga surfa bala'i, duk yadda ya yi ƙoƙarin sanar masa da cewa, hukuncin zaluncin da ta yi wa ummi ne, ya sanya ya hukunta da haka ya kasa, saboda tuni ta kai sunansa wurin malamai, a kan ko ya mayar da ummi, ko kuma duk izayar da zata yi mata ba zai iya magana ba, yarinyar ta gaji ta bar gidan.
Tun a haihuwar inteesar, ya so saka mata sunan mahaifiyarsa Salma, farida ta ce ba ta san zancen ba, ba ta so, aka saka sunan ta ta uwar, haihuwar khausar ma, ta ce sunan yayarta da ta rasu za a saka, wannan ma suna ta kai ruwa rana a kan ita gaskiya ya bari sai wani lokacin a saka Salman, tun da sanyan wa Æ´aÆ´a sunan iyaye ba wajibi bane ba, wai Jidda za a sakawa yarinyar, tana son sunan.
Shi kuma ya sanyawa yarinyar mariya, sunan mahaifiyar ummi, wanda ita Farida sam hankalinta bai kai kan cewa sunan babar ummi bane ba.
Ya fice daga ɗakin ya bar ta tana ta sababi da kumfar baki, ya zo falo ya tarar da ƴan uwan farida na ta cin abinci da lemuka da nama zuƙu-zuƙu.
Ga ummi da ɗagaggiyar riga, tana ta mopping, tare da haɗa kwanukan da suka ɓata, sai ta kwashe zata tafi, sai a kirata a jefa mata wani kwanon.
Gyaran muryar da yayi ne ya sanya duk suka juya, mai neman gyale nayi su rufe jikinsu, masu gyara zama na yi.
"Yauwwa, ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala, da kyautar haihuwar mace da ya bani, ina kuma godiya a gareku wurin tsayawa tsayin daka, wurin kula da Æ´ar uwakku, duk da hakkina ne. Ina godiya sosai, dan Allah idan kun gama cin abincin, zaku iya tafiya gida, rahama zata iya cigaba da kula da ita. Ba za a yi taron suna ba, ga yanayin rayuwa, gara a tattala kuÉ—in tayi jego mai kyau, kuna iya tafiya idan kun gama kan magariba dan Allah, sunan jaririya mariya, za a dinga kiranta da noor"
Gaba ɗaya turus suka yi suna kallonsa, tun da suke zuwa gidan, su yi duk hauka da rashin hankalin da suke so, bai taɓa yi musu magana ba, sai yau, dan maganar tasa ta wani fannin kamar cin fuska.
Ummi kuwa washe baki tayi, jin an sakawa jaririyar mariya, duk da ba ta san dan sunan mahaifiyarta ya saka sunan ba, amma wani irin daÉ—i da farinciki ya ratsa ta.
A hankali ta ce "Allah ya raya noor takwarar mama"
Daga in da yake ya hango farinciki a kan fuskar ummi, yayi murmushi ya fice, yana tawasalli da farincikin da ya sanyata yana neman biyan buƙatunsa a wurin Allah.
Farida ta sha kuka, da yin alwashi kala-kala a kan yahaya, saboda yadda ya wulaƙanta ta, ya tozarta ta a gaban ƴan uwanta.
Suka din ga rarrashinta, tare da bata shawarwari daban-daban.
Babbar yayarsu ta xe "Duk sakacinki ne, waye ya gaya miki ana barin namiji haka, kyakywar mallaka zaki nema, ta mai da É—an gida bawa, ki juya shi yadda yake so, kar ki yi bori da yawa, ki girgiÉ—e auren, duk cikinmu babu wanda yake cikin rufin asiri da kwanciyar hankali kamar ke, kar ki yi mana sagegeduwa, amma dole mu zage damtse".
Suka din ga zigata, ƙarshe kan sallar magariba suka watse daga gidan sai rahma, rahama kuma ba wani abun kirki take yi mata ba, saboda shegen son jiki ne da ita.
Bayan watsewar ƴan gidansu, ta ƙuduri aniyar ƙuntatawa dr. Ta hanyar nuna halin ko in kula ga yarinyar, gashi mutum ne mai mugun son yara, baya son ya ga ƙaramin yaro cikin damuwa.
Yarinyar shegen kuka ne da ita, ba ta taɓa ɗa mai kukanta ba, idan tana kukan sai ta yi banza da ita. Yayi ta maganar ta kula da ita amma ta share shi.
Ranar da aka yanka hakika kuwa, ummi ce ta zage ƙwanji, tsaf ta gyara hanjin nan, dan kuwa rahama ƙin fitowa tayi kan naman, ga rana na dukan kayan kitchen.
Abdul ne ma ya kama mata wasu abubuwan, ta kunna murhu ta É—ora sai ka ce babbar mace.