Sashe 66
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu kamar wasa, aka yi ta shirin yi wa raihan liyafa, ya so ummi ta je, amma ta ce ba zata ba.
Abokan hulÉ—ar Alhaji Tahir wasu sun ga wautarsa, na bawa raihan jagoranci babban business irin wannan, matashi mai shekaru 23 dan ma yana da siffar kwarjini da girman jiki, amma kallo É—aya zaka yi masa ka san yaro ne.
Sai dai ko a kalamansa na godiya, da na kama aiki, sun tabattar wa da mutane ƙaraminsu babbansu ne, kamar yadda Alhaji Tahir yake faɗa, wanda wasu maganganun ummi ce ta gaya masa abun da zai ce, dan Alhaji Tahir ya sanar masa ya shirya kalaman da zai faɗa ranar liyafa.
Aka yi taro aka watse, ya turawa ummi hotunan abun da aka yi, ta ɗauki hotonsa guda ɗaya ya sha coat, ƙuruciyarsa ta fito sosai, sai dai ya tsare gida babu fara'a, ta saka shi a status da caption na "Allah ya tayaka riƙo ƙanina, MD Muhammad Raihan"
Ta kai awanni biyu da yin status ɗin, da ta buɗe what's app ta tarar da saƙonni, na tambayar waye shi, ciki har da yaya magaji, babban wanda ya fi bata mamaki shi ne message ɗin maryam, tun da raihan ya haɗa su, suka yi magana maryam ba ta sake kulata ba, idan ta yi mata magana ma, sai ta ga tana shareta, dan haka ita ma ta daina kulata, sai yanzu taga message ɗin ta, wai ya aka yi ki ka sani?.
Ummi ta yi mata reply da "Shi ya gaya mini".
Maryam ta ce "A ina ku ka haÉ—u ya gaya miki?"
"Muna gaisawa idan zai wuce ta wurin da muke aiki ne".
Ta yi reply da "Dan Allah ki cire shi, ba kowa ya sani ba, kar azo hakan ya bashi matsala" Ummi ta daÉ—e tana jujjuya message É—in, ita mutum nawa ne ma a what's app É—in nata. Ta ga ita kanta maryam É—in, ta saka hotunan sun fi goma, kodayeke wata kusan ta fi wata, dan haka ummi ta goge.
Tamkar jira yake ta goge, ya ce "Meyasa ki ka goge status É—inki?"
"Bakomai".
"Akwai dalili mana, saboda Maryam ko?".
Abun ya bata mamaki, kan ta yi magana ya sake turo wani saƙon ya ce "Muna tare take nuna wa mami status ɗin naki ai, ita take saka miki data da zata ce ki cire abu kuma ki cire? Ina ruwanta, ko haifarki tayi da zata bani umarni ki bi? Akwai mutane a wurin ne ya san na ƙyale maganar, ƙarewa gobe in Allah ya kaimu hira za ayi da ni a wani gidan jarida. Dan Allah ki daina bari ana raina mini ke bana so"
Karanta saƙon nasa ta din ga yi, tana ƙoƙarin bawa saƙon damar yin tasiri a zuciyarta, amma ta kasa.
"Dan Allah ki sake duba wani hoton, ki É—ora ni ki yi mini addu'a, tun da ba ki je taron ba Please".
"Yanzu ka gama cewa a daina sani abu in yi, ai ba kai ka saka mini data ba" ta tura masa tana dariya.
Emojin dariya ya tura mata ya ce "Ta kaina zaki fara kenan? Ni ki ka raina ko?"
"Kai ka mayar da ni haka ai, ina salihata ka koya mini surutu".
"Dama can kin iya abinki"
"To na ji, sai da safe bacci nake ji"
" ya kaimu" ya rufe data ya ajiye wayar, ya lumshe ido yana tuno moments ɗin su tare, ba zaka taɓa cewa ummi na magana ba, dama ce kawai ba ta samu ba, amma tana da baki sosai".
***
Alhaji Tahir kallon mami yake yi, bayan ta gama kora masa bayanin abun da take so.
Ta kalleshi ta ce "Wai ya ka yi shiru kana kallona ne?"
"To ai abun ne na ji shi banbarakwai, guda nawa raihan É—in nawa yake zaki ce ayi masa aure yanzu? Daga É—ora masa wannan É—awainiyar sai kuma ki ce ayi masa aure?".
"To ai shine cikar kamalarsa, ya samu matsayi ya zamana yana da iyali, dole zai nutsu ya mayar da hankalinsa, ko so ka ke na saki jiki shima ya lalace? Ni dai dan Allah ka taimaka ka amince"
Alhaji ya ce "Ai ni bani da damuwa, in dai ya amince yana so shikenan, Allah ya sanya alkhairi"
"Yauwwa, dan Allah ka tayani shawo kansa, ka san ko budurwa ba shi da ita, ko zancen na yi masa sai ya sha kunu, dan Allah ka tayani lallaɓa shi, ko da Safiyyar Anty rakiya a haɗa shi"
Ya kashingiÉ—a ya ce "Wannan ba hurumina bane, kin san takura wa É—a ba ya cikin tsarina, ku tattauna kawai"
Tayi ajiyar zuciya ta jinjina kai.
Mami ta din ga fargabar tunkarar raihan da maganar, haka nan ta dake da safe ya shiga gaisheta zai fita office, ta ɗaukko masa zancen, aikuwa ya haɗe rai, ya ce "Dan mami ki daina wannan zancen, abokaina kowa ba wanda yayi aure sai ni, kawai na tsufa da wuri, kuma matar ma ki rasa wa zaki zaɓar mini sai wannan marar kunyar, ni ba zan auri matar da ba zan iya tanƙwarata ba, yarinyar da bata da kunya, ni bana so".
"Raihan, cikar kamalar mutum iyali, ace kana da wannan matsayin baka da aure, ai sai a rainaka, kuma ganin kai baka da ko budurwa ya sanya na zaɓa maka, aure yana ƙarawa mutum kamala"
Ya ce "To mami na ji, amma dan Allah ki ƙyaleni, idan lokaci yayi zan yi miki magana zan yi auren, amma ni yanzu wallahi ban yi niyyar yin auren ba, kuma da kaina zan samo budurwa da zan aura, ummi ta ce in nutsu in samo mace ta gari".
Cikin mamaki mami ta ce "Wacece ummi kuma?"
Ya miƙe tsaye ya ce "Kar ki damu mami, ni dai ki bar wannan maganar"
"Wallahi ba zan barta ba, dole ka yi aure dan ba zan zuba ido ka lalace a banza ba, ko wata ta lallaɓa ta lalataka ba, wato ni nake yi maka kallon salihi, har mai baka shawara ce da kai a waje?".
"You should thank God, shawarar kirki take bani, ita ta saita ni a hanyar da na ci jarrabawar Alhaji" daga haka ya fice ya bar falon.
Abu kamar wasa, raihan har ba ya son shiga sashin mami, dan ta fara hura masa wuta, shi ko zancen ba ya so.
Yanzu Ummi haÉ—uwa da raihan yana bata wahala, saboda yadda aiki ya saka shi a gaba, ba shi da cikakken lokacin kansa.
Yau ya kirata a waya ya ce mata zasu fita, zai zo ya É—au excuse a wurin manager.
Da azahar ya zo ya sameta, lokacin ta gama aiki, tana ta tsokanarsa MD, yayi mata shiru yana hararta.
Ta bashi wayarta ta ce "Raihan, dan Allah ka buÉ—e mini Instagram"
"Me zaki yi da shi?"
Ta ce "Kallon abubuwa zan din ga yi"
"Wai wannan wayar taki, da ke da ita waye ya girmi wani? kalli yadda ta ci ƙaniyarta"
"To sai ka bani taka ai" tayi maganar tana hararsa.
Ya ce "Kin samu, ciro mini layukana ki É—auka"
"Ni da wasa nake yi, ka buÉ—e mini dan Allah na kasa buÉ—ewa".
Raihan ya ce "Ke Instagram ba zai hau wannan dattijuwar wayar taki ba, ai na ce ki É—au tawa, ba abun da zaki ce na baki na hanaki"
"Da wasa nake yi maka, ka buɗe mini" tayi maganar tana miƙa masa wayar tana ɓata fuska kamar ƴar yaye.
"Da gaske na bar miki wayata ummi, kawo wayar taki mu yi exchange na layukan".
"So kake ace na fara sata ko? Me nake sayarwa da zan mallaki wannan wayar?"
Ya ce "Sai ki ce ke ƙawar MD ce"
"A'a nice ma MDn, tun da ba zaka buɗe mini ba shikenan" ya karɓi wayar ta ta yana dubawa, ya ce.
"Tashi muje mu dawo da wuri"
"Ina zamu je?"
"Budurwata zan sai wa wasu kaya, mu je ki tayani saya, za ta yi ki a jiki, bana son na sai mata wanda zai yi mata yawa".
Ta harare shi ta ce "Kuma saboda ka raina ni, da ni zaka gwada? Daga baka muƙami ka fara kule-kule, guda nawa ka ke da ka fara yin ƴan mata" wani irin kallo yayi mata, tayi shiru, ta zata maganar da tayi ne, ta ɓata masa rai.
Shi kuwa hoton da ya gani ne ya bashi mamaki, hotonta da noor, gashin kanta kamar aljana.
Sai dai yayi tunanin ko sakawa tayi, amma ina ummi take da wata wayewar saka gashi.
"Tashi mu je" ta tashi tabi bayansa, a ranta tana fatan Allah ya sa ba haushi ya ji ba.
Ita kanta mamakin kanta take yi, yadda take bin raihan duk in da ya ce suje, ba tare da musu ba, yanzu ta daina fargabar shiga motarsa, kodayeke zuciya na son mai kyautata mata, kuma bai taɓa yi mata wani abu na rashin ɗa'a ba.
Suna tafe a motar, ta ciro leda a jakarta ta ce "Gashi, dama ina ta jira mu haÉ—u, kuma saura ka ce baka so, sai ka je gida zaka duba"
Ya amsa mata da "To babbar yaya"
Wani ƙaton shagon sayar da kayan sawa suka je, suka shiga raihan suka gaisa da matar da ke shagon.
Ya nuna mata ummi ya ce "Yauwwa hajjaju, ban san size É—in da take sakawa ba, amma ga wata mun zo tare da ita, ki bata ta gwada, idan dai ta yi mata dai-dai, ita ma za ta yi mata.
Matar ta ce "Masha Allah, bisimillah, muje to ka zaɓa sai ta gwada".
Tarin abaya ne a wurin da suka je, kala-kala na kece raini.
Ya kalli ummi ya ce "Zaɓo ɗaya wadda za ta yi mata kyau sosai".
"To ai ban san ya take ba, ko wanda ta fi so ba, fara ce ko baƙa?"
"Ina ruwanki da kalarta? to black beauty ce"
Ta tsaya ta kalleshi ta riƙe ƙugu ta ce "Daga baka office, ka fara kashewa ƴan mata kuɗi ko? Alhaji ya sani?"
Raihan shima ya riƙe ƙugu ya ce "Yau nake ganin ikon Allah, ke ina ruwanki ne? Wai ce miki aka yi ɗan zaman banza ne ni? Ɗauki muje akwai in da zamu je".