← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 134

Sashe 71

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta jinjina mata kai, tare da jin matsananciyar faÉ—uwar gaba, dan wannan ne karon farko da zata tsaya tayi zance da wani, da sunan yana sonta, gashi alamu sun nuna da gaske yake, tunda ya biyo ta wurin dr., Duk da abun da take ta addu'a a kai kenan, idan tana da rabon aure, Allah ya kawo mata miji nagari, sai dai gaba É—aya ba ta murna da lamarin a yanzu, kuma ta rasa dalili.

Sai dai ta tsinke da al'amarin, ganin headmastern su a gareji, wai shi ya zo wurinta, kenan shi ne baƙon?

Suka gaisa suka zauna a kan fararen kujeru, tana bin sa da ido, dan ba ta gama yadda da shine baƙon ba.

Yayi gyaran murya ya ce "Wato ummi na san zaki yi mamakin ganina, da dalilin zuwana, duk da nasan mahaifinki yayi miki bayani.
To ni dai ummi ba wani abu ne ya kawo ni wurinki ba face alkhairi, na daÉ—e ina sonki, tun ranar da na ga kin cire hijjabi kina alwala, watannin baya baki ganni ba ke amma, to a lokacin gidana mata huÉ—u ne, amma yanzu Alhamdilillah mun rabu da ta ukun, dan haka akwai gurbin mutum É—aya, ya sanya na ce tun da naga alamar babu tsayayye bari ni na tsaya, mu dai-daita mu rufawa juna asiri, dan yanzu kin san maza tsada muke yi" yayi maganar yana murmushi yana kallonta.

Ummi dai sama-sama take jin sa, ƙasan zuciyarta lissafi take yi, ta yi wa raihan reply ko ta ƙyale shi, ta san duk daɗewa idan ya dawo sai ya nemeta.

Dan haka sama-sama take jin maganganun headmastern.

"Ba zan takuraki yanzu ba, amma dai ki yi tunani, dan kuwa da wuri nake son ayi auren nan, bana son ɓata lokaci, kuma za ayi abu ne dai-dai talaka da tsarin addini, ba wani ɓarnar bidi'a, in kawo abun da Allah ya yassare ayi"

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce "To malam, idan na yi tunanin sai mu yi magana"

Ya ce "Yauwwa ummi, Allah ya wuce mana gaba " ta amsa da Amin, ya tashi ya tafi, ita kuma ta dasa sabon zama tana nazari da tunani.

Sai da ta ji sauron wurin na neman halakata, sannan ta tashi ta koma cikin gida.

Kitchen ta nufa ta zubo abinci, zata fito farida ta tare ta ta ce "Ubanki ne ya kawo abincin?" Ummi ta girgiza kai.

"To ajiye ki fita, mayya mara zuciya, ai si ki je wurin waÉ—anda ki ke bi ku watse su saya miki kaya, su saya miki abincin, wallahi takura da masifa yanzu ki ka fara ganinta, sai ranar da ki ka bar mini gida, ko ki yi aure, ko ki koma in da ki ka fito ko ki bi duniya "

Salin alin ummi ta ajiye abinci, ta bar kitchen É—in.

'Tabbas! Tura ta kai bango, yakamata na yi wani abu na matsa daga gidan nan, na fuskanci ƙalubalen da ke gaba, zaman gidan nan yana neman fin ƙarfina" tayi maganar a zuciyarta.

Abokin kukan nata ga ƙoƙarin da take yi a kansa, ta nesanta kanta da shi.

Abubuwa suka cigaba da É—aukar zafi, dan da kawu zai koma aiki, sai da ya gindawa farida sharaÉ—i, a kan muddin ya dawo ya tarar ummi ba ta nan, sai ya saketa.

Farida har mamaki take yi, yanzu asirin ya daina kama dr. Al'amari in dai ya shafi ummi, ba ya saurarawa.

Ummi ta din ga sallar dare tana kai wa Allah kukanta, amma a ƙasan zuciyarta ta ji ta amince da auren headmaster, no matter what wahala ba yanzu ta fara shigar ta ba, tarwatsewar gidan dr., Da kuma alƙarsu da raihan su ne manyan barazanar ta a yanzu, idan ta yi aure ta san ta rage kaso mafi yawa daga matsalolinta.

Raihan ya sha mamakin burus da ummi ta yi da shi, ba dan ba ta ganin saƙonninsa ba.

Gajeren saƙo ta tura masa "Baka yi mini komai ba raihan, tarayyarmu na barazana ga kwanciyar hankalina, da jefa zargi a zuciyar mariƙana, ka yi haƙuri da hukuncin da na yanke"

Message ɗin ya nuna blue tick, alamar ya ga saƙon amma yaƙi reply, tun ummi na jiran yayi reply, har ta sare, sai kuma abun ya dame ta ta rasa sukuni, ga headmaster ya matsa mata kamar maye, ita har mamaki take yi, duk lokacin da suka shafe, bai ji yana son ta ba, sai watannin baya da ya ganta tana alwala, mata huɗu sun rabu da ɗaya zai aureta, kodayeke wannan duk bai dameta ba, wutar gabanta take ƙoƙarin kashewa, dan haka ta ce masa ta amince.

Tamkar ya goya ummi, saboda murna da nishaÉ—i, ta amince da aurensa, ya ce mata zai zo wurin kawu su yi maganar kawo kuÉ—in aure, ta ce masa baya nan sai ya dawo.

Ya fara yi wa ummi huÉ—ubar shi talaka ne, dan haka kuÉ—in sadaki, da na lefe da na aure, zai bayar dubu É—ari, dan Allah ta ce ta yarda a haka, ko da babanta zai ce ba yadda ba.

Ummi ta amsa masa da to, dan ba ta da burin da ya wuce ta ɗaga daga gidan nan, ita ma tana burin ta ganta a ɗakinta, ko ta samu sauƙin gorin da take sha.

Kullum cikin duba wayarta take, taga raihan yayi mata reply na message ɗin da tayi masa, amma yaƙi yin reply, wasu lokutan tana kallon sa online, amma bai yi responding ba.

Tunani ta din ga yi hanyar da ta bi tana neman maraba da raihan tayi musu tsauri daga ita har shi, amma ta san idan tayi masa bayani, ba zai taɓa tsayawa ya fuskanceta ba, dan akwai shi da kafiya wasu lokutan.

Noor tana ta gyara wa ummi kan mudubin ta, tana jera mata mayukanta tana faɗin "Ai yaya ummi ba sai kin cigaba da ɓoyewa ba, kawai ki jera abun ki, dama na san dr. Ba zai yi miki faɗa ba" ta lura hankalin ummi baya kanta, dan haka ta ce "Wai yaya ummi me ki ke jira a wayar ne, ko salary ki ke jira ne?"

"Noor raihan ya daina kulani"

Noor ta É—an waro ido ta ce "FaÉ—a ku ka yi? Innalillahi yaya raihan É—in namu?"

Ummi ta ce "Ni na fara daina kula shi, noor bana son zargi ya shiga ran kawu a kaina ne, kuma aure nake son yi, bana son na yi aure mu kasa rabuwa".

"To yaushe zaki auren?"

"Malam ya ce idan kawu ya dawo zai zo su yi magana ya kawo kuÉ—in aure, sonake ya kawo kan raihan ya dawo"

Noor ta kwaɓe bakk ta ce "Wai wani malam, ni fa bana son malam ɗin nan, Astagfirullah bari dai na yi shiru, amma dan Allah kar ki auri wani malam, ki auri raihan mana" ummi ta zare ido ta ce "Ke ƙanina ne fa, kamar ɗan uwa yake a wurina, malam ya ce zai bayar da dubu ɗari kuɗin komai da komai, kar a wuce wata uku, amma ban san yadda za su yi da kawu ba".

Kamar shashasha noor ta kalli ummi ta ce "Wai ke yaya ummi, ni na rasa me zance, shikenan ke ba za a kawo miki lefe ba? Matansa fa uku, gashi tsoho, to kina son sa ne?"

"Mama ƙyaleni, surutun nan naki ma ya fara damuna".

"Hmm, Yaya raihan yayi fushi da ke fa, har makarantarmu ya je, bayan mun dawo daga gagarawa, ya tambayeni idan tare muka dawo kuma lafiyarki ƙalau, na ce masa eh. Ya jinjina kai ya tafi"

Cikin tsananin mamaki ta ce "Ya aka yi ya san makarantar ku har ya je? Sau biyu fa kawai kuka taɓa haɗuwa, Kin ga dalilin da yasa nake son mu rabu, raihan ya iya rigima fa"

Noor ta ce "Eh amma yana da kirki sosai ai, tun da ya taɓa bani kuɗi, wannan malam ɗin gaskiya talaka ne, ko kuma wayo, dubu ɗari fa ba ta da yawa sosai, shikenan ke ba za a kawo miki akwatuna masu yawa ba, kamar na inteesar"

Ummi kawai ta kwana ta yi wa noor shiru.
Ta cigaba da kallon wayar, a ranta ta ce 'Haba babban mutum, manyan ba sa haka fa' ta cigaba da duba chats É—in su na baya.

Headmaster ya kira dr. A waya, yana tambayarsa yaushe zai dawo, so yake da ya dawo, ya kawo kuÉ—in, dr. Ya ce masa baya son gaggawa ya jira shi tukuna.

Wasa-wasa kusan sati uku kenan, raihan da ummi ba su yi magana ba, ba kuma dan hakan yana yi wa kowanensu daÉ—i ba.

Ummi ta kira direban da yake aikowa ya karɓar masa abinci, ta tambaye shi ko raihan ya dawo, ya ce mata a'a.

Yanayin sintiri da nacin da headmaster yake yi mata, abun har mamaki yake bata, kamar ya É—auketa ya kaita gidansa ya ajiye.

In da Allah ya rufawa ummi asiri, aikin nan nata, tana É—an samun salary, idan tayi girki ta gama farida sai ta hanata abinci, tayi ta janyo mata masifa da bala'i da miyagun alkaba'i, tare da fatan ta sha wahala a rayuwa kamar yadda ta wahalar da ita a gidan aurenta.

Ummi a ranta ta ce 'Wahala waccece ban sha ta ba, kuma ban cutar da ke ba a zamanmu ke ki ka cutar da ni!"

Tun da dr. Ya zo gida, headmaster yake sintiri, a kan zai kawo kuÉ—in, dr. Ya ce ya É—an ba shi lokaci tukuna.

Hatta wurin aiki manager ya lura yanayin ummi ya sauya, kamar wani abu na damunta, amma dai yayi shiru bai ce mata komai ba.

Dr. Ya kira ummi ya tambayeta ko tana son malam Isa, ummi ta ce eh.

"Ummi, kar takura ko damuwa ta sanya ki kai kanki ga halaka, rauwar aure ba rayuwar gida ba ce da babu nauyin kowa a kanki, kar ki kai kanki in da zaki yi dana sani, mutumin nan babban mutum ne, kar ki zo daga baya azo a samu matsala, ki dai je ki sake tunani" ummi ta amsa masa da to, ba dan ta so ba, ita fatanta kawai dr. Ya amince.
Chapter 71 · 0% Book details