← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 134

Sashe 122

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka ta gane yana shan sigari, tayi ta masa mita, ya ce idan ya nemo mata ummi, zai daina sha.

Haka nan yake jin daÉ—in mu'amalarsa da Æ´ar yarinyar da da yayi auren wurin zai haifeta.

CIGABAN LABARI.

Hajiya sun daɗe tare da ummi, kuma ummi ta samu ta ci abincin da hajiya ta kawo mata sosai ta ƙoshi, kuma Allah ya taimaketa ba ta yi amansa ba.

Bayan tafiyar Hajiya, Dr. Ya kira ummi a waya, bayan sun gaisa ya ce "Noor tana gidanki ko?"

Ta ce "Eh kawu"

"Na san ta riga ta gaya miki komai ma,  bayan mun zo gidanki mun yi wannan maganar, na yanke shawarar yin abun cikin gaggawa, saboda kar wani abun ya kutso ya hana.

Na kira baban maiduguri, muka yi magana da shi, da na tabattar da ya amince, kawai da muka je jiya, na tafi da sadaki aka ɗaura, dan hatta ƴan gagarawa ba su sani ba, sai da aka ɗaura na san za a iya samun matsala ko daga gare su ko wani ɓangaren.
Nan da sati É—aya idan komai na ta ya zama ready, zan É—aukkota ta yi miki kwana É—aya ko biyu sai mu wuce".

Ummi bakinta ya kasa rufuwa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya cigaba da faranta maka kamar yadda ka ke yi mana kawu, Allah ya saka da alkhairi na gode sosai da sosai"

Dr. Ya ce "Ba komai ummi, yi wa kai ne".

Can Maiduguri kuwa, mariya na zaune ta yi shiru tayi zurfi a tunani, mama ta ce "Mariya, wai menene? Ko abincinki fa baki taɓa ba"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Wallahi mama tunani nake kawai"

"Tunanin me?"

"Auren nan mana, ni fa banda baba ya matsa ba zan yi wani aure ba, ido ya mutu kwalli ba zai farfaÉ—o da shi ba, kuma idan ina tuna wahalar da na sha a hannun iya, ko a mafarki bana fatan sake yin aure"

"Ashsha, mariya ba a fitar da rai da rahamar Ubangiji, kuma ke ba tsohuwa ba, haryanzu da sauranki, babu wanda zai ce kin haifi ummi, gashi albarkaci auren har jirgi zaki hau" ta ƙarasa maganar cikin zolaya.

Mariya dai ta rausayar da kai ta ce "Wallahi mama ba na ƙaunar abun da zai sake haɗa ni da iya, auren nan ya sake mayar da ni jikin su"

Mama ta girgiza mata kai ta ce "Akwai banbanci, tsakanin Bashir da Yahaya, Kuma ai ba wuri ɗaya zaku zauna ba" mama tayi ta lallaɓata tana kwantar mata da hankali.

Can gidan dr. Kuwa Farida kamar za ta kama dr. Ta daka, saboda azabar kishi da bala'i, sai dai fafur ya mayar da ita kamar mahaukaciya ya ƙi saurarenta.

Yanzu da safe Abdul ya kawo kai zai shigo falo, ya ji yo muryarta tana ta ɓaɓatu, tare da amfani da kausasan malamai wurin ci masa mutunci.

Dr. Ya fito ya fice, ba tare da ya ce mata uffan ba, Kausar na ta ba ta haƙuri, Abdul ya shigo rai a ɓace ya kalli farida ya ce "Maama wannan abun da ki ke yi ba mutuncinki bane ba, duk maƙwabta na jinki, wannan zubar mana da mutunci ki ke yi"

"Haba yaya Abdul, ka san menene kishiya kuwa? Kuma kishiya da mahaukaciya ku baku san komai a kan wannan lamarin ba"

Farida ta ce "Rabu da shi, baƙin ciki ya kasheni, sai su ci duniya da tsinke da ubansa, bands butulci da zalunci irin na ɗan Adam, duk halaccin da na yi masa ya rasa da mai zai saka mini sai wannan rashin mutuncin, maimakon ya auro cikakkiyar mace da zan yi kishin na gaske da ita, sai ya ƙare a mahaukaciya, ai da ƴar tata ya aura shi ne ƙarshen soyayya"

Abdul ya ce "Koma wa ya auro, hakan dai zaki yi maama, wallahi Abba ba ma bin sa bashi, shi ne yake bin mu, menene bai yi mana ba na kulawa a rayuwar nan, shekara sama da ashirin yana ƙarar da ƙarfin sa saboda mu, kuma lokaci ɗaya duk sai mu haɗu mu goya miki baya mu rabu da shi? Bamu yi masa adalci ba, kuma wataƙila da baki kori ummi ba, da bai ce zai ƙara auren ba".

Muguwar ashariyar da ta luluƙa masa ya sanya shi waro ido, ba shiri ya fice ya bar su da kausar.

Ta kalli kausari ta ce "Ki shirya ki je gidan ta, ki dawo mini da ƴa ta, idan ta ƙi ki ci uban noor ɗin, tun da ba mahaukaciyar uwarta ce ta haifeta ba, sannan ki tabattar kin ci mata mutunci da sai ta zubar da hawaye"

Kausar ta ce "Zan yi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga fa yadda ki ke haki" gaba É—aya farida sai ta fi kama da mahaukaciyar tuburan.

Noor kuwa ta miƙe abun ta a gidan ummi, ummi ta fara samun sauƙin wasu abubuwan saboda noor, ita take bata kuɗin motar zuwa makaranta boko da islamiyya.
Ummi ta ce mata yakamata ta biya gida, su gaisa da su farida, amma ta ce ita ba ta son ta je gidan ta tarar da su Abba suna faÉ—a.

Ɓangaren mami ma abubuwa sun yi mata zafi sosai, dan haryanzu Alhaji fushi yake yi da ita, ga ɓangaren su safiyya sun hura mata wuta, dan zuba ido suke yi, a danƙaro musu kayan lefe.

Sai dai zancen nema yake yi ya shiririce, dan Alhaji ma ya ce kar ta sake yi masa maganar auren raihan, shi na fari da ya yi masa, shi ne hurumin sa.

Kuma sanin halinta ya sanya yayi mata gargaÉ—i na gaske, a kan gidan da raihan ya saya wa ummi.

Kausar kuwa da ta je gidan ummi, hankali kwance ta tarar da su har da raihan suna kallo, babu abun da ya dame su.

Sai duk ta kasa sakewa ta yi rashin mutuncin da ta ƙullo, duba da yadda raihan yake muzurai.

Hankali kwance ummi ta karɓeta, ta karrama ta.

Ta ce "Dama maama ce ta ce noor ta koma gida"

Raihan ya ce "Saboda me?"

"Haka dai ta ce"

Raihan ya ce "To ai ni mun yi magana da dr. Ya ce tayi zamanta, ta din ga zuwa makaranta daga nan, amma noor kin ji abun da mamanki ta ce"

Noor ta tura baki ta ce "Ni na tambayi Abba ya ce na zauna, zan koma amma ba yau ba" juyin duniya, noor ta ce ba in da za ta je, ita fa maama ba son ta take yi ba, dan kullum cikin yi mata faÉ—a take da zaginta.

GAGARWA.

"Kai auwalu, daga kai har Alhassan kun kashe zuciyarku, kalli yadda rana ta take, sai baccin asara ka ke yi ba zaka tashi ba?" Tayi maganar tana dukan ƙofar ɗakinsa.

Amma ya ƙi tashi, ta gama ɓaɓatunta yayi burus da ita, ta ƙyale shi, ta koma sashinta, ta ɗebi ruwa tana alwala.

Ta É—ago za ta tashi, ta ji an yi ball da ita gaba, ta dungura.

Cikin tangaÉ—i da maye, ya ce "Ke banzar tsohuwa, ban gaya miki babu ruwanki da ni ba? Ko in tashi ko kar in tashi ban hana ki shiga harkata ba"

Iya da ƙyar ta motsa, wani irin jiri ya din ga ɗibar ta, taga gari yana jujjuya mata.

Kan ta ankara, ya sake surarta yayi jifa da ita kamar tsummokara.

Ta kurma uban ihu, amma ba kowa, ya din ga jifa da ita, tun tana ihu, ta koma kakari, jini ya fara zuba daga hancinta.

Ya sake surarta yana tangaÉ—i ya nufi wawakekiyar rijiyar da ke tsakar gidan.

Ayshercool

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

47

PAID ADVERT

*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*

47

Gadan-gadan ya nufi rijiyar yana tangaÉ—i.

Amaryar kawu Ilyasu ta ƙwala ihu da salati, bayan ta shigo daga cefane.

Bai kai ga rijiyar ba, ya sake yin jifa da ita. Ta tafi da gudu tana kiran sunan iya, sai dai jini sai zuba yake daga hancinta.
Chapter 122 · 0% Book details