← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 134

Sashe 82

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta É—an yi murmushi ta ce "Muryartaka ba gata nan a what's app É—ina ba? Su Alhaji sun zo É—azu"

Yayi murmushi ya ce "Shiyasa na ji bakin ki yaƙi rufuwa, zaki yi wuf da ɗan kyakykyawa yaron da ki ka raina"

Ta ce "Hmm amma kuÉ—in da su Alhaji suka kawo, har da kayan lefe ko?"

"Yaushe muka yi haka da ke?"

"Ba muyi ba tambayarka kawai na yi, kuɗin da yawa ka manta na taɓa aure ne?"

"Ke ki ka san kin taɓa auren ai, ni ban sani ba, kuma ke ina ruwanki da abun da zan yi, ke da ba kya so na, ina ruwanki idan zan yi lefen koma ba zan yi ba"

"Yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye.

Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ummi ke malama ce, annabi Sallallahu alaihi Wasallam, mutum ne mai hidimtawa iyalinsa, kuma rayuwarsa ce abun koyi a garemu, haka zalika mahaifina mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai haka na tashi na ga yana yi, kuma babana mudubina ne, bana cikin maza masu nakasashiyar zuciya duk abun da na kashewa wadda zan aura ribata ce, kin san tsare hakkin iyali yana ƙarawa namiji kima da kwarjini a wurin iyalinsa. To balle ni da nake yaro kuma ba a so na, dole sai na yi aiki tuƙuru tukuna, dan saya wa kaina kima a wurin matata"

Ummi ta numfasa ta ce "In dai kai Allah ya ƙaddara ka zama mijina, ba ka buƙatar wahalar da kanka, zan yi maka biyayya iya yi na, ban yi wayo sosai da mahaifiyata ba, amma mama mace mai matuƙar biyayya ga babana"

Cikin yanayi na nishaÉ—i ya ce "Allah ya sakawa iyayenmu da mafificin alkhairi ummi, ya nuna mana auren nan lafiya" Ummi ta yi shiru ta kasa amsawa.

Hira suka yi sosai, sannan suka yi sallama.

Raihan yana zaune a É—akinsa yana danna system yana shan lemon kwali, Salim ya yi sallama a É—akin.

Raihan ya amsa yana mamakin ganin Yaya salim a É—akin nasa, dan sai ya shafe shekara bai shiga É—akin sa ba.

Kamar wanda yayi baƙo raihan ya tashi yana faɗin "Sannu da zuwa yaya"

Salim ya jinjina masa kai ya zauna, ya kalleshi ya ce "Yanzu muke magana da hajiya, ashe yau an yi maka engagement? Ubangiji Allah ya sanya alkhairi babban mutum, girma zai ƙara hawa kanka, Allah ya sanya alkhairi"

Duk in da É—an uwa yake É—an uwa ne, maganganun ummi suka din ga dawo masa, ya dubi Salim ya ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya sa ayi naka kafin ayi nawa"

Salim yayi murmushi ya ce "Sai ka ce wasan yara? Allah ya baku zaman lafiya, ace ina gaisheta" yayi maganar yana shafa sumar raihan.

Salim shi ne babba, aƙalla ya kai shekaru talatin da huɗu, ya fi Sagir sauƙin kai, ba shi da magana, sannan mutum ne mai son kaɗaici, amma akwai abokan banza, dan su suka koya masa shaye-shaye.

Raihan ya ce "Za ta ji, amma ita tana yawan cewa a gaishe ku, da kai da Yaya sagir"

Ya É—an kalli raihan ya ce "Ta sanni ne?"

"Eh, ummi ce ai ƙawar maryam, ta sanku, sannan ina yi mata zancenku"

Ya ce "Ohh that dark lady, mai brwon eyes ko? Wow na yi maka murna she's decent and good lady"

"Amm yaya dan Allah da gaske ummi mummuna ce? Mami tana ta complain a kan hakan"

Salim ya ce "Ita wannan mamin naka, ra'ayi idan ba nata ba, kowa bai iya ba, just go ahead, ita kuma mamin ka yi ta sakata a addu'a, Allah ya kwantar maka da hankalinta shikenan kawai"

Raihan ya riƙe hannun Salim ya ce "Na gode sosai Babban yaya, Ubangiji Allah ya baka kujerar MD Tahir and Son's"

Salim ya ce "You are not serious, kai dai Allah ya tayaka riƙo, ya sanya maka albarka, take care" ya fice daga ɗakin.

Raihan yayi shiru, babu shaƙuwa sosai a tsakaninsu, saboda shi raihan a Bauchi ya ƙarasa girma, gidan yayar Alhajinsu Hajiya Aisha, mijinta da ita da Alhaji duk cousin's ne, shi kuma su Salim suna nan kano, kuma mami ba ta da aiki sai gaya masa yayi a hankali da Hajiya da yaranta ba sa ƙaunar su, kuma kar su Sagir su koya masa shaye-shaye.

Sai dai shi bai ga alamar hakan ba, hasali ma ba sa wani shiga shirgin sa, dan ba sa'aninsa bane ba, har gara Sagir ma suna faÉ—a da raihan sosai. Hajiya kuwa kamar É—an da ta haifa haka ta É—auki raihan da ma duk Æ´aÆ´an mami, amma matan duk mami ta hure musu kunne.

Farida ko a jikinta, jin an kawo kuÉ—in auren Ummi, dan kawai jikinta bai bata ummi wani mutumin kirki za ta aura ba, dan da an kawo abun arziki da jiki na rawa dr. Zai gaya mata, sai dai yayi mata shiru bai gaya mata me aka kawo ba, kuma wa za ta aura ba.

Noor ta kasa nutsuwa saboda murna, sai tsara yadda bikin zai kasance take yi, har da cewa sai dr. Ya É—inka mata sababbin kaya guda hamsin har da irin na amarya da ango.

Saboda tsokana ta je ta samu kausar tana bata labarin yadda raihan yake, ta koreta amma ta ƙi tafiya ta cigaba da cewa "Kin ganshi kuwa? Wallahi duk saurayinki babu mai kyan sa, fari ne fa sosai da sosai, wallahi motarsa ta fi biyar, masu kyau ɗan bala'i, idan yana magana yana ɗage girarsa guda ɗaya, me kyau da shi" kasancewar hankalin kausar ba a kan noor yake ba, ya sanya sam ba ta fahimci me noor ɗin ke faɗa mata ba.

Mami ba ta nemi raihan ba, sai yau da safe ya je karyawa, tayi masa shiru, ya gaisheta ta amsa masa, ya kammala cin abinci, ya tashi zai fita, ta janyo hannunsa da ƙarfi ta tankaɗa shi har ɗakinta ta mayar da mukulli ta rufe, ta dawo ta ɗauke shi da mari har kashi biyu.

Sai dai ya tsaya yana kallon mami da mamaki, ba tare da kuma ya yi yinƙurin kare marin ba.

Ta ɗora da ɗura masa ashar, amma ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kallon tiles.

"Ashe ba ka da hankali raihan, ba ka da mutunci ba ka san abun da yake maka ciwo ba, ashe yarinyar nan bazawara ce, ka je zaka auri bazawara sauran wani, da ƙuruciyarka da komai, ashe baka san me yake yi maka ciwo ba?
To ai dama ni na ce zan yi maka aure ko? To na janye na fasa, ba zaka yi auren yanzun ba, sai ranar da ka fuskanci kai mutum ne da daraja da girma. Dan haka umarni nake baka ba shawara ba, ka je ka janye maganar auren nan. Saboda hauka tana bazawara ga muni da rashin gata, amma ka ɗauki kuɗin aure har dubu ɗari biyar, ka bayar a kai, to baka isa ba wallahi, idan har ni na haifeka ka ka je ka gaya wa mahaifinka ka fasa auren nan, ba zaka aureta ba dan kai kaɗai ne kawai zaka gaya masa haka ya yarda, idan ba haka ba zaka fuskanci abun da baka taɓa tununi daga gareni ba, na gaya maka. Ka wuce ka je ka same shi ka ce masa ka fasa yanzu ba anjima ba. Matar da na zaɓa maka ita zaka aura, duk matan garin nan masu kyau da aji, ba ka ga kowa ba sai wannan cilakowar?"

Tuni fuskar raihan ta yi jawur, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, saboda tashin hankali da ɓacin rai, ya buɗe ƙofar ya fice, yana gazgata maganar ummi da ta taɓa ce masa su mata mutane ne masu masifar son kansu, bai yi mamakin hakan daga mami ba, duba da yanayin halinta kuma gashi jiya ya ga Anty rakiya ta zo gidan, ya san ita zata sake ziga mami, amma ita bazawara ba mutum ba ce?.

Zuciyar sa na wani irin tafasa ya tafi sashin Alhaji, Alhaji tashin sa kenan, yana ta shiri za shi Abuja, ya ga raihan, bai yi wa raihan magana ba, Raihan ya ce "Na fasa auren ummi, na janye, ka karɓo kuɗin auren, amma idan aka karɓo kuɗin auren nan an karɓo kenan aure sai dai in ga ana yi, babu ƴar da za a sake kaiwa kuɗin aure da sunan zan aureta" yana gama maganar ya juya ya fice.

Alhaji bai yi niyyar dakatar da shi ba, dan ko magana bai yi masa ba, ko raihan bai yi masa bayani ba, ya san bilki ce ta kunno shi, dan raihan akwai ladabi, idan ya je bango kuma akwai taurin kai, dan haka Alhaji ya ƙyale shi, da nufin idan ya huce sai su yi maganar.

Ummi na wurin aiki tana ta shigar da sabbin price a computer, ta ga raihan ya shigo, fuskar sa babu walwala.

Bai ce mata uffan ba, ya zagaya ya zauna a kujerar kusa da ita.

"Baka gaya mini zaka zo ba, ai da na dafo maka wani abun, baka da lafiya ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Bauchi zan tafi daga nan, na zo mu yi sallama ne, babu lallai na dawo nan kusa"

Da sauri ummi ta ce "Saboda me?"

Ya kalleta wani abu mai É—aci na kaiwa na komowa a zuciyarsa, ga wani irin tausayin ummi da yake ji, idan ya fasa aurenta bai yi mata adalci ba sam.

"Ka gaya mini mana, menene meyafaru gaba É—aya ka yi wani iri, me aka yi maka ne?" Tayi maganar cikin rauni sosai, saboda ba ta fiye ganinsa a irin wannan yanayin ba.

Kasa magana yayi, ya tashi ba tare da ya ce mata komai ba zai tafi, karo na farko ta riƙo hannunsa a nata ta ce "Ka zauna ka gaya mini menene, ka ɗaga mini hankali ka gaya mini menene?"

Ya zauna a hankali ya ce "Ummi, ban san me yake shirin faruwa ba, daga yanzu zuwa ko yaushe abu mai daÉ—i ko akasin haka ka iya faruwa, dan Allah ko me ye ya faru, ni dai ki saka a ranki ina son ki sosai da sosai ummi, kuma ba zan daina sonki ba, ki tsananta yi mana addu'a, ko da ke ba kya so na, ni ina sonki ummi"
Chapter 82 · 0% Book details