Sashe 69
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern makarantar islamiyyar su ya zo dubata ba, har da kawo kayan dubiya, headmaster yana daga cikin mutanen da su kan hantari ummi, mussman idan ta je a makare, gashi ita kuÉ—in makaranta take biya, wurin É—aukar nata karatun, ita kuma koyarwar da take yi, ko sisi basa bata, dan raihan har mita yake yi, a kan hakan ya ce yakamata ko ba yawa a din ga biyanta.
Amma ga mamakinta sai ga headmastern ya zo dubata, ba ta kawo komai a ranta ba, tayi masa godiya ya tafi.
Saboda rigimar raihan, ummi ta lallaɓa ta koma aiki, dan kuwa idan ba ta yi wasa ba, a sintirin da yake yi, sai an san da alaƙarsu, alaƙar da ba ta san ta yaya za ta yi bayaninta ba.
Har wurin aikin yake bin ta, ya tabbattar ta ci abinci ta sha magani.
Ta sanar masa da batun zuwa gagarawa, da yadda take cikin damuwar hakan, kar idan ta je a riƙeta a can.
Raihan ya ce "Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru sai ikon Allah, kuma babu wanda zai rabaki da garin nan, abun da nake so da ke, ki yi iya ƙoƙarinki ki sake samo information a kan mama idan kin je, zan san ƙoƙarin da zan yi a kan hakan, da wallahi suka riƙe ki a garin nan, ba abun da zai hana ni binki"
ÆŠan buÉ—e baki ta yi tana kallon sa, da gaske har cikin zuciyarsa yayi maganar.
"Raihan wai ranar da na yi aure, yaya zaka yi ne?"
"Yaya zamu yi dai? A Æ´an uwanmu zan samo miki miji nagari, ni kin san kuwa mami ta sakani a gaba, wai tun da Alhaji ya bani ragamar kasuwancin nan, wai sai na yi aure"
Ummi tayi dariya ta ce "DaÉ—ina da mami hangen nesa, wallahi kuma da gaskiyarta"
Ya girgiza kai ya ce "Ba zaki gane bane yanzu haka kawai ganina ki ke yi, bana son yawan takura miki, amma sai kin tayani da addu'a, akwai ƙalubale sosai a harkar kasuwancin nan, kuma kamar yadda ki ka faɗa, akwai buƙatar yadda ki ka gaya mini, ina buƙatar mace ta gari to assist me, wallahi ummi ban taɓa budurwa ba, kuma bana son auren haɗi, ni ba zan auri matar da bana so ba"
Ummi ta yi dariya ta ce "Za a sha ƙiriniya, amaryar ka za ta sha fama da ƙuruciya"
Kallonta yayi ya ce "Kin rainani da yawa fa, idan na fita kin ga yadda nake tsare gida kuwa a waje, a man of 24yrs, ki ke cewa za a sha ƙuruciya"
Ummi ta waro masa idanunta ta ce "24 kuma, ka ji tsoron Allah raihan, yaushe ka kai 24yrs kuma?"
Ya ce "Wallahi na cika 24yrs"
Da suka yi lissafi, watanni goma sha huÉ—u ummi ta bashi.
Ya ce "Da na san ba wani girmata ki ka yi ba, ba zan bari ki raina ni ba, ashe ma sa'ata ce na ma fa fiki girma ummi, daga yanzu ma ni ne yayanki yaya zaki din ga ce mini"
Ummi ta ce "To meye a ciki Han? Ai duk in da namiji yake jagora ne, mai girma MD, sai dai ba a canzawa tuwo suna, ni yayarka ce"
Yayi dariya yana shafa sajensa, ya na bin ta da kallo, ya kasa gane a wane bugire ma ya ajiye ummin ne a yanzu.
"Me ka ke kallo ne?"
"Your eyes, masha Allah i like them, ina son idanunki"
Ummi ta rausayar da kai ta ce "Idan ka faÉ—i haka kana tuna mini da babana, idan na ce masa baba wai idona irin na akuya ne da mage? Sai ya ce A'a, idonki mai kyau ne, ina son idonki ummina"
Raihan ya ce "Allah sarki, Allah ya jiƙan baba da rahama"
"Amin Yaya Han, ina godiya sosai da sosai"
Yayi murmushi ya ce "Han sai ka ce sunan Æ´an china, amma duk yadda ki ka faÉ—a zan amsa, ki kula da kanki sosai a garin idan kin je, zamu din ga waya har ku dawo"
Ummi ta ce "To, in sha Allah"
Ummi na son nunawa raihan hotunan da ta yi da rigunan nan a wayarta, amma ta kasa, shi kuma bai takurata da tambayar bai taɓa ganin ta saka kayan da ya bata ba.
Ummi ta lura kamar babu jituwa tsakanin dr. Da farida tun wancan karon da ya koma aiki, har wannan dawowar tasa, sai dai kasancewar ummi ba huruminta bane ba, ya sanya ta cigaba da sabgoginta.
Ranar tafiyarsu gagarawa na ƙaratowa, adadin tashin hankalinta, da fargaba na ƙaruwa, sai dai ta na ta addu'a a kan Allah ya kare faruwar dukkan wani abun ƙi.
Ta É—auki É—aya daga cikin dogwayen rigunan wurin raihan, da abun da ba a rasa ba, ta haÉ—a kayan da zata yi tafiyar da su.
Dr. Ya ce har da noor zasu tafi, noor ta din ga murna, tana jin daÉ—i.
Suna tafe a hanya, adadin fargaba da tashin hankalinta, yana ƙaruwa, tana tuna irin azabar da ta sha a gagarawa, ta din ga fatan ina ma har ta je ta dawo, ba zata haɗu da wasu mutanen ba, dan ko ambatar sunansu na sanyata cikin damuwa.
Kwantsin yaran gidan ne suka firfito, suna shelar ga kawu Yahaya ya zo, yaran da galibi duk ba ta san su ba, dan da yawansu bayan ta baro garin aka haife su.
Kallon gidan ummi take, zata iya cewa wannan gidan shi ne kurku mafi azaba a tarihin rayuwarta.
Da yawa yaran basu san ummi ba, dan haka suka din ga bin ta da kallo.
A tsakar gida sashen iya, mata nata hada-hadar shirin biki, sallamarta ce ta janyo hankalin matan.
Wanda suka santa, suka din ga zuzuta girman da tayi, ta É—aga kai ta kalli É—akinsu, É—akin mai É—auke da É—umbin tarihi, alamu ya nuna akwai mutane a É—akin, amma ba ta san suwaye a É—akin ba.
ÆŠakin Iya ta nufa, ta tarar da Iya zaune a tsakar É—akin ta, tana ta bayar da umarni.
Saroro ta bi ummi da kallo, cikin ƙarfin hali ummi tayi murmushi tana gaida Iya.
"Yau Allah ya kawo ki wurin mayu kenan, wanda za su cinyeki?" Ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kai.
Noor dai ta kame tana kallon kowa É—aya bayan É—aya.
Dr. Ya shigo shima yana ta gaisawa da mutane, da ya isa ɗakin iya, ko gaisawa ba su yi ba, ta fara masifar ya bar ummi ta balage ba aure, kodayeke dama ya za ayi ta auru, ai dama tun da tun farko taƙi amincewa da rufin asirin aure, ya goya mata baya, haka zata riƙe a gida ba aure.
Aikuwa kawu yahaya ya haÉ—e rai ya ce "Iya dan Allah ya isa haka, haba ummin guda nawa take? Ke ba ki yi farincikin ganinta tayi ilimi, a nutse a kame ba, ni na zaci wannan abubuwan duk sun wuce tun a baya?".
Ummi ta sha mamakin yadda Iya ba ta canza ba, tsawon wannan lokacin.
Tun a daren yaya magaji ya zo wurin ummi, sun daɗe suna hira, tare da murnar ganin sauyin da ummi ta samu, ya din ga gaya mata irin yadda abubuwa suke ta kwaɓewa a cikin dangin nasu.
Abubuwan duk babu daɗin ji, mussaman gidan Idris, yarinyar su ta gaba da alfatiha, ƙalubalen da take fuskanta ya sanya ta fara fanɗarewa ita ma.
Al'amarin bai yi wa ummi daÉ—i ba, wanda jahilci ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanen gidan.
Washegari ɗaurin aure, bayan ummi da noor sun yi wanka sun shirya, ta ja noor suka fita gidansu na'ima, amma ta tarar maman na'ima ta rasu, ƙannenta duk sun yi aure.
Doguwar riga ummi ta saka ta wurin raihan, sai dai tana jin ta kamar ba ita ba, saboda jin ta take a takure a cikin kayan, dan ma rigar isashiya ce, sai dai fa ta zama a bar kallo a cikin gidan, duk in da tabi sai a kalleta.
Iya ta din ga nuna wa mutane ummi, ga ƴar wurin bashir, da Idiris ya aura taƙi zama, ta bi kawu yahaya gashi haryanzu ta gama balagewa ta riƙa ba aure shi yanzu yana da yara biyar.
Idiris kuwa tun da ya ga ummi kamar maye, saboda azabar kallo, sai dai ga mamakinsa ummi tayi masa kwarjinin da ko magana ya kasa yi mata, gashi dai ba wani abun ta canza ba, kamaninta suna nan, sai dai ta girma ta cika, kai ba ka ce tana fuskantar ƙalubale a in da take ba.
Ko in da Idris yake bata kalla ba, balle ya sanya ran za ta gaishe shi.
Su Alhassan ma duk sun girma, da su auwwalu, sai dai babu wani cigaba su ma, dan kuwa auwwalu ma ya zama É—an shaye-shaye sosai da sosai, dan har prison yayi, babu sana'ar kirki ya zama criminal.
Alhassan ma babu sana'ar kirki, sai kamasho da Æ´an buge-buge.
Raihan kuwa yana ta kiran ummi a waya, da jin ko komai lafiya ƙalau.
Ana dawowa daga É—aurin aure, kawu yahaya ya ce zasu koma gida, sai dai ummi ta sha surutun mutanen gidan na rashin aure.
Suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha, a kan ta kwantar da hankalinta a kan rashin aure, saboda lokaci ne, shi aure ba gaggawa ba samun nagartaccen miji da gidan aure mai cike da farinciki shi ne abun fata.
Ita dai ummi ganin sun taho daga gagarawa ya fi komai faranta mata rai.
Tashin hankali ba a saka masa rana, bayan su ummi sun sauka a kano gida, ummi ta tarar da ɗakinta a garƙame an saka masa mukulli.
Falo ummi ta tafi, ta samu Farida ta ce "Anty ke ki ka kulle É—akina?"
"Eh ni na kulle, saboda ba gidan ubanki bane ba? Dan mun riga mun yi da shi ba zaki dawo mini gida ba"
Saroro ummi ta yi tana kallon fareeda, dr. Ya fito yana faÉ—in "Wai farida bamu gama wannan maganar ba? To wallahi idan ki ka cigaba da matsawa, sai dai ke ki bar gidan, kema ki koma naku gidan"