Sashe 15
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba wani a razane, da a razane take ai da ba ta kai kanta ba, yarinya ƙanƙanuwarta da ita, ta san ta je wurin namiji"
"Haba iya, me ummin ta sani da zaki faÉ—i wannan mummunar maganar a kanta?"
Iya ta ce "Zaka zo ka kai mini dusar ko ta É—auka ta kai mini?"
Ya ƙarasa ya ɗauki dusar ya fita, zuciyarsa kamar ta tarwatse, tausayin yarinyar na damunsa sosai da sosai.
Kwanaki biyu tsakanin abun da ya faru, sannan idiris ya shigo sashin Iya.
Iya ta dube shi ta ce "Idris, kashedi zan yi maka a kan yarinyar nan, kar ka kuskura ka sake saka yarinyar nan a loko kana lalubeta, wallahi idan ka sake wani abu ya afku ba zan rufa maka asiri ba, kuma ba zaka janyo mini masifa ba, kai gashi ba sana'a ba balle ace ayi maka aure, in huta. Ina yi maka kashedi, wallahi wani abu ya faru ba zan saurara maka ba, na gaya maka"
Cikin fushi ya ce "Me kuma na yi, magaji ne ya zo ya ce na yi mata wani abu?"
"A'a ni banga magaji ba, bai gaya mini komai ba, fuskanta kawai na yi"
Ficewa yayi ba tare da ya sake magana ba.
Rashin samun biyan buƙatar sa a jikin ummi, ya sanya ya ji ya ƙara tsanar yarinyar, ko son ganinta ba ya yi, ita kanta ummi, har fargaba take yi a aike ta, saboda bayan iya ta yi masa wannan faɗan, sai da ya zane ta, saboda a zaton sa ita ta gaya wa Iya.
Duk wannan cin kashin da ake yi wa yarinyar, daga ƴan uwan ubanta da suke ciki ɗaya, da wanda uba suka haɗa da matayen su, babu wanda ya taɓa shawartar iya a kan sassautawa ummi azabtarwar da ake yi mata, tamkar ƴar tsintuwar da ta faɗo daga sama.
Azumi saura wata biyu, aka yi bikin na'ima, ta yi kuka sosai, ciki har da na rabuwa da ummi, dan har cikin zuciyarta take jin rabuwa da ummi.
Mariya kuwa tun ƴan uwanta na ta tata, suna rarrashin ta, suna bata haƙuri, har suka zubawa sarautar Allah ido suka ƙyaleta, ta riga dai ta kamu da larurar hawan jini, a hankali kuma ciwon damuwa ya fara addabar ta, kullum tana ɗaki, daga bacci, kuka sai shiru.
Yaya É—an lami ya fara tunanin ko ta koma makaranta, amma yanayin da take ciki, ya tabbatar masa da ko an mayar da ita makarantar ba za ta iya mayar da hankali ba.
Dama labarin haihuwar ta ta ko su iya ba a gayawa ba, dan gaba É—aya sun fuskanci sabgar Iya babu Allah a cikinta.
Yaya ɗan lami kuwa da suka ga mariya taƙi sakin ranta, ya ƙare mata cin mutunci, tare da tabbatar mata da muddin ta je wurin su Iya babu su babu ita, ƴa ce idan ta girma da kanta za ta neme ta.
Watan azumin ramadana ya kama, wanda hakan ya sake jefa ummi tsaka mai wuya. Ba iya azumi take yi ba, dan haka babu mai kulawa ya bata abinci, haka za ta yi ta gararanba ta wuni a kwance, idan makaranta ta je, tana kallo yara na ciye-ciye, ita ba raɓar su take yi ba ma, balle ta yi musu kwaɗayi, ko kuɗin makaranta ba bata ake yi ba, dan haka bata saba da kashe-kashen kuɗi ba.
Sai an sha ruwa take samu ta ci abinci, sai da hashim ya fuskanci ba ta samun abun da za ta ci da rana, shi ne yake rage mata abincin sa, da safe ya bata, da rana ya sai wani abun ya bata. A haka har aka ƙare azumi.
Da salla kowane É—a cikin kyakywar shiga mai kyau, ummi kuwa kayan bikin na'ima ta saka, da suka fara koÉ—ewa, da takalmin makarantar da kawunsu ya saya mata, shi ta koma tana sakawa tayi yawo da shi a gari, saboda ko silifas ba ta da shi, wanda naima ta saya mata tuni ya lalace.
Yara na ta shiga su na fita, ummi kuwa na ƙofar ɗakin mamanta, ta zauna tana wasa da duwatsun wurin.
Hashim yayi sallama, ummi ta amsa cikin Æ´ar siriyar muryarta.
Ya ƙarasa in da take zaune, ya ce "Kin je sallar idi ne?" Ta girgiza kai alamar a'a.
"Me ki ke yi a nan wurin?"
Ta ce "Bakomai"
"Kin ci tuwon salla kuwa?"
Ta ce "A'a iya dai ta ce zata bani"
Ya miƙa mata hannu ya ce "Taso mu je"
Ta saka hannunta a nasa, ya ja ta zuwa sashin mahaifiyar sa.
Babansa ma, da ake cewa baba sagir, yana zaune yana cin abinci.
Ummi ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata babu yabo ba fallasa.
Ya ce "Yaya a zubawa ummi abincin salla dan Allah"
Ta ce "Ga maimuna nan, ya zuba mata" ta kalli ummi ta ce "Ke ummi baki da kayan salla ne, ki ka saka wannan koÉ—aÉ—É—iyar atamfar?"
Ummi tayi shiru tana kallon ta.
Aka kawo wa ummi abinci, ya saka ta wanke hannunta, ta zauna ta saka tuwon sallar nan a gaba tana ci, tana yi tana kallon yadda yara suka yi kyau sosai a sababbin kaya.
Ta gama ci ta hau tattara musu kwanukan wanke wanke, ta share musu tsakar gida.
Hashim ya dawo sashin, ya tarar da ummi ta haÉ—a kwanukan wanke-wanke.
"Me kuma zaki yi?"
"Wanke-wanke zan yi".
"Ke yara na can waje suna tsalle-tsalle, suna wasanni, amma ke kina nan ki na haÉ—a wanke-wanke, ki je ki yi wasanki sa yi wanke-wanken da kan su"
"A'a bani da kayan salla, idan na fita tsokanata za ayi, su ce mini baƙa" tayi maganar tana ƙoƙarin jan kujera ƴar tsuguno tayi wanke-wanken.
Shiru yayi yana kallonta, cikin tausayawa.
Yana zaune yana kallonta, gata yarinya ƙarama amma ta riga ta saba da wahala, yadda yake wanke manyan kwanukan da aka ɓata da miyar abincin salla.
Wata ragowar miya da ta rage, ta zuba mata ruwa zata zubar, idirisa ya kawo kai ta watsa masa a jikinsa.
Ayshercool
08081012143
           *CUTARWA!*
Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
What's app 08081012143
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
P8
Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ƙaraso kan ummi, yayi ball da ita ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa.
A cikin azama hashim ya ƙarasa, ya hankaɗe idiris, yana faɗin "Idirs meye haka?"
"Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?"
"Kai za a cewa dabba, ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa yarinyar nan yayi yawa fa"
Ummi kuwa karo tayi da ƙafar tukunyar ƙarfe, fiƙarta ɗaya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo.
Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faÉ—in "Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?"
Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun bakinta ya gauraye da jini".
"Ita kuma wannan meya sameta?"
"Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan" Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris.
Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta ɓata da miya.
Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita.
Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani.
Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai.
***
Mariya na zaune a ɗaki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai maƙwanciyar su suke yi, wadda ƴar ta aka kai gagarawa, suka haɗu da balarabe suka yi aure.
Tana bawa mama labarin Æ´ar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa.
Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan Æ´ar jummai a kai a bawa ummi ba.
Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan Æ´ar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuÉ—i mijinta É—an sanda ne, idan suka haÉ—u da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta.
Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa "Ai nan asalamiyya ke bani labari, ƴar da mariya ta baro, wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ƙafarta, na ce ta ɗan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun ɗaukko yarinyar nan"
Mama ta ce "Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ƙi, shiyasa muka ƙyalesu, ba su da mutunci ko kaɗan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ƙyale su idan yarinyar ta girma ta nememu"
Jimmai ta ce "Ashsha! To Allah ya kyauta".
Mama ta amsa da "Amin"
Mariya ta ajiye ninkin, ta haÉ—a kai da gwiwa ta din ga kuka.
Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga ɗakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce "Mariya na san kin ji abun da jimmai take faɗa, amma haƙuri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini" shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ƙona zuciya, tana ji a ranta ba zata taɓa yafe wa Iya ba.