← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 134

Sashe 38

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida ta ce "Rahama ƙyaleta, kar ta ja miki bala'i, ta riƙe miki kurwa kamar yadda ta yi mini, wallahi sai ya biyani kuɗina, kuma a wannan karon ko ubanta zai fito daga kabari ta din ga yawo da shi, sai ta bar mini gida ta koma in da ta fito, ba zan zauna da ɓarauniya ba, ga sata ga maita ba zai yiwu ba".

"Antyn dan Muhammadurasulillah ki yi haƙuri, dan Allah kar ki mayar da ni ƙauye, wallahi ban taɓa sata ba, ban san menene maita ba"

"Zaki santa yau, ɗaukko ƙullin kayanki ki wuce, ba zai yiwu ba"

Suka hankaÉ—o ummi waje, duk attention É—in mutanen gidan ya dawo kansu, noor da ta fara dariya, tana hango ummi ta hau dariya tana É—aga mata hannu.

"Lallai farida an haÉ—aki da masifa, satar kuÉ—i kuma, wannan wataran sai ta ganki a makara hankalinta zai kwanta" a tsakiyar falon suka zazzage mata kayanta, sai ga dubu É—aya sabuwa fil wadda kawunta ne ya bata.

Rahama ta ce "Anty ta fito da sauran, suna wurinta wallahi, kalli dubu É—aya fa a ina ta samu".

Inteesar ta ce "Tashi a caje ki, olay" kausar ta ƙyalƙyale da dariya tana maimaita olay.

Dr. Yayi sallama tare da Abdul ya tarar da ummi a durƙushe, tana ta gursheƙen kuka, noor sai zillo take ummi ta ɗauke ta.

"Lafiya kuwa?"

"Dr. Ni fa na gaji, da abun da yarinyar nan take yi mini, daga bawa rahama ajiyar kuɗi ta kwashe, ta bani kuɗi tun da girma da arziki amma taƙi".

"Shi ne zaki ajiyeta a gaban mutane kina tozarta ta haka? Idan yaranki ne haka zaki yi handling É—in su? Nawa ne kuÉ—in?"

Cikin mamaki ta ce "Au haka ma zaka ce?"

"Na ce nawa ne kuÉ—in?"

"Dubu hamsin" ta bashi amsa tana riƙe ƙugu.

"Sana'ar me ki ke yi da har ki ka tara dubu hamsin? Idan ma akwaita na san a jikina aka sameta, zan biya na kashe maganar nan daga yau, kuma daga yanzu. Ummi ba ɓarauniya ba ce ba halin ta bane". Ta yinƙura za ta sake magana ya tari numfashin ta ta hanyar cewa "Na ce na kashe maganar nan"

Ya dubi ummi ya ce "Ummana, tashi kiyi tafiyarki"

Ba tare da ummi ta yi zuciya ba, ta dubi yarinyar da take ta zillo tana kuka, ta ƙarasa ta ɗauketa, ta nufi ɗaki da ita.

Abdul ya durƙusa yana kwashewa ummi kayanta.

"Farida anya maganin nan yayi kuwa? Kin ga fa abun da yayi miki".

Farida ta kasa magana saboda takaici, yau ta ƙuduri aniyar ummi ta bar mata gida, tun da yau sun yi sababbin ayyuka a gidan.

Ummi kuwa zuruuu tayi da ido, tana kallon noor da ke ta ɓangale baki tana yi mata dariya.

Cikin kuka take yi wa noor surutai, ta ce "Mamana, kin gani ko, tun tafiyarki ban taɓa kwanan farinciki ba, dan Allah mama ki dawo, ko ina ne ki tafi da ni, mama kamar in sha guba in mutu" tayi maganar tana kifa kanta a kan ƴan ƙafafuwan noor, tana wani irin kuka mai sauti"

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

Ayshercool
08081012143
       

                      *CUTARWA!"

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P17

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI

P17

Shiru noor tayi, tamkar tana jin abun da ummi take faÉ—a.

Sosai ummi ke kuka, tamkar za ta shiɗe, duk da ba wannan ne karon farko da aka yi mata ƙazafin sata ba, amma na yau yayi mata zafi da ciwo ba kaɗan ba.

Ji tayi an dafa ta, ta É—ago da sauri dan ba ta ji shigowar mutum ba.

Abdul ta gani a bayanta da kayanta a hannunsa, cikin damuwa ya ce "Dan Allah yaya ummi kiyi haƙuri, na san ba zaki yi sata ba, amma ki yi haƙuri dan Allah ki daina kuka, kar kanki yayi ciwo".

"Yaya Abdul, ya aka yi kai ka yadda ba zan sata ba, amma anty farida da rahama suka ɗora mini sata? Suka ci mutuncina a gaban mutane?" ya durƙusa ya ce "Na san babu daɗi, kiyi haƙuri dai dan Allah"

Ta jinjina masa kai, dan kuwa tana ganin mutuncin Abdul sosai da sosai.

Ya É—ora da cewa "Kar ki ga É—akinki a haka, mun yi magana da abba ne, ya ce a bari mu tare ya ga É—akin da maama zata baki, sai ayi miki furnitures, kar a saka miki ta hanaki É—akin".

Ummi ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka bari yayi mini, ya kashe kuɗi da yawa, ni katifata ta isheni, duk kyan furnitures ɗin da za a saka mini, ƙarshe a tsakiyar ƙasa za a binne ni, hakan ma ya isa"

Shiru yayi yana kallon ummi, ta kwanta a kusa da noor, ta sanya hannunta ta riƙe ɗan ƙaramin hannun jaririyar.

Abdul ya tashi ya fita yana waiwayenta, duk abun da aka yi mata, bai sanya tayi zuciya taƙi kula noor ba.

Kasancewar a gajiye take, wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita, baccin da rabon da tayi makamancinsa har ta manta.

Kwanki uku da tarewarsu, aka kawo wa ummi ƙatuwar katifa, da wardrobe mai biyu, sai ɗan mudubi da stool.

Ba ƙaramar murna ummi tayi ba, tare da wani farinciki, wai duk wannan nata ne abun mamaki.

Kawu yahaya ya fara deciding zuwa ƙauye, ya gaida Iya, dan haka ya tambayi ummi ko za ta bi shi, ta je a gaggaisa.

Amma tayi shiru ba ta ce komai ba.

"Ummana baki ce komai ba"

"Kawu ka ce ina gaishe su, ba sai na je ba" tayi maganar tana addu'a a zuciyarta, kar ya matsa ya ce sai ya tafi da ita, saboda tana tsoron ya tafi da ita, Iya ta sake cewa ba zata biyo shi ba.

"Ƙauyen ne ba kya son zuwa ko ummana?"

Ummi ta gyaÉ—a masa kai alamar eh.

Yayi murmushi ya ce "Kwantar da hankalinki kyakywar uwa, abun da ki ke so shi za a yi, zan sanar da su saƙon gaisuwarki, ko ni ba zan so ki je ba, sai kin zama cikakkiyar mutum, da babu wanda zai tursasaki yin abun da ba kya so a rayuwarki".

Kawu yahaya da kansa ya je ƙauye dan ya ɗaukko iya, ta zo ta ga sabon gidansa da jaririya, amma ta ce ba zata ba, saboda matarsa ba ta da mutunci.

Hashim kuwa yana ganin kawu yahaya ummi ya fara tambayarsa.

Ya ce "Ummi na nan lafiya ƙalau Alhamdilillah, tana nan tana karatunta duk ta ce a gaishe ku"

"Allah sarki ummi, muna amsawa".

Iya ta ce "To wai yaushe zaka dawo mini da ita ne?"

Kawu yahaya yayi murmushi ya ce "Ai Ummi sai Allah ya kaimu lokacin aurenta zamu gayyace ku, ba zata sake zuwa gagarawa ba".

A É—an hasale ta ce "Saboda me?"

"Saboda babu abun da za ta zo tayi muku"

"Kai yahaya bana son sakarci, zumuncin fa? So kake ka raba mini kan iyali?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba, na nemi iznin zuwa da ita, ta ce in gaishe ku, saboda makarantar ta"

"Innalillahi wa Innalillahi raziƙuna, ita ummun ce ta faɗi haka? Ta fifita boko a kaina?"

Magaji ya ce "Iya wa Innalillahi raji'un ake cewa ba raziƙuna ba"

"Zan ci uwarka idan na sake magana ka tsoma mini baki, tun kan a haifi uwarka haka ake faÉ—a, ba damar mutum ya motsa sai ka ce zaka ci gyaransa?"

Ganin Iya na son dasa faifan cin zarafin ummi da iyayenta, ya sanya shi bawa Iya abun da zai bata ya tashi ya ce zai tafi.

Har mota hashim ya raka dr., Ya ce a cewa ummi yana gaisheta, tayi karatu da kyau.

Kawu yahaya yayi alƙawarin isar da saƙonsa ga ummi.
Chapter 38 · 0% Book details