← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 134

Sashe 91

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun ya bashi mamaki, dan haka da safe ya zo har gidan, ya duba ko bata da lafiya ne.

Amma ya ga ta fito da shirinta na zuwa aiki, har ya fara murmushi, kawai ya ga ta yi gaba, ba ta nufo in da yake ba, kan ya bita ga shige lunguna, ta ɓulla titi ta haye napep ta yi tafiyar ta.

Nan da nan raihan ya kiÉ—ime, ya fara tunanin laifin me yayi mata? Da take share shi haka? Ya rigata isa wurin aikin na ta, ya tarar mai gadi ya buÉ—e wurin yayi shara.

Ya shiga ya zauna, yana jiran isowarta, da ta iso É—in ma, tana kallonsa ta ajiye jakarta ta shiga hidimomin ta, kallon ta kawai yake yi, ya zuba mata ido yana son gano meyake damunta, ko me yayi mata, amma ya kasa gano komai.

Ana ta kirnaa a waya, ana jiransa amma yana zaune yana jiran ummi ta gama jan ajin ta saurare shi.

Shi yadda ta share shin, take abubuwan ta ma, burge shi yayi, da alama fushi take yi.

Ga wani irin kyau da ta yi kamar ya sace ya ya gudu, ta yi kyau sosai da sosai, ta ɗan washe sai sheƙi fatarta take yi.

Ta zo ta zauna, ta kunna computer ta, za ta fara aiki, ya zuba mata ido, duk da a takure take da kallon, amma ta wani maze.

Dukan teburin yayi da ɗan ƙarfi, sai da ta razana, ya ce "Yaushe zaki saurare ni ne?"

"Ba rana ta bashi amsa tana harararsa" a ransa ya ce "Wow, ta fara iya tsiwa"

Ya kwantar da murya ya ce "Ayi haƙuri dan Allah, laifin me na yi ne? Kina kallona har ki ka share ni ki ka yi tafiyarki?"

"Ai na zata ɓatan kai ka yi ai, gidansu Safiyya zaka je"

Wani irin shock ya ji da abun da ta faÉ—a, wani irin shu'umin kallo yayi mata, sannan ya ce "Wacece Safiyya kuma?"

"Ka fi ni sani ai, idan ka san an haÉ—aka da wata a gidanku, ni me zaka yi mini?"

"Ke a ina ki ka santa?"

A ɗan ƙule ta ce "Wace irin tambaya ce wannan? Kirana ta yi a waya" tayi maganar tana tura masa wayarta.

Ya É—auki wayar yana dubawa, kawai ya kwashe da dariya.

Ta zuba masa ido tana kallon sa, ya ce "Kina da haƙuri da kawaici a kan komai, amma banda kishi kenan? Aishikenan gaskiya ne Safiyya ita ce wadda ake son haɗa ni da ita, ni kuma ke nake so, shiyasa na ce miki akwai ƙalubale, ko ba komai safiyya ta saka na gane in da ki ka dosa, yanzu zaɓi ya rage naki sweetheart, ki kula da ni sosai kar Safiyya ta ƙwace miki ni, kin san zuciya na son mai kyautata mata, ke kin ce ba kya so na, safiyya kuma tana so na, ki zage damtse kar ki bari a ƙwace ni, i so much love you baby"

ÆŠaga ido tayi ta kalleshi, ya ga kamar hawaye ne yake shirin taruwa a idon ummi, ya tashi tsaye ya ce "Bari in tafi wurin safiyyan, tun da ita take so na, na san zata yi mini, idan kin tashi ki kirani"

"Idan ka je kar ka dawo, a É—aura muku aure yau"

Gwalo yayi mata ya ce "Ki gama iyayin da tsiwar, raihan É—in dai ki ke so".

Ayshercool
08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

                        *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

36

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

AFUWAN BAN YI EDITING BA

36

Ya fice daga shagon yana murmushi, ta iya ɓoye fushinta da damuwa, amma ta gaza ɓoye kishinta.

Yana tuƙi yana tuno fuskarta, wai har da yin fushi saboda shi, fushi sosai kishinta ya fito.

Ya shafi gemunsa ya ce "Ina sonki sosai salma, in sha Allah idan na aureki ba zaki sake yin kukan damuwar rashin wani abu ba"

Ummi kuwa, tayi shiru tana tunani, tare da ganin kamar tayi wauta raihan ya gano tana kishinsa, tayi guntun tsaki za ta cigaba da aiki, kawai sai Safiyya ta faÉ—o mata.

Sai gabanta ya faɗi, gaskiya ne akwai banbanci tsakanin budurwa da bazawara, amma ita babu abun da ya taɓa haɗa ta da Idiris har suka rabu, a take kuma tunaninta ya sauya da tunanin kar matsalar da ta faru da ita a farko ta sake faruwa da ita.

Tayi shiru tana tunani menene mafita? Ita ba ƙawaye ba, mamanta kuma ba lafiya ba su yaya maryam kuma ba sabawa suka yi ba, ko da sun saba ma, ba zata iya gaya musu wannan lamarin ba.

Ta din ga saƙe-saƙe a ranta, ta tuna duk da tsanar da Idiris yayi mata, larurar nan ta ƙara taka muhimmiyar rawa, wurin kashe mata aure, dan da ya samu abun da yake so, da sai ya gama moreta kan ya saketa, ta tuna yadda ya din ga ƙoƙarin haike mata tana yarinya, take ta kawar da tunanin, dan a duk lokacin da ta tuna har kuka take yi, yadda Idris ɗin yake lalubeta, ba ta jin a duniya ko zata yafewa kowa za ta iya yafewa Idiris, ba ta riƙe CUTARWA! idan an yi mata amma cutarwa irin ta iya da Idiris ba zasu goge a tarihin rayuwarta ba cikin sauƙi.

Ta cigaba da tunani a irin wa'azin da take bibiya, mussman na malamai daban-daban da sauran shirye-shiryen gidajen rediyo, domin kasancewar ta ƴar jarida, ya sanya tana yawan sauraren Radio, da bibiyar labarai, ta fuskanci cewa duk soyayyar da namiji yake yi wa mace, idan aka samu naƙasu akwai matsala, ƙila ba lallai raihan ya jure ba ya auro safiyya su juya mata baya, kamar yadda aka yi wa inteesar.

Sai kuma kawai ta ga abun banbarakwai, wai ace raihan ya aureta shi ne mijinta, ta haÉ—a shimfiÉ—a da shi, goÉ—ai-goÉ—ai da ita, kawai ta ji wata kunya ta sake kamata.

A ƙarshe ta yanke shawarar yin haɗin da malamar asibitin nan ta taɓa bata, na kanumfari, citta, namijin goro da tafarnuwa, tun da maganin sanyi ne sosai.

Aikin ma dai ta kasa mayar da hankali a kansa sosai, sai saƙe-saƙe, rayuwar aure rayuwa ce da ke buƙatar a zaunar da mace a karanta mata darussa daban-daban, ba kuma wai sai lokacin da aka kawo kuɗin aure aka saka mata rana ba, yakamata mace ta san wasu abubuwan, amma ummi ba ta da wani da zai zauna da ita ya buɗa mata, duk da daga ita har mijin nata ba wani mai yawan shekaru sosai.

***
Yaya maryam ta kira dr. A waya,suna yi masa tunin ya kawo musu ummi, suka cigaba da shirye shiryen su na al'ada, ga mariya ma duk ta ishesu, har da koke-koke a kan a dawo da ummi.

Ya ce mata so yake ƙarshen wata, tayi sallama da wurin aiki ya rage saura wata biyun sai ta dawo.

Ya gaya musu yadda aka tsara bikin, ta ce a matsayin su na dangin uwa, zasu gabatar da nasu bukukuwan a nan maiduguri, sai su taho da ummin kano, suma su yi nasu.

"Amma ina ganin kar É—awainiya tayi muku yawa, ba sai kun yi ba, ku bari duk ayi a kanon"

Ta ce "Haba baban ummi, ƴar mariyar ƙwaya ɗaya tal mu kasa bajinta a bikinta, a'a ka bari zamu yi mata bikk na gani na faɗa, sai mu taho da ita, da mu da abun da Allah ya yassare mana"
Chapter 91 · 0% Book details