← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 134

Sashe 43

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Yau lahadi, ummi sun yi hutun makarantar islamiyya, sai dai ta kasa zama wuri É—aya ta hutawa ranta, dan kuwa ta san babu wanda ya bata wannan damar.
Dan haka wuni tayi tana kaiwa tare da komowa, wurin yin kwalema da tsabtace ko ina na gidan.

Tana sanye da dogon hijjabinta, da ya zame mata tamkar uniform, duk zafi ko sanyi, ko a cikin gida, da hijjbi take yawo, dan ko da ta fara ƙirgar dangi, tsananta rufe jikinta tayi, balle yanzu da take aji biyar na sakandare ta ƙara cika sosai.

Dan idan tana girki, wuta ta sha kamo mata hijjabin, ko ta yi ɓarna a kitchen, farida ta ci mata mutunci, amma hakan bai sanya ta daina sawa ba.

Hijjabin jikin nata ya sha jiki ya koÉ—e, sai dai kasancewar a goge yake, muninsa ya ragu.

Tana mopping noor na biye da ita suna hira, ta saki jiki tana biyewa noor, suna shiririta.

Ƙamshin turaren da ya cika falon ne, ya sanya ummi ɗaga kai, aikuwa tayi tozali da intee ta fito, sai taku take ɗaya-ɗaya.

Ta sha doguwar rigar abaya, ƙamshin kansa ummi ta kasa tantance wane iri inteesar take yi.

Tayi light make up, sai wani yatsuna fuska take yi.

Ummi a ranta ta ce "Tubarkallah masha Allah, kyau yana in da yake" ba iya kyan da inteesar tayi ne ya burge ummi ba, doguwar rigar jikinta ma ta tafi da ita, ta ji ina ma ita ma tana da ita ta saka, taga ya zata yi a ciki, dogayen riguna irin haka suna burgeta".

"Ke! Kalli gabanta kar ki kama mini kurwar Æ´a" farida tayi maganar cikin tsawa.

ÆŠan zabura ummi tayi, ta cigaba da aikin gabanta.

Kausar kuwa ta kwashe da dariya, yadda ummin ta É—an shagala da kallon yayarta kamar shashasha.

Farida ta yi murmushi ta ce "Farar mace....

Caraf kausar ta ce "Alkyabbar mata"

"Farar mace kalar kyau, kalar babban gida da manyan motoci, kalar hutu da jin daÉ—i farar mace mowar mata"

Inteesar kamar kanta ya fashe, saboda kirarin da mamanta ke yi mata.

Ta dubi ummi ta ce "Baƙar mace borar gida".

Farida ta amsa da "Idan ta samu mijin ba"

"Idan ba ta samu ba kuma ta dauwwama Æ´ar wanke-wanke"

Ummi tayi burus, ta cigaba da hirarta da noor, tana jin zuciyarta na wani irin zafi.

Intee ta yamutsa fuska ta ce "Maama bari na je, ya kirani a waya, ya zo".

"To shikenan, a kula sosai, a iya karairaya da jan hankali"

"Kar ki damu maama, ammm ummi kin kammala girkin da na saki?"

"Na gama"

"Ok, ki shirya mini komai a tray, in the next few minutes ki kawo mana"

Kallon ƙasan ido ummi tayi mata, ta yi mata girkin tarar saurayi, kuma ita za ta kai musu.

Tayi ajiyar zuciya, tare da É—an girgiza kanta.

Farida ta ce "Ke ummi in tambayeki mana"

Ummi ta É—ago tana kallonta.

"Wai dan Allah ina babarki ne?"

Ummi ta É—an yi jimm, dan ba ta zaci wannan tambayar ba.

"Ban san in da take ba"

"Kamar yaya baki san in da take ba?"

Ummi ta ce "Ai tun ranar da ta tafi, Iya ta hana a tafi da ni, ban sake ganinta ba, sau kusan uku ƴan uwanta na zuwa su tafi da ni, amma ta ƙi bayar da ni".

"Kuma saboda rashin lissafi, ba ta sake neman in da ki ke ba, daga ita har ƴan uwanta, yau shekarar ki nawa a gidan nan, ko kare daga dangin majaifiyarki ba wanda ya nemi in da ki ke, wace irin uwa ce wannan? Ko suma ba sa buƙatar ki ne, an rasa mai riƙe ki, aka liƙa mana, anya babu lauje cikin naɗi a game da ke, ta hanyar aure aka same ki kowa yake gudunki?"

Tuni idon ummi ya fara tara hawaye, cikin ƙoƙarin kare mahaifiyarta ta ce "Ai an ce ba ta da lafiya, tun da aka ƙwace ni, ta haihu ɗan babu rai, ta samu matsalar ƙwaƙwalwa"

"Mahaukaciya ce kenan?" Kausar ta faÉ—a kai tsaye.

Farida ta ce "To ai mahaukaci ya san É—an sa, jahilci kawai da rashin sanin ciwon kai, idan ita ba ta da hankali, Æ´an uwanta fa?"

Ummi ta yi shiru, ta kasa magana.

Farida ta shigo falon a fusace ta ce "Wai ke ummi me ki ke taƙama da shi ne? Cewa fa na yi ki kawo mana abinci, amma dan wulaƙanci kin shanya ni, bana son rashin mutunci"

Ummi ta jingine mopper ba tare da ta ce komai ba, ta je ta É—auki tray, ta kai wa saurayin intee.
Kallo É—aya ummi ta yi masa ta sunkuyar da kai, gaba É—aya bai yi kalar mutane masu É—a'a ba.

Tunanin abun da farida ta faɗa ya ɗarsu a ran ummi, idan an ce mamanta ta samu matsalar ƙwaƙwalwa, to ƴan uwanta fa, yakamata ace sun nemeta, ta san da a hannunsu take, ba za su wahalar da ita sosai ba.

Sakawa tayi a ranta a wannan karon idan kawu ya zo gida, za ta tuna masa alƙawarin da yayi mata na binciko maata in da mamanta take, dan ita ba ta taɓa jin ko sunan garinsu wani ya faɗa ba.

***
Can gida gagarawa kuwa, an samu da ƙyar da siɗin goshi, su hindu sun karɓi jaririya, babanta ya ce idan ta yi arba'in, su zo su kawo kuɗin aure, kuma yadda ake auren budurwa komai da komai, haka za a haɗo mata, kuma shayarwa da hindu, za ta yi, sai an biyata kuɗin shayarwa ko su dawo musu da jaririyar.

Kan su dawo gida, sai da babanta ya caje su kuÉ—i masu yawa, sannan suka dawo, suka sanar da Iya abun da babanta ya faÉ—a.

Iya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin matsiyatam mutane ne? Sai an yi mata komai kamar auren budurwa ba ta riga ta haihu ba, har wani kuɗin shyarwa suke nema, a gidan ubanwa aka taɓa haka, ai da an dawo da ƴar a din ga bata nonon akuya".

"A'a iya, a samu a lallaɓa mu rabu da mutanen nan lafiya, kowa ya ɗebo da zafi ai bakinsa, gobe ba ya ƙara ba".

Da labari ya iske idiris kuwa, masifa ya fara yi, yana baloƙoƙon shi fa ba ya son Hindu, ban da zalunci yarinyar da har haihuwa ta yi, tayaya za a ce wai ayi mata kaya kamar budurwa, saboda son zuciya.

Cikin tsananin fusata mahaifinsa ya ce "Rufe mini baki, ko na turmushe ka a wurin, mara mutunci, muna zaman zamanmu ka janyo mana masifa, ka sanya kowa a tashin hankali, kuma wallahi ko ka so, ko ka ƙi sai ka auri yarinyar nan, ka ƙarata can bayan auren" yayi masa ta tas ya tafi ya bar shi.

Magaji yayi murmushi ya ce "Allah sarki ummi, baiwar Allah yanzu idan na ce hakkinta ne ya fara bibiyarku, sai ace ƙarya ne a hayayyaƙo mini, da ka yi haƙuri da ummi, ka nema mata magani tsaf zata warke ku zauna lafiya, amma ka din ga muzanta ta, kana yamaɗiɗi da ita a kan larurar da ta same ta, har abokan ka suna ce maka angon ɗaɗɗoya saboda zunzurutun wulaƙanci da tozarci, ka saketa bayan ka gama azabtar da ita, saboda ka na taƙama da kai ɗan iska ne.
Kai ma gashi Allah ya tozarta ka, gara nata tarihi zai iya shafe shi, naka kuwa har gaban abada ba zai goge ba, kuma kaÉ—an ka gani, ba dai bariki ba sai ma ka auro wannan É—in, zaka san ka yi asarar mace".
Duk wannan faÉ—an da magaji yake yi masa, bai iya cewa komai ba, saboda ya san ba shi da gaskiya, kuma yanzu yana cikin tashin hankali da tunanin menene mafita.

***
Ummi tana ta dakon zuwan kawu, tare da fatan Ubangiji Allah ya sanya ya samo in da mama take, gara ta tattara ta koma can wurinta, dan da ta san in da take da ta daÉ—e da barin gidan nan, ko bola take bi za ta din ga bin ta.

Sai da aka shafe kusan sati uku, sannan dr. Ya zo gida, bayan yayi kwana biyu ya É—an nutsu ya huta, ummi ta same shi shikaÉ—ai a falo, ta gaishe ta samu wuri ta zauna.

"Ummana, ya aka yi ne?"

"Dama ba wani abu bane kawu, dama tambayarka zan yi ko ka gano in da maman take?" Tayi maganar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Ya É—an yi shiru yana nazarin ta, sannan ya ce "Akwai matsala ne?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Na san ba zaki faɗa ba dama, rabonki da yi mini wannan zancen an kwana biyu, na san a takure ki ke ummi, amma ki yi haƙuri, ina nan ina ta ƙoƙari a kai, ba yadda ban yi da Iya ba, ta ce mini ita ba ta sani ba.
Ƙanin babanmu da yayi masa walicci ma ya rasu, su ilyasu sun ce basu san sunan garin ba, su dai kawai an zo da mota an kai su, na san faɗa kawai suke yi, Iya ce ta hana su faɗa.
Amma ina nan ina ta bincike, ina da hotunanta biyu, da aka yi mana bayan bikin da na je gida, ina ta bincikawa, na samo sunan garin, ainihin yankin da take a garin ne ban sani ba, ana ta bincikawa ummi, ina sane ban manta ba, ki cigaba da addu'a da kula da karatunki, komai zai warware in sha Allah".

Ummi ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi".

Ya ce "Amin ummana, baki ce Allah ya yi mini albarka ba"

Rufe fuska ummi tayi tana murmushi.

Ya ɗora da cewa "Kwanaki an ce mini ɗan uwan mamanki ya zo ganinki, Iya taƙi gaya masa in da ki ke, ta ci mutuncin sa ya tafi. Amma dai in sha Allah ina nan ina ƙoƙari a kai".

"To kawu na gode"

Ta tashi ta nufi ɗakinta, tana sake jinjina ƙiyayyar da Iya take yi wa mahaifiyarta da ƴan uwanta.

Kasancewar maryam gaba take da ummi dama, dan haka ta riga ummi candy, tun kan ta yi candy aka kawo kuÉ—in aurenta, dan haka an yi candy babu daÉ—ewa bikin ya tinkaro.
Chapter 43 · 0% Book details