Sashe 13
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai an ce baba ba zai dawo ba, ya mutu yana cikin kabari".
"Haka ne mamana, kina yi masa addu'a ko?" Ta gyaÉ—a kai alamar eh.
"Yanzu me ki ke son na saya miki?"
"Littafi" ta bashi amsa.
"Littafin makaranta?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya ce "To shikenan, zan sai miki in sayo miki kifi ko nama, wanne zaki ci?"
"Nama" ta faÉ—a tana murmushi.
Yayi mata murmushi shi ma, ya ce "To bari su sallame mu, sai na saya miki mu tafi gida"
Har ummi ta ɗan murmuro, ya saya mata tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san baƙar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya riƙe ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can gidansa, faɗa za suyi da Fauziyya matarsa, dan ya san ba zata karɓi ummi ba.
Gashi shi bai san a ina mahaifiyarta take a Maiduguri ba, dan lokacin da balarabe yayi aure, yana kudu karatu.
A mota ya sanya ummi ta ci, har ta ƙoshi, wani irin daɗi take ji, yau ta ci kayan daɗi, wataran tana kallo ake kawo wa Iya, bata sammata.
A ƙofar gidan yayi parking, ya buɗewa ummi ta fito, ya riƙo ledar maganinta, ya riƙe hannunta suka shiga cikin gidan.
"Baƙar randa, baƙin zunubi, an dawo jinsinmu na maza" Alhassan ya faɗa yana ƙyaƙyata dariya".
Yahaya ya tsaya cak, ya kalle shi ya ce "Alhassan, wa ka ke cewa baƙin zunubi? Ummi ba ƙanwarka ba ce ba? Dan me zaku din ga aibata ta?"
Alhassan ya yi shiru ya sunkuyar da kai.
"Kai da ubanka na halitta, da zai halittoka da wannan kunnuwan kan kamar zomo na zikiri, ga ƙaton kai kamar marmara?"
Ya girgiza kai alamar a'a, nan yayi ta yi masa faɗa, ya shiga cikin gida nan ma ya ɗora, tare da yi wa iya ƙorafi a kan lallai ta sanya ido, a daina ci wa ummi zarafi, idan ba haka ba, zata dashi ba ta karsashi a cikin al'umma, saboda gudun kar a aibanta halittarta.
Jin sa kawai Iya take yi, amma ba dan ta ji zata iya hana wani aibata ummi ba, dan ita ma aibata tan take yi.
Yahaya ya kawo kuɗi ja bawa iya nata, kamar yadda ya saba yi mata alkhairi, ya sanya a ka kira masa magaji, ya bashi dubu goma ya ce "Ga dubu goma, dan Allah duk abun da Yarinyar nan take buƙata, ko na rashin lafiya, ko na makaranta ka cira ka saya mata, idan da damuwa zan rubuta lambar wayata, a kira ni a sanar da ni duk abun da take buƙata, zan biya.
Zumunci bai ce haka ba, mahaifinta ya rasu, an rabata da mahaifiyarta, kuma aƙi tsayawa a kula da ita, dan Allah a kula da marainiya".
Hashim ya ce "Ina sha Allah kawu, za ayi duk abun da ya dace" ya dubi ummi ya ce "Sannu ummi"
Ta ce "Yauwwa"
Yahaya ya miƙe ya ce "To iya, sai wani lokacin kuma, ayi ta haƙuri, Allah ya rufa mana asiri"
Iya ta kwaɓe baki ta amsa da Amin.
Da sauri ummi ta riƙe rigarsa ta ce "Baba yaushe zaka dawo?"
"Da wuri in sha Allah ummi".
"To ka ce ina gaishe da mama"
Ya kalli iya, iya ta kawar da kanta gefe, ya ce "Iya yakamata a sanya lokaci a kaita ta ga mahaifiyarta, bai kamata idan ma wani abu ne a tsakanin ku da mahaifiyarta ya shafe ta ba"
Iya ba dan ɗan abun duniyar da ya bata ba, da babu abun da zai hana, ta ɗura masa ashar. Sai dai ta yi masa shiru, ya ƙaraci maganarsa ya tafi.
Hashim ya tafi raka shi, suna tafe yana sake jaddada masa, dan Allah a kula da ummi, babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarrabe shi da irin abun da ya jarrabe ta.
Suka ɗan yi hira a kan karatun Hashim, yake gaya masa ai yayi jamb, ya ce duk yadda ake ciki, idan yana buƙatar wani taimako yayi masa magana.
Suka yi sallama ya dawo sashin Iya, sai dai fa iya nata jibgar ummi da kara, Idris na tsaye yana kallonsu.
Da sauri ya ƙarasa ya ƙwace ummi, ya ce "Iya daga asibiti fa aka dawo da yarinyar nan"
"A'a daga mutuware aka dawo da ita, duk yadda nake ƙoƙari a kan yarinyar nan, bata da wani buri da ya wuce ta tozarta ni, ta nunawa duniya azabtar da ita nake yi"
"To yanzu iya me tayi miki?"
"Ban sani ba, tun da makaho ne kai, baka gani, munafukar yarinya, wallahi duk ranar da wani ya kuma zuwa gidan nan, ki ka yi masa zancen uwarki, sai mai shirin tafiya kabari ya fiki kwanciyar hankali, sai na casa ki, shegiya mai idon munafukai"
Ummi ta cukuikuye rigar hashim tana kuka.
Iya ta kalli Hashim ta ce "Kai ma É—aya munafukin, bani kuÉ—in da ya baka, ai ba ita kaÉ—ai ce Æ´a a gidan ba, kuma idan bayarwar ne, ai ni yakamata ya bawa"
Cikin takaici ya ce "Amma iya...
"Rufe mini baki, ka bani na ce kan na ɓata maka rai" ya ciro kuɗin ya ajiye mata, ya fice.
Ummi da sauri ita ma ta fita, jikinta na ciwo, ga zazzaɓi na sake son rufe ta.
Ta koma ƙofar gida, ta samu in da rana take da saura, ɗumin yana ratsata.
Auwwalu ya taho da tawagar abokansa, har ya wuce ta ya dawo ya ce "Yara baƙar randa ta koma baƙin namiji, aski aka yi mata fa"
ÆŠaya daga cikin yaran ya ce "Haba dai"
Ya ce "Bari ku ga" ya tunkari ummi, yana zuwa ya fara ƙoƙarin ja mata hijjabi, ta rirriƙe hijjabin ta fara kuka.
Ƙarasawa yaran suka yi, suka taya shi, kasancewar maza ne, gashi ba ta da ƙwari ga rashin lafiya, suka kayar da ita, suka yage hijjabin.
Ta saka hannu bibbiyu ta rufe kanta, tana kiran mama.
Saboda mugunta irin ta yara, daga haka suka din ga kai mata duka a ka, wai sun ci ladan aski.
Suka tuburbuɗata a cikin ƙasa, duk ta kurje jikinta, kan da aka yi wa dressing, duk suka cika shi da ƙasa.
Mariya daga alhinin mutuwar miji da rabuwa da Ummi, mariya ta zarce da damuwa, ba ta hira ba ta walwala, sai dai kullum cikin wuni a É—aki, duk lokacin da ta kwanta, ba ta da wani aiki sai mafarkin ummi, da kuma marigayin mijinta.
Asibiti da maryam ke kaita awo, suka ce da zarar ta fara naƙuda, a kai ta asibiti ta haihu a can, saboda hawan da jininta yayi.
Sai dai kusan kwanaki uku kenan, tana jin ciwo, kuma sai ta yi ta mafarkin gata ta haifi ummi tan jaririya, amma tayi shiru da bakinta, taƙi faɗa.
Mama ta shiga ɗakin, da niyyar tashin mariya ta yi salla, ta tarar da ita tana jijjiga, sai datse harshenta take yi, tana mimmiƙewa ga kuma haɗe da jini na fita daga bakinta.
Ayshercool
08081012143
             *CUTARWA!*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
arewabooks ayshercool7724
Watpad ayshercool7724
Subscribe my YouTube channel https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
P7
A guje mama ta koma tsakar gida, tana ƙwalawa malam kira, a kan ya zo ya ga abun da mariya take yi.
Suka dawo a tare, ya tarar da yadda jikinta yake ta rawa tana jijjiga, ya fita da sauri, aka nemo maƙwabcin su, kasancewar yana da abun hawa, aka saka mariya a mota suka tafi asibiti.
Can kuma hashim ne ya fito zai fita titi, ya hango yara sun yi dandazo, har zai wuce ya hango ƙafar ummi, ya ƙarasa da sauri, ya tarar da ita a kwance, yara sun yage mata hajjabi, ta sanya hannayenta biyu ta rufe kanta, sai kuka take yi.
Wani irin baƙin ciki ya turnuƙe masa zuciya, ya rasa dalilin da ya sanya yara suka tsani ummi haka, kodayeke iyayensu suka gani suna yi, da sun tsawatar musu da tarbiyantar da su a kan girmama halittar ɗan Adam komai muninta, da ba su yi mata wani abun ba.
Kai tsaye ya je ya tarwatsa yaran, yayi nasarar kama auwwalu, ya din ga kifa masa mari, yana ball da shi, yayi masa dukan tsiya, sannan ya ɗaukko ummi ya shiga da ita gida.
Gaban iya ne ya faɗi ganin yadda ya shigo da ummi, ta miƙe tana faɗin lafiya?.
"Wallahi auwwalu ne ya tara yara, suka cire mata hijjabi suka yi ta dukanta a waje"
"Saboda iskanci, me tayi masa?"
"Oho masa"
"Kema uban waye ya ce ki fita?" Tayi maganar tana kallon ummi, da take ta zirarar da hawaye.
Ya ce "Dan Allah iya ki yi haƙuri, a jigace take, jikinta zafi rau da zazzaɓi"
Ya karkaɗe mata ƙasar nan, ya samu ruwa ya din ga shashshafa mata a jikinta, ya kaita ɗakin gwaggo ya kwantar da ita.
Iya kuwa mita take tana "Na rasa wannan baƙin jini na yarinyar nan, ƴa sai ka ce mujiya, ƴan uwanki yara ma gudunki suke yi, kodayeke ai dole a guje ki, wannan munin gaba ɗaya kalarki ba irin ta mutane ba" Hashim bai kula iya ba ya fice, saboda haushinta da yake ji, dan ya fara tsinkewa da lamarin son zuciyarta, gashi babu wanda zai iya tarar ta ya gaya mata gaskiya kowa tsoronta yake ji.
Duk yadda likitoci suka yi ƙoƙarin ceto ran mariya da yaronta, Allah bai yi ba, yaron ya zo babu rai, kuma alamu sun nuna ya kwan biyu da mutuwa a cikin ta, saboda yadda fatarsa ta fara marmasowa.
Sai dai har kusan kwana biyu da haihuwar ta, an kasa samo kanta yadda yakamata, da magani ya sake ta sai jini ya sake hawa.
Sai suka shafe sati uku a asibiti, sannan aka sallame su, suka koma gida, sai dai abu idan ba ya zama dole ba, ba ta magana.