← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 134

Sashe 40

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shashshafa turare, tafin hannunta har ɗaukar ido yake yi, saboda tafin hannunta fari ne ƙal, kamar mata jini a jiki, kuma aka ɗora mata jan lalle a kai.

Ta ɗauki ƴar ƙaramar jakarta ta fito, Abdul ya ce "Inyee ka ga amaren sauka"

Kawu yahaya ya dube ta cikin fara'a ya ce "Congratulations dear, Ubangiji Allah ya sanyawa karatunki albarka, ya ƙara hasken makaranta" ta risuna ta ce "Amin kawu, na gode sosai da sosai"

Ya kalli farida da Æ´an matanta da suke ta sabgoginsu, kamar ba su san da zaman su a falon ba ya ce "To mu mun tafi wurin saukar"

"Allah ya tsare" ta faÉ—a a yatsune.

Kawu yahaya yaji babu daÉ—i, da yaransa ko mutum É—aya babu wanda yayi saukar nan, idan baya nan sai sun ga dama suke zuwa makaranta, dan kuwa farida wurin koyon kwalliya ma ta sama musu, maimakon zuwa makarantar.

Ummi gaba ɗaya bakinta yaƙi rufuwa, kaf a ƴan saukar ita ce ƙarama, danma tana da jiki ne, dan ko Maryam shekara biyu ta bata, itakaɗai ce mai shekaru sha shida a cikinsu, maryam na da sha takwas.

Aka gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan aka fara raba musu alluna.

Ana bata nata ta nufi rumfar iyaye maza, har da gudu, wurin kawu ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa tana cewa "Kawu ka ga"

Ya karɓi allon yana murmushi ya shafa kanta ya ce
"Allah ya sanya albarka ummana"

"Amin kawu na gode" tayi maganar cikin tsantsar farinciki.

Abdul ya ce "Rufe bakin mana"

Ta kalleshi ta ce "Ta ina ka san bakina a buɗe yake a cikin niƙab".

"Yadda ki ke magana ne ya sa na gane"

Ta ce "Bari Yaya Abdul, Alqur'ani da daÉ—i wallahi".

"Wannan gaskiya ne ummana, kalli baƙin ki na waccan rumfar" ummi ta waiwaya ta ɗaga kai.

Wa zata gani? Yaya Magaji da auwwal, har da su Alhassan.

Maimakon ta yi murna sai gabanta ya faɗi, ta kasa magana, dan fatanta Allah ya sa babu Idris suka zo, dan bata ƙaunar ganinsa.

Sunanta aka din ga kira a speaker, ta zo ta karɓi kyautarta ta ɗaliba mai hazaƙa.

A hankali ta tashi ta nufi in da ake kiranta, tafiya take cikin nutsuwa, shugaban makarantar ya ce "Ƙaramar su babbar su, Salma Muhammad Bashir, kun ganta nan duk ita ce ƙarama a ƴan sauka, amma babu ɗalibar da ta kai ta cin maki lokacin screening"

Ummi ta karɓi kyaututtuka daban-daban, na hazaƙa, ladabi da biyayya da sauransu.

Mamin su maryam ummi ta hango, ta tafi wurin da take, dan jan lallen da aka yi mata ma, gidan su maryam ta je, mamin ce ta biya.

Mamin ta rungume ta tana faÉ—in "Allah yayi albarka ummi, Allah ya sanya wa karatunku albarka"

Ta risuna ta ce "Amin ya Allah"

Sau ɗaya ya ɗaga kai ya kalleta, ya lura da yadda ko iya haɗa ido da mamin ba ta yi, saboda tsananin tarbiyya da girmama manya, ya so ta ɗaga niƙabin ya ga ainihin fuskarta.

Ya dubi Maryam ya ce "Ke ba uban da aka baki? ba na ƙoƙarin, babu na ɗa'ar" yayi maganar yana sake gyara zaman face mask ɗin sa.

Cike da tsiwa Maryam ta ce "Ina ruwanka da ni? Ba a bani ɗin ba sai ka ƙwace allon saukar ma gaba ɗaya, mami ki rabani da shi wallahi, ai da yake ma ba gayyatarka na yi ba, waye ya ce ka zo?"

"Rufen baki kan na ɓarar da ke a wurin nan"

Ummi dai murmushi kawai take yi, duk ta san yayyen Maryam, wannan ne dai bata sani ba, kuma da alama maryam É—in ta raina shi.

Aka tashi daga filin sauka, su yaya magaji suka nufo su, "Ummi masha Allah, kin ga yadda ki ka girma?" Magaji Yayi maganar yana kallon ta.

Alhassan ya ce "Ummi har kin yi sauka anya ba zuƙu ba ce ba?".

Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai makarantar nan ba a saukar zuƙu"

Suka rankaya zuwa gida, suna komawa gida ta tarar da Iya, sai da ta É—an ci burki, domin kuwa ba ta zaci Iyan za ta zo ba.

Ta ɓoye mamakinta ta ce "Iya sannu da zuwa, dama zaki zo?"

Ta harari ummi ta ce "Eh, da ki ka ce ke ba zaki zo in da nake ba, kar na yanka ki na cinye ko?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a makaranta ce take hanani zuwa, ya gida ya kowa da kowa?".

A ciki Iya ta amsa mata da lafiya lau.

Dai-dai gwargwado kawu ya yi wa ummi ƙoƙari, dan naman kasuwa ya sayo fal, ya bata tayi girkin da zata rarrabawa mutane da ƙawayenta.

Ita ummi ma kasancewar ba ta da ƙawaye, sai maƙwabta ta babbawa, sai su Iya da suka zo.

Sam farida ba ta bi ta kan Iya ba, ummi ce take ta É—awainiya da su, suna ta hirar makaranta da su magaji, sai dai ko da wasa, ba ta nuna musu tana shan wahala a gidan ba ko kaÉ—an.

Kawu yahaya ya ji daɗin yadda ummi ta samu sakewa yau cikin ƴan uwa, tana hira ba kamar da da kullum a rakuɓe take ba.

Iya kuwa ba dalilin saukar ummi ne ya kawota ba, balli ne ya tashi, Idris ya mayar da hindu tamkar matar da ya aura, tun bata saba ba har suka saba da sheƙe ayarsu.
Kwatsam ciki ya bayyana a jikin hindu, suka rasa yadda za su yi da cikin, har sai da iyayen hindun suka farga.
Dan haka zance ya fasu a gari, sai faÉ—uwa ta zo dai-dai da zama, domin kuwa iyayen hindu sun ce sai ya auri hindu, shi kuma ya ce ba ya son ta.
Dan kuwa zance ya fara fasuwa, an fara zunÉ—ensu a garin.
Baban hindun kuma ya dage ba za a zubar da ciki ba, sai an haifi wannan ɗa ya riƙe, kuma sai ya aureta.
shiyasa Iya ta lallaɓo wai kawu yahaya ya ɗauke shi ya sama masa sana'a a nan Kano, a mayar da aurensa da ummi!!!

Iya a É—akin kawu yahaya ta same shi, ta kora masa wannan jawabin.

Yayi ƙuri da ido yana kallon Iya, har ta gama jawabinta.

Kasancewar ummi na wurin, gabanta yayi wata irin mummunar faÉ—uwa, kawu yahaya ya kalli Iya ya ce "Amincewar ummi zaki nema, ni ba zan yanke mata hukunci ba, abun da take so shi nake so".

"Zancen banza kenan, wane irin sai ta yarda ko ba ta yarda ba? Ba ɗan uwanta bane ba, rufin asirinmu ba nata bane ba, idan shi ma ya baro garin, suka neme shi suka rasa ba shikenan ba, asiri ya rufu, ai rufa masa asiri za ta yi,  ai umarni nake bayarwa ba shawara ba, dauɗar gora ai ciki ka sha ta!"

Ayshercool
08081012143.
WHAT'S APP ONLY PLEASE 🙏

18

Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshsheƙar kuka take yi, dan kuwa da ace ta koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa.

Iya cikin masifa ta ce "To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ƙone ƙurmus, har wani zaɓi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba".

Kawu yahaya ya ce "Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni".

"Ka ga ni kar ka yi mini wa'azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo É—in, sai a ja masa kunne"

Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshsheƙar kuka ya ce "Ummana, jeki ɗaki abunki kin kwaso gajiyar sauka" ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi ɗakinta tana kuka, tare da adduo'i kala-kala a zuciyarta, tana fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faɗa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko maƙiyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris.

Noor ta bita É—akin tana kiran sunanta.

Kawu ya kalli Iya ya ce "Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba É—aya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci É—an wani ba, yadda ya yi wa Æ´ar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba.
Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauÉ—ar gorar ba, sai ummi?
Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan riƙe ƙato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ƙauye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi haƙuri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke ɗawainiya da shi".

Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce "Haka ka ce?"

"Ba faɗa na yi dan na ɓata miki rai ba, amma gaskiya ce" Iya ta yi ƙwafa ta ce "Shikenan na tabattar da uwarka ce ba zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku ɗaya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba".
Chapter 40 · 0% Book details