← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 134

Sashe 9

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mariya ta wani fannin ta ji daɗi zasu koma gida, wani ɓangaren wata irin kewar ɗakinta da mai ɗakik wato baban ummi, ta sake mamaye mata zuciya, har take jin anya ba za ta ce a bar ta a ɗakin nan ba, za ta cigaba da haƙuri da ita, kawai dan ya din ga gurbin da bashir yake dabdala.

A daren Maryam ta taimaka mata, ta harhaɗa kayanta, abun da zasu buƙata, Maryam ta ce daga baya azo a sayar da sauran kayanta, dan ba zasu iya dakon kaya zuwa Maiduguri ba.

Da sassafe maryam ta yi wa ummi wanka, suka yi wanka suka karya, ummi tana murna zasu tafi su bar gidan nan, tana fatan Allah ya sa idan sun je can babu yara masu tsokanar ta, ko dukanta.

Sun fito maryam na ce mata, ta yi sallama da mutanen gidan, ta nemi afuwarsu, Iya na tsaye tana kallon su.

Iya ya ce "Ummi zo mana mu yi sallama". Saroro ummi tayi tana kallon iya, ta É—aga kai ta kalli mariya, mariya ta ce "Je ki Iya na kira"

Ummi ta tafi sannu a hankali, ta ƙarasa gaban iya.

Caraf iya ta sanya hannu ta riƙe hannun ummi, sannan ta kalli mariya ta ce "To, Allah ya raka taki gona, ummi dai ba da ita ki ka zo ba, kin san wannan, dan haka a sauka lafiya"

Mariya tayi turus tana kallon iya, dan ganin abun take kamar almara.

Maryam ta ce "Ban gane ba, yarinyar da ki ka ce ba taku ba ce ba"

"Ɓacin rai ne ya sanya ni faɗar hakan, ba zan bayar da ita aje ayi mata gurguwar tarbiyya ba, ta tashi tana sa'insa da manya ba, dan haka ni zan riƙe ummi, ita kaɗai ya haifa, na rasa ɗa na, ina buƙatar ganin jinin sa a gabana".

Cikin kuka mariya ta ce "Dan martabar Allah kar ki yi mini haka iya, ba zan iya jure zama babu ummi a kusa da ni ba, idan ma tafiyar ce na fasa, dan Allah ki bani Æ´a ta".

"A a, a kan me zan hana ki tafiya, haifarki na yi, na rasa É—a na balle wata ke, Allah ya raka taki gona"

Ƙoƙarin ƙwacewa ummi ta fara yi, tana kiran sunan mama.

"Nutsu dan ubanki" Iya tayi mata tsawa.

Yayansu mariya ya shigo, yana cewa su fito kar su yi rana, amma ya tarar da sabuwar dambarwa.

Juyin duniya, Iya ta ce ba zata bayar da ummi ba.

Mariya ta zube a kan gwiwoyinta, tana gursheƙen kuka, a kan iya ta bata ƴar ta, ta din ga cewa mutanen da suka taru, su saka baki iya ta bata ƴar ta, amma matar nan mirsisi taƙi.

Ummi na kuka mariya na kuka, yayan su ya hasala ya kalli mariya ya ce "Ke tashi mu tafi, in dai Æ´a ce su cinye, tashi mu tafi"

"Yaya ka taimake ni, ba zan iya rayuwa babu ummi ba, dan Allah kar a rabani da ƴa ta, dan girman Allah ku yi mini rai, da wanne zan ji, na rasa mijina ƴar ma a ƙwace mini? Dan Allah ku bani ummina"

"Sai dai kiyi kukan jini kuwa"

A fusace ya daka wa mariya tsawa, ya ce ta wuce su tafi.

Iya tayi tsaki ta ce "Aikin banza, ban da rashin tarbiyya, wai a kan Æ´ar fari take wannan abun"

Idris ya shigo, Iya ta ce "Kai kuma mun yi magana ka ɓata mini lokaci, ɗauke ta ka tafi da ita in da na ce maka"

Ya ƙarasa babu walwala, zai danƙi hannun ummi, ummi ya rirriƙe Iya, tana wani irin kuka, dan a rayuwarta, ta tsani ko haɗa hanya su yi da idris, ta ƙarfin tsiya ya danƙi ummi, tana kuka tana kiran mama, mariya ta bi bayansu da gudu tana kiran "Ka zo ka bani ƴa ta, ku bani ƴa ta ba ƙaunar ta ku ke yi ba, ku bani ƴa ta. Yaya maryam ki karɓo mini ƴa ta, ke shaida ce ba son ummi suke yi ba"

Cikin tausaya maryam ta ce "Zaki kashe kanki ne? In dai ummi ce Allah zai kula miki da ita" shiru ta yi tana kallon maryam, ana gobe bashir zai tafi yake cewa Allah ga Æ´a ta da mata ta Allah ka kula mini da su.

"Wuce mu tafi, su je su cinye ta, kema kina da masu sonki" auwwalu ne ya bi bayansu da warin takalmin mariya, dan takalmi ɗaya ne a ƙafarta, hawaye ne kawai yake zuba daga idonta, can ƙarshen hanya ta hango ummi tana ɗaga mata hannu tana kiran mama cikin hawaye!

Iya ta ce "Ba dai ke tsagera ba, daga ke har yayar taki dai-dai nake da ku, ummi ce dai tana hannuna, ba wani uban gado da za a raba, a baki ku cinye, gayyar tsiya arna a idi".

*Page ɗin nan sadaukarwa ne, ga duk matar da ta rasa mijinta ko aurenta, kuma aka zo aka rabata da ƴaƴanta, we know is difficult to endure, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri 🙏 Allah ya shiga lamarinku, ya kula muku da yaranku*

Ayshercool
08081012143
       *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
What's app 08081012143

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

*BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_

Tsari👯🏻‍♀️
Duk page É—aya 200
Duka littafin kuma 600
Shafi biyar a littafi É—aya 1000
A littafai uku kuma 3000
Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼

P5

Har suka je tasha, jan ƙafa kawai mariya take yi, dan bata gane komai, hankalinta yana kan ummi, wace irin rayuwa ummi za ta yi a wannan gidan? Tana nan ma a ya aka cika, balle yanzu da babu idonta, kuma ya zamana ba ayi rabuwar arziki ba.

"Allah ka kula mini da ƴa ta, Allah kar ka sanya ƴa ta ta lalace, Ubangiji Allah ka duba mini ita, ka tsare mini ita, Allah kai ka san dalilin da ya sanya, ka karɓi mahaifinta ka rabani da ita, Allah ka kula mini da ita. Haka ta din ga wannan addu'ar, jin abubuwan take tamkar a cikin nannauyan bacci, da take fatan ta farka.

Har suka shiga mota suka kama hanya, duk wata nasiha da maryam ke yi mata, ba ji take ba, balle ta fahimta.

Mariya ji take tamkar ta sauka daga cikin motar nan, ta koma ta rayu da ummi, ta san ummi wahala kawai za ta sha, dan iya ba ƙaunarta take yi ba.
Tunawa da tayi da cin zarafin da aka yi wa ummi, ya sake karya mata gwiwa, ta sake fashewa da kuka mai sauti.

"Idan ba zaki rufe mana baki ba, a tsaya ki sauka ki koma, ki je duk uban da za su yi miki, su yi miki, sai ka ce a kanki aka fara haihuwa, duk cin zarafin da suka yi miki bai isheki ba, ba dai ƴa ba ce su je su cinye ta, ai ta su ce da ma, dangin uba su ke da ɗa" tun da ya fara yi mata masifar ƴan cikin motar suka yi tsit, sai da ya gama ake bashi haƙuri.

Maryam ta san abun da mariya ke ji, dan haka ta rungume ta tana rarrashinta, haka tana ji tana gani ta bar garin da duka goma da ashirin, ga rashin miji ga rashin Æ´a.

Ummi kuwa sai can daf da magariba aka saka yara suka rakata gida, dan can gidan wata Æ´ar uwarta ta sanya aka kai ta.

Ta ci kuka ta ƙoshi, sai ajiyar zuciya take yi, ana zuwa gidan da sauri ta shiga ta nufi ƙofar ɗakinsu, sai dai ta tarar da shi da ƙaton kwaɗon da su mariya suka rufe ɗakin da shi.

Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar ɗakin, ta cigaba da rera kuka.

Babu wanda ya saurareta, balle ya kula da ita ya rarrasheta.

Sa'adatu ce tayi sallama, ta kawo wa iya tuwon dare.

Ta ajiye mata suka taɓa hira, ta tashi fito, tana daf da shiga sashinta, ta ji ana bin ta a baya, ta tsaya ta waiwayo taga ummi.

"Ke, lafiya ki ke bina?"

"Dan Allah ina mama? Haryanzu ba ta dawo ba, ta buÉ—e mana É—aki in yi salla, sanyi nake ji"

Sa'adatu ta yi shiru tana kallon ummi, sam ba ta ga dalilin da zai sanya iya raba mariya da ƴar ta ba, ta san iya ba iya riƙe ta zata yi ba, saboda tsabar mugunta da rashin imani.

"Ummi babarki ba zata dawo ba, ki tafi wurin iya ki je ki kwanta, gari da sanyi"

"Ita ma maman ta mutu? Ba zata dawo ba kamar baba?"

"Ba mutuwa tayi ba, nan kusa dai ba zata dawo ba, ki yi addu'a Allah ya sanya ta dawo ta tafi da ke, can in da aka kai ki kin ci abinci?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "Mama ta hana ni cin abinci a gidan mutane"

Sa'adatu ta ce "Kenan wuni ki ka yi baki ci abinci ba, tafi na kai wa iya abinci, ki je ta zuba miki" ummi ta ce "To"

Ta juya jikinta a sanyaye, ta koma sashinsu, ta zauna a ƙofar ɗakin su, tana kallon ƙofar ɗakin Iya, kuka take a hankali tana jin kewar mahaifiyarta, da yanzu mama ta yi mata wanka, ta shafa mata mai ta saka mata kayan sanyi.

Tana nan zaune a ƙofar ɗakin, sanyi sai ratsata yake yi, ga ƙanan ƙwari na bin ta.

Gani tayi an hasketa da fitila, ta saurin rintse idanuwanta, saboda hasken fitilar, bai ɗauke fitilar ba, har ya ƙaraso kanta ya tsaya.

"Me ki ke yi a nan?" Jin muryarsa ya sanya ta tashi a razane ta ja da baya jikinta na rawa, dan ita duk wani namiji tsoro yake bata.

"Me ki ke yi a nan?"

"Mama nake jira ta dawo"

"Kuma sai ki zauna a nan ga sanyi, ki tafi É—akin iya ki jirata mana"

Ta girgiza kai ta ce "Zan zauna a nan"

"Wuce ki tafi dalla!" Yayi maganar cikin tsawa. Da sauri ta nufi É—akin Iya, ya bi bayanta.
Chapter 9 · 0% Book details