Sashe 7
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina ƙaunar ki ummina, Allah ga ƴa ta da mata ta, Allah ka kula mini da su, ƴar kyakywar ɗiya ta" yayi maganar yana jan kumatunta. Ummi ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi ta cigaba da bacci.
Washegari da zai tafi har soro suka raka shi, ji yake tamkar kar ya tafi, amma yana fatan idan har tafiyar ta sa zata zama silar walwalar iyalin sa gara ya tafi.
Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana neman yi musu tijara, sannan suka rabu ya tafi.
Kwanaki uku da tafiyar baban ummi, kewa duk ta ishi ummi da mariya, sai dai tafiyar ta sa bata sanya sun samu sassaucin jaraba da masifar iya ba da gore-gore, gashi a lokacin waya bata yawaita ba, dan haka ba wanda ya san halin da wani yake ciki.
Bai fi sati biyu ba da tafiyar sa, abun da ya bar musu duk ya ƙare, gashi abu kamar wasa, muraran yara ke cigaba da cin zalin ummi, ga farmaki da Idris yake cigaba da kai mata, loka-lokaci da wasu daga samarin gidan, dan ma yanzu ta yi wayo sosai da sosai, da ta gansu sai gudu.
Cin zali a wurin Æ´an samarin yaran nan maza, tamkar sun samu sa'ar su, saboda tana mace, abu kaÉ—an sai a kai mata duka, ko ayi mata wata izayar ko a gida ko a makaranta, saboda ana ganin ummin tamkar sokuwa, kuma babu mai tare mata, da mariya tayi magana iya tayi kanta da tijara.
ÆŠan abun da ya rage a hannunta, ta fara fanken sayarwa, saboda ta samu abun juyawa, amma sai da iya ta cinye jarin da cin bashi, tare da tula mata ayyukan da zasu hanata sana'ar.
Abubuwa fa suka fara yi wa mariya da ummi yawa, duka ko ta ko ina, wani ta iya karewa, wani ta kasa sai dai tayi kuka ta gaya wa Allah.
Tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta samu da ƙyar ta jiƙawa ummi garrin kwaki, bayan ta dawo daga makaranta tana sha, ta ji hayaniya ta yi yawa a waje. Bata damu ba ta cigaba da aikinta.
Da gudu Alhassan ya shigo ya ce "Babar ummi Albishirinki?"
Ta kalleshi ta ce "Albishirina kuma? Menene?"
"Wai baban ummi Æ´an fashi suka kashe a hanya, zasu taho gida daga ikko!!!"
Ayshercool
08081012143
            *CUTARWA!*
Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
What's app 08081012143
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
P4
Wani irin jifa mariya tayi da kwanon hannunta, ta miƙe a gigice jikinta na wata irin tsuma, zuciyarta na bugawa da saurin gaske amma ta kasa magana.
Miƙewa ummi ta yi ita ma, tana bin su da kallo.
Iya ta fito a gigice ta ƙundumawa Alhassan ashariya ya ce "Uban wa ye ya gaya maka haka? In ji wani ɗan iskan".
Ilyas da saminu ne suka shigo, fuskokin su babu walwala.
"Ku gyara wurin da za a shigo da balarabe, Allah ya yi masa rasuwa, tun safe muka tafi É—aukko gawarsa"
A gigice iya ta ce "Ƙarya ne ban yarda ba, ya za ayi ace ya mutu? Balaraben ne ya rasu? Waye ya kashe shi, ya aka yi aka kashe shi?"
Sagir yayi sallama tare da idris, ya ce "A ina za a kwantar da shi idan an shigo ne? Ana jira fa"
Mariya ji take abun kamar mafarki, addu'a take Ubangiji Allah ya sanya mafarki ne, Allah ya sa ba mijinta ne ya mutu ba, Allah ya sa ba baban umminta ne ya mutu ba".
Magaji ya shigo da tabarma, ya shimfiÉ—a, aka yi sallama tare da Æ´an sanda, da rabi'u da suka tafi tare, aka shigo da gawar bashir, tana ta É—igar da jini.
Nan da nan gida ya cika da jama'a, Iya sai ihu take tana kururuwa tana kuka, kai da gani ka san jahilci ya samu gidin zama a wurin iya, saboda yadda take ihun ta shiga uku ta lalace.
Jiki na rawa mariya ta saka hannu ta buɗe mayafin da aka rufe gawar bashir, fuskar nan fayau kamar yana bacci, kamar wanda yayi wanka ya fito haka gawar take, ga ƙirjinsa in da aka harbe shi, jini yana ta zuba.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abun da mariya ke ta nanatawa, tare da fatan Allah ya saukar mata da nutsuwa da dangana.
Ummi ta shafa fuskar sa tana faÉ—in "Baba ka tashi, baba ka tashi daga bacci mama tana kuka" cikin haÉ—e rai sagir ya yi wa ummi tsawa ya ce ta tashi.
Sa'adatu ta ce "Haba baban auwwalu, ka tausaya musu mana".
Mutane suka cika gidan danƙam, saboda mutane sun san bashir sosai, mutum ne na mutane mai matuƙar haƙuri da girmama mutane.
Sai ajiyar zuciya kawai mariya take yi, tana rungume da ummi, aka shiga da shi É—akin Iya, aka yi masa sutura, sannan aka ce su je su yi sallama da shi.
Har a lokacin mariya ta gaza zubar da hawaye, sai wata irin ƙuna da zuciyarta ke yi mata, abu kamar wasa bashir shikenan an yi an gama, rayuwar ta ƙare.
Duk da yarinta ta ummi, amma ta san idan an mutu ba a dawowa, tayi kuka idonta duk ya kumbura, ta dinga taɓa shi tana "Baba ka tashi, ka ce zaka sai mini ƴar tsana in yi addu'a ka samu kuɗi, kullum ina yi maka addu'a"
Mariya kam zubawa gawar ido kawai tayi, tana kallon ikon Allah, wai bashir ya mutu.
Sa'adatu ta ce "Mariya ki riƙe yarinyar nan, za a shigo a ɗauki gawar"
Mariya kamar sokuwa, dan kamar ma ba ta iya gane me ake cewa.
Aka zo aka ɗauki gawar bashir, ana ta iface-iface, ummi ta riƙe ƙafar Saminu wan mahaifinta, da suka ɗaga gawar, tana wani irin kuka, amma babu tausayi ko imani, ya angije ta ƙasa suka yi waje.
Allah sarki, ba ta karaya ba ta sake bin su, tana faÉ—in "Ku dawo da baban, zai tashi fa, bacci yake yi"
Surayya, wadda take ƴar autar su bashir, ta riƙo hannun ummi tana kuka, ta rungume ta, tana ta rarrashinta.
Gida ya cika da jama'a ana gaisuwa, mariya kuwa ta samu gindin bishiyar da ke tsakar gidan ta rakuɓe, tayi shiru ba ta cewa komai, ita kaɗai ta san azabar da zuciyarta take yi mata.
Bata san hawa ba, ba ta san sauka ba, ta ji muryar iya na bala'i a cikin mutane "Dama ya za ayi mutuwar ta dame ta, ai dama ba dan Allah take zaune da shi ba, kalleta a ƙeƙashe ko kuka ba ta yi ba, alhalin ita ta takura lallai ya tafi neman abun duniya, ya zo ya wahalta mata, wallahi ban yafe miki ba"
Daram! Gaban mariya ya faɗi, jin abun da iya ta faɗa na ƙarshe.
Mutane suka shiga salallami, surayya ta ce "Haba iya, haba iya, baki san kukan zuci yafi kowanne ƙuna ba, gara ke kin yi kukan, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta, da can ba ta ce ya tafi neman kuɗi ba, sai yanzu, dama Allah ya yi ajalinsa a can za same shi".
Ai nan ta mayar da faɗan kan surayya, wanda hakan ya tilasta mata yin shiru, wasu suka goyi bayan iya saboda makira ce, wasu kuma suka goyi bayan mariya, kowa ya san kusan halinta ɗaya da mijinta, ba sawa ba fitarwa, akwai haƙuri da juriya, mussman a zamanta da iya.
Yadda ta ga rana haka taga dare, abu goma da ashirin, ga raɗaɗin mutuwar mijinta, ga sharrin da iya ta ƙulla mata, wai ita ce silar mutuwar sa, ita ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi.
Ta rasa me ta tsarewa iya, take yi mata wannan azababbiyar ƙiyayyar, saboda kawai tana auren ɗan ta, abun da ba haka take yi wa sauran sirikanta ba, kuma dukkansu babu wanda yake yi mata biyayyar da take yi mata, kawai ta camfata cewar ita ce mai farar ƙafar da ta toshe masa hanyar arzikin sa, ya kasa gaba ya kasa baya, gashi ya ɗauki son duniya ya ɗorawa mariya, yana matuƙar son ta da ƙaunarta.
Ko fuskanta Iya tayi sun yi mu'amalar aure, ta ga sun yi wanka, to wunin ranar, haka zata wuni cikin ɓacin rai da tashin hankali, a wurin iya ta din ga ƙirƙirar mata laifi kenan tana ci mata mutunci, ta rasa wannan masifar, ga uwa uba ummi sunan kishiyar ta ne da ita, wanda hakan ya sa ta ƙara tsanar ummi, ga ƴaƴanta sun riƙe ta uwa, abun da ta dama suke sha, amma tana masifar kishi da uwar su.
Washegari da azahar, dangin mariya suka dira a jigawa, suka zo gaisuwa, haka zalika Yahaya, yayan bashir da yake birni, shi ma ya zo ta'aziyya, ya ji mutuwar bashir ba kaɗan ba, abun ya girgiza shi, dan kaf cikin ƴan uwansa, ko wanda suke ciki ɗaya, basa shirin da suke yi da bashir, saboda biyayyar sa, yana matuƙar girmama shi.
Yana son ummi, kasancewar sunan mahaifiyarsu ne shi ma da ita, marigayiyya uwar gidan malam hashimu.
Ya tarar ana ta fama da ummi, ba ta ci abinci ba, sa'adatu da ba wani shiri suke yi da mariya ba, amma mutuwar bashir, da abubuwan da iya ke ta yi, ya sanya wani irin tausayin su ya kamata.
Yahaya ya ga yadda ake fama da ummi, tana kwance a jikin mariya, ba wanda ya iya cin abinci a cikinsu.
Duk da tana tsoron maza sosai da sosai, kuma shi baya yawan zuwa gidan, amma ta gane shi, dan yana kama da babanta sosai, kuma yana bata tsaraba idan ya zo.
Ya ƙarasa ya ɗauketa, ya saka hannunsa a nata, ya ce "Mamana, ki din ga yi wa babanki addu'a, kuma ki din ga cin abinci, kuka ba zai yi magani ba"
"Baba ba zai dawo ba ko, ya mutu wai?" Tayi maganar hawaye na zubo mata, kamar an kunna famfo.
"Ba zai dawo ba ummi, amma zai ji daÉ—i idan kina yi masa addu'a"
Cikin kuka ta ce "Na fi son ya dawo" ya din ga share mata hawaye, cike da tausayawa.