← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 134

Sashe 50

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ummi kawai take tana kallon noor, soyayyarta da noor gamon jini ce.

Bayan magariba Rayhan ya dawo yana zaune a falon mami, yana ta bawa ƙannensa umarni, duk barkwancinsa idan yana nan basa wani sakewa saboda akwai dealing.

Mami na zaune a gefe tana cin abinci, tana kallon citruss.

Ya kalleta ya ce "Mami kin san ina ta yi wa baƙuwar ɗazu kallon sani, sai daga baya na tuna a wurin saukar su Maryam na san muryarta, dan ban ga fuskarta ba ranar"

Mami ta ce "Auu wai ummi, yarinyar kirki".

Ya ce "Tana da tarbiyya sosai tun ranar da na ganta a wurin saukar nan, tubarkallah idonta mai kyau, ban taɓa ganin irin idonta ba".

Mami tayi dariya ta ce "Kaga iskancin da su maryam suka din ga yi mata suna Islamiyya, saboda fatarta da idonta, duk in da maryam ta zauna sai ta bayar da labarin baƙin ummi. Gashi uwar riƙonta na azabtar da ita, ai ainihin ƙawancensu ma, maryam ce ta ture ta, ta faɗi ashe ƙonuwa ce a cikin ta, ta dinga zubar da jini, uwar riƙon ta ƙonata da dutsen guga a ciki, shima da ƙyar ta gayawa malaman ƙunar duk ta jagwale"

A razane raihan ya tashi zaune, ya ce "Ta ƙonata da dutsen guga fa ki ka ce?"

"Wallahi kuwa, maryam ta ce kusan kullum cikin kuka ummin take, kuma bata magana sai ta ga dama, duk yadda za ayi da ita, ba zata faÉ—i ga abun da yake damunta ba, sai kuka".

Ya murza goshinsa a hankali ya ce "Mami kuma babu wani abu da ki ka yi, ki taimaka mata a wannan lokacin?"

"Rufa mini asiri, ai yanzu ba a wannan shishshigin, na so dai na din ga taimaka mata financially, amma yarinyar nan ba a bata kyauta ta karɓa, halint sai ita"

Ya dinga kaɗa ƙafarsa a hankali yana tunani, gaba ɗaya kalar ummi ba mai hayaniya bace, hasali ma fuskarta kalar tausayi ce.
To wani laifi za ta yi wa mutum, har a ƙonata da iron a ciki, ita kuwa wannan wace irin azzaluma ce.

Labarin da mami ta bashi tana dariya, bai ga abun dariya ba a ciki, na cewa yara na tsokanarta saboda tana da duhu da kuma ƙwayar idonta, meye a baƙar fata duk halittar Allah ce, kuma idanunta meye aibunsu, ai abun a hukunta su ne a wancan lokacin, ga child abuse a gida, makaranta ga takura daga abokan karatunta, Allah ka ɗai ya san the hardship she goes through.
Dan bai manta yadda Maryam ke bashi labarin abun da ake yi wa ummi ba, da yadda take kwatanta masa baƙinta, sai duk iya ƙoƙarin sa wurin gano muninta shi bai gani ba.

Fuskarta kawai yake hangowa, ko ɗazu da suka yi faɗa kan ya shigo bashi da gaskiya, amma ta bashi haƙuri, komai nata simple ne.

Ya miƙe tsaye ya ce "Mami sai da safe, bacci nake ji" yana gama maganar ya fita.

***
Ko da farida ta dawo sai da ta ci wa ummi mutunci, duk da ta san ummin wurin aiki take zuwa, domin kuwa bautar ƙasa take a lokacin a wani gidan jarida, daily news.

"Maama dan Allah ki daina yi wa anty ummi faÉ—a, ba gashi nan duk mun gama yi miki aikin gidan ba".

Cikin tsawa ta ce "Idan ina magana ki na saka mini baki sai na yi ball dake" tayi maganar tana nuna noor da yatsa.

Ta mayar da idonta kan ummi ta ce "Dan kan ki, gaba É—aya kin mayar mini da yarinya fitsararriya mara É—a'a kamar ke, zaki haifa ne kema. Sakwara zaki daka, da jar miya, kije Abdul ya kai ki asibiti ki kai wa inteesar ki kwana da ita asibiti, kausar ta dawo gida".

Daga auren inteesar zuwa yanzu, tayi ɓari ba adadi, dan kamar har mijin nata ya fara ƙosawa da hakan.

Ummi ta je kwana da ita, ta tarar ana yi mata ƙarin jini, duk ta rame, ƙannen mijin suna zazzaune, suna ta hirarsu ko a jikinsu da halin da take ciki, kausar ce a kusa da ita a zaune, ita ma kuma danna wayarta take yi.

Ko da ta ga ummi ta wani haɗe rai ta yatsine fuska ta ce "Dan wulaƙanci, tun kan mu taho asibitin nan ake jiranki, amma ki ka ƙi dawowa kin bar mutane da yunwa, kuma kin san dai ba iya cin abincin sayarwa muke ba"

Ummi ta ja wuri ta zauna ba tare da ta kulata ba, suka gaisa da ƙannen mijin inteesar.

Babu kunya suka ja kwanon sakwarar nan suka buɗe, suka ci abin su, suka gama suka ƙara gaba.

Sai da inteesar ta yi sati a asibiti, ummi ce ke sintirin kai abinci da É—awainiyar kwana da ita, amma duk basa gani sai rashin mutunci da hantara, gashi idan ta kwana kan wani yazo daga gida ta koma ta shirya ta tafi in da take SIWES, sai ta makara sosai da sosai.

Idan ta je wurin aiki, shima ayi ta yi mata faÉ—a a kan makara.

Farida ta cewa sageer ya bata inteesar su tafi gida, ta É—an kwana biyu ta huta.

Inteesar ta ji daɗin hakan, dan kuwa azabar ƙannen mijinta sun isheta, mijin suna zaune lafiya sai abun da ba a rasa ba, amma fa ƙannensa ba sa laifi, dan akan su har zaginta yake yi, ya ci mata mutunci tayi ta musu bauta.

***

A ƙalla ummi ta shafe mintuna goma sha biyar a tsaye a bakin titi, tana ƙoƙarin tsallakawa, amma ta kasa saboda tarin ababen hawa da ke kaiwa suna komowa. Ga rana gashi ta gaji matuƙa, ta gaji da tsayuwa.

"Tsallaka titin ma sai kin yi masa yanga Yaya?" Sai da gabanta ya faÉ—i, dan kuwa ta tsorata sosai.

A hankali ta waiwaya tana kallon fuskar sa.

Idon da yake son gani ya samu yana kallo, dan yau ba niƙab ta saka ba, facemask ne.

Sai dai bai kalla yadda yake so ba ta janye idonta, tana ajiyar zuciya.

"Na tsorata ki ne?"

Ta ce "Na tsorata ne, ina wuni?"

Ya dawo gefenta ya tsaya ya ce "Yini yana gidan biki, Ai mami ta ce ki daina gaisheni, ni ƙaninki ne, dama kin ce girma ya riga hankali zuwa"

Murmushi ta yi ta sake cewa "Ya mamin da kowa da kowa?"

Raihan ya ce "Suna nan ƙalau, ke na hango na tsaya a tsallake, morethan 20minutes, kin kasa tsallaka titi ki na yanga"

A É—an marairaice ta ce "Eyya ba yanga nake yi ba, kasa tsallakawa na yi ne"

Ya jinjina kai ya ce "I see"

Ya ce "Taho mu tsallaka" Gaba ya fara yi, tabi bayansa a hankali, sai da suka je tsakiyar titi, ta juya zata koma da gudu saboda motar da ta taho da gudu. Hanata hakan yayi, ta hanyar danƙo hannunta yayi suka yi gaba suka tsallaka.

Ƙoƙarin cire hannunta take daga nasa, amma ya riƙe gam ya ce "Ke haka ki ke tsallaka titi? Gaba ɗaya kin tsorata kanki? Nutsuwa ake yi idan za a tsallaka titi"

Ta sunkuyar da kai, tana cigaba da ƙoƙarin cire hannunta daga nasa.

Ya kalli hannayensu nasa fari tas, na ummi mai duhu, sai dai nata hannun yafi nasa kyau sosai da sosai, nasa da gani kaga hannun namiji, duk a murɗe ga uban jijiyoyi, nata kuma ɗan madaidaici, ɗauke da dogayen yatsu, tafin hannunta fari tas, haka faratanta farare ƙal dogwaye gwanin sha'awa, ga hannunta tamkar auduga dan taushi.

Ya zare nasa ya basar ya ce "Mu je na ajiye ki a gida"

Ta ce "A'a kar ka damu, wannan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi"

Raihan ya ce "Ai ba babur bane, yau mota ce, tun da ba kya hawa babur sai mota".

"A'a ba haka bane wallahi, kar ka damu, yanzu zan tafi na gode sosai".

Sai ka ce ubanta haka ya haÉ—e rai, ya ce "Mu je in sauke ki, bana satar mutane ai, ki daina haka"

Haka nan ummi tayi tsuru-tsuru, dan da ya haɗe rai sai yayi mata kwarjini, ya nufi tsaleliyar motar da yayi parking ɗin ta a gefen titi, glasanta baƙaƙe wuluk, sai sheƙi yake, da gani ka san ba a daɗe da fara hawanta ba.

Ya buɗe wa ummi gaban motar, gaba ɗaya ji tayi kamar zata aikata zunubi, ko da wasa bata taɓa hawa motar wani ba, idan ba ta kawu yahaya ba.

Wani sanyi ne haɗe da ƙamshi mai daɗin gaske ya baƙunceta a cikin motar.

Ya zagaya ya zauna, ya rufe motar, ya ɗaukko robar ruwa da lemo, ya miƙa mata ya ce "Ga ruwa ki sha, kin daɗe a rana".

Fuskar sa ta kalla, ta karɓa ta ajiye a kan cinyarta.

"Ina zaki yi ne?"

"Gida"

"Gida ina?" Ta kwatanta masa, ya ja motar ya fara tafiya.

Ta gefen idonsa yake kallon yadda duk tayi tsuru-tsuru kamar ba ta da gaskiya, gaba ɗaya a takure take, kamar wadda ke zaune a kan ƙaya.

Tunani yake ta yi a zuciyarsa, this innocent looking lady, ace an azabtar da ita har haka, to wane irin laifi zata yi, da zai saka ayi maka haka?.

ÆŠan satar kallon sa tayi, kamar ba shi ta gani wancan lokacin ba, yana barkwanci da wasa da dariya ba.

Ya É—aukko wayarsa ya nemo lambar Maryam, ya saka a hansfree.

"Ke yane?"

Ta amsa da "Normal, ya aka yi?"

"Guess what?"

Ta ce "I have no idea, menene?"

"Na sake haɗuwa da ƙawar nan taki, da na ce miki tazo gida gaida mami"

Ta ce "Allah sarki, ummi?"

"Eh ita"

"Wallahi bani da numbernta, ban sani ba ko tana da waya ma?"

"Baki da kirki, maybe tun da ki ka yi aure baki sake neman ta ba".

"To a ina zan ganta, ban son zuwa gidansu, antynta ba ta da mutunci"

Ya ce "Ai shikenan, a gaida yaran"

"Za su ji in sha Allah".

Ya ajiye wayar, ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa.

"In da na É—auko ki aiki ki ke ne a wurin?".

Ummi ta ce "SIWES"

"Me ki ke karanta ne?"

Ummi ta ce "Mass communication"

"Mass communication, ai karatun masu baki ne, ke kuma kamar ba kya magana ma"
Chapter 50 · 0% Book details