← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 134

Sashe 102

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da yana complain da kunyarta ta yi yawa, amma yana jin daɗin wuninsa a gida tare da ita, ya ci abinci da ita, ya shaƙi daddaɗan ƙamashin turarukan ta, uwa uba lallausar fatarta da ba ya gajiya da taɓawa, jikinta tamkar jikin tarwaɗa, ko kuma wata fulawa.
Shi komai na ta burgeshi yake yi.

Raihan ya kalli mami ya ce  "Maman bauci tazo tana gidanmu tana jirana"

"Saura ka je ka gaya mata wani abu, ta zo ta cika mini kunne da masifa".

Mintuna arba'in sai ga raihan ya dawo.

Aikuwa hajiya Aisha ta din ga masifar weekend ya zauna a gida da matarsa, amma ya fita yawo, idan ya je wurin mamin shayar da shi take ko kuwa?.

Shi dai bai ce komai ba ya ce "Ayi haƙuri na daina, amma kar a juya mini baya a koma wurin ummi"

Ta ce "A'a ni fa na yi ƴa, ga iya girki ga mutunci, kalli yadda ka yi ƙiba fa, ummi ta iya kiwo, ya ma sunan da ka ke gaya mata"

Ba kunya raihan ya ce "Khairun nisa'i"

Ummi kuwa kamar ta nutse, ta tashi ta tafi kitchen tana wanke kwanuka.

Ya sameta a kitchen ya ce "Madam sannu da ƙoƙari, Mummy na ta yaba miki, ina godiya sosai da sosai"

Hararsa tayi ta ce "Baƙina ne ai ba naka ba"

Ya ce "To ai shikenan, zo ku yi sallama"

Ummi ta ce "Har tafiya za su yi?"

"Wallahi kuwa, ta ce ko gidanmu ba zata ba bauchi zasu koma, gashi ba su taho da direba ba, kar su yi dare".

Ta ce "To yi gaba zan taho"

"Saboda me?"

"To kawai sai kuma a ga mun jero tare?"

Danƙo hannunta yayi suka yi waje, turus ummi ta yi ganin iyayen akwatuna a falo.

Hajiya Aisha ta ce "To ga kayanku nan, ku duba abun da bai yi miki ba, sai a canzo, ko kuma ma yi waya kawai, tafiya zamu yi"

Ummi ta ce "Mummy ki bari ki kwana mana"

Hajiya Aisha ta ce "Taɓ mijina yana gari, wa zai kula mini da shi, sai mun yi waya"

Cikin sauri ummi ta tafi É—aki, ta É—ebo turaren wuta, na gashi da na jiki, ta din ga haÉ—o kaya a leda, ta bawa Siyama ta ce musu ba yawa.

Hajiya Aisha ta yi musu nasiha, tare da fatan alkhairi suka tafi.

Nan raihan ya zauna a falon, yana bubbuɗe akwatunan, ummi kawai ta zuba masa ido tana kallon uban kayan da ko a mafarki ba ta taɓa tunanin mallakar su ba.

"Ki saukko ki gani mana sweetheart" ta saukko ta zauna a kusa da shi tana kallon kayan.

Ganin tayi saroro kamar sokuwa ya sanya ya ce "Ko kayan ba su yi miki bane ba?"

Kawai ya ga hawaye na bin idonta, gaba ɗaya ya rikice ya ce "Menene kuma? Ko Mummy sun yi miki wani abun da ya ɓata miki rai ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To menene? Bana son kukanki ummi, gaya mini"

Ta ƙara matsawa kusa da shi, ta rungume shi tana kuka.

Ya saka hannunsa ya tallafo fuskarta, cikin kulawa ya ce "Gaya mini menene?"

"Na gode" tayi maganar wasu hawayen na zubo mata.

Raihan ya ce "Haƙƙinki ne fa ummi, meyasa zaki yi kuka?"

Ta sake kwantar da kanta a jikinsa, ta ce "You mean a lot to me, na tuna lokacin da na shekara biyu babu kayan kirki, yau ka gwangwaje ni da wannan uban kayan, ni wallahi ban san ma me zan ce ba, kamar kalmar godiya ta yi kaÉ—an, Allah ya suturta ka duniya da lahira, ya yalwata arzikinka, na gode MD"

Jikinsa yayi sanyi sosai, duk da bai san cikakken tarihin ummi ba, amma alamu sun nuna ta sha gwagwarmaya da rayuwa.

"To ki daina kukan haka, in sha Allah in dai ina raye, sutura sai dai ki É—auka ki bawa wani, sutura ba zamu yi ta É—inka ta muna sawa".

"Na gode MD, amma dan Allah kar ka takurawa kanka yi mini abun da ba ka da shi, ni dai na gode sosai"

"To ba zaki kirani da wani suna na soyayya ba, sai MD"

"MD my dear" ta faÉ—a tana murmushi.

"Wow ashe duk tsawon wannan lokacin, am your dear ban sani ba, barakallahu fik baby"

ÆŠaÉ—É—aga mata kayan ya cigaba da yi, kaya sun haÉ—u masu tsada har da gwal.

Sai da ya zo kan akwatin ƙanan kaya, ya din ga ɗaɗɗagawa yana cewa ba ƙaramin kyau zaki yi a ciki ba.

Ummi ta ce "Ai kai a nan ka fi kauri, ni bari na je kitchen abincina kar ya kama".

Idan ummi ta kalli raihan ta kalli kayan nan, sai ta rasa me ma za ta ce masa, ya baje yana ta aiki a system gefen sa ga biro da takarda.

Dogon matashi cikakke, dai-dai gwargwado raihan kyakkyawa ne, kuma duk kyawawan mata babu wadda ya gani ya ce yana so, sai ita kuma yake ta wahala da ita.

"Ya dai madam?"

Ta tashi ta ce "Bakomai, zan je wancan falon na gyara shi kan magariba".

Ya ce "Yauwwa, ni kuwa na ce ko Æ´ar aiki za a samo miki ne? Ta din ga taya ki aikin nan, yayi miki yawa".

Ummi ta ce "Aikin gidan nan guda nawa yake, zan iya abuna"

"FaÉ—i gaskiya dai, ko abun ne ya motsa, dan kar a aure ni"

"To a aurekan mana, duk wadda za ta iya zama da ni ta shigo"

Ya kwashe da dariya ya ce "Eh lallai kin yi baki baby".

Ummi ta É—auki hoton kayan, ta turawa su Yaya maryam, suka din ga murna tare da sanyawa raihan albarka.

Iya ƙoƙari ummi take yi, wurin rage kunyar raihan da take ji.
Dan haka a yau tayi iya yin ta tayi irin shigar da yake so.

Aikuwa daga kallon da ya din ga yi mata, ta gane ya ji daÉ—in hakan sosai da sosai.

Ya sha mamaki sosai da sosai, dan kuwa tayi masa kyau sosai da sosai, Allah ya taimaki ummi raihan ba shi da abokan da zai yi zaman majalisa da su.

Duk a kunyacen take, amma ta dake kar sokoncinta ya sanya shi fara kalle-kallen.

"Baby zaka kai ni gaida su mamin da su kawu".

Ya ce "Wow, shagwaɓar nan taki tana burgeni ummi"

Maganar Iya ta tuna, da take ce mata 'Tana shagwaɓa da fuska kamar kashi'

Ya amince da zuwanta gaida su mami, amma ya ce sai ranar juma'a da daddare. Washegari ranar asabar kuma sai ya kai ta gidansu.

Ummi ta yi ta murna, raihan ya ce "Ai in dai zaki din ga abun da nake so, zan zama mijin hajiya Salma.

Wata irin soyayya raihan yake nuna wa ummi, da take fatan ta É—ore har abada.

Ranar juma'a tun safe, ummi take aikin yin sinasir da miyar agushi, wanda za ta kai gidan su raihan.

Tun sallar magariba ta shirya take jiran raihan, ya dawo ya ƙare mata kallo ya ce "Gaskiya kin yi kyau da yawa, ba zan tafi da ke a haka ba, sai ƙamshi kuma ki ke yi, am jealous ki rage kyan nan"

"Daga ni sai kai fa zamu tafi a mota mu dawo, dan Allah ka shirya mu tafi"

Sai da ummi tayi da gaske, sannan ya shirya suka tafi.

Tambayarta ya din ga yi a kan wannan kulolin restaurant za ta buÉ—e ne?.

"Eh in dai zaka yi patronizing É—ina"

"To É—an buÉ—e ki san mini abun da ki ka dafa É—in"

"Aikuwa ba za ka ci ba"

"Suna tafe suna faÉ—ansu irin na masoya".

Karɓar da mami tayi mata kawai jikinta yayi sanyi, ko kallo ummi ba ta isheta ba.

Safiyya kuwa tun da ta ga ummi jikinta yayi sanyi, ana ta ummi mummuna ce, amma ta ga ummi dirarriyar mace, muryarta kawai idan ta yi magana sai ka so ganin waye yake yin maganar, gashi komai na ta a nutse. Duk da dare ne amma duk wanda ya ga ummi ya santa a da, ya san ta canza sosai, fatar nan ta ƙara kwanciya tayi fresh sai ƙamshi take yi.

Ko gaisuwar ummi taƙi amsawa.

Raihan ya ce "Mami zuwa muka yi ta gaishe ki, ta yi muku bangajiya"

"Na ce maka ina nemanta ne, tun a farko ban gaya maka babu yawuna a maganar aurenka ba? Ka nema mata wata sirikar bani ba. Muguwa kawai, sumi-sumi da ke na zata ta Allah ce, ashe mutuniyar banza ce, kuma da ni ki ke zancen. ÆŠa na ne dai wallahi sai kin bar shi, zan yi masa irin auren da nake so, kuma ina nan dawowa kanki"

Raihan ya tashi ya ce "Ummi mu je mu gaida su Alhaji mu tafi kar dare yayi"

Ta tashi kanta a ƙasa, ta ɗauki kwandon da suka zo da shi, ta ajiye wa mami na ta food flask ɗin.

Mami  ta ce "Kwashe tsiyarki, ba abun da zan yi da abincinki"

Raihan ya durƙusa ya ɗauka ya ce "Bari a ƙarawa mami da shi"

Ta buÉ—e baki tana kallon raihan.

Bayan fitarsu Nihal ta ce "Taɓ mami dama haka matar yayan take? Gaskiya babu lallai ya saurari safiyya, kin san halin sa ba komai yake burge shi ba, amma idan ya ce yana son abu ya dage, canza shi sai Allah. Kalli dirarriyar mace ga iyayi".

"Ke dalla rufe mini baki, tashi ki bar falon nan"

Can kuwa ummi jikinta yayi sanyi, amma karɓar da ta samu a wurin Alhaji da Hajiya, sai ya mantar da ita abun da mami ta yi mata.

Sai gashi sun shantake, har goma na dare suna gidan, sun sha nasiha da sanya albarka daga bakin Hajiya da kuma Alhaji.

Alhaji da kansa ya kira Salim da Sagir a waya cewa yana nemansu, bayan sun zo, ya sake gabatar musu da ummi.

Tun ummi na nan suka fara cin abincin su, suna santi ana koÉ—a girkin nata, wanda hakan ya yi wa ummi daÉ—i sosai.

Goma da rabi, sannan suka tafi gida, raihan bai yi mata maganar abun da mami ta yi ba, ita ma ba ta yi masa ba, sai dai ta damu da ganin safiyya ya É—aga wa ummi hankali, ganinta yarinya kuma kyakykyawa.
Chapter 102 · 0% Book details