← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 134

Sashe 70

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida ta duba wajen dining, ta É—aukko kaya ta watso su tsakar falon ta ce "Sai ka tambayeta a ina ta samu wannan kayan? Wallahi dole ta bar mini gida, kan ta lalace ta lalata mini yara"

Ummi tabi kayan da kallo, kayan mayukanta ne, na wurin raihan da kayan sawa.

"Wannan kayan sun fi ƙarfin na dubu ɗari, sai ka tuhumeta a ina ta samu, kuma gidanka ba zan bar shi ba, dan na ci gida".....

Ayshercool
08081012143
[4/20, 7:20 PM] Authoresses: *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P29

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

29

Wata irin tsuma jikin ummi ya fara yi, dan ba ta san ta ina zata fara bayani ba, bata taɓa tunanin farida za ta shiga ɗakinta, tayi mata bincike ba.

Dr. Ya bi kayan É—aya bayan É—aya da kallo.

Cikin haƙilo farida ta ce "Sai ta yi maka bayanin in da take samun wannan kayan, idan ba wani mugun abun take aikatawa na rashin gaskiya ba"

Tsulum noor ta tsoma baki ta ce "Kai, yaya raihan ne fa ya saya ya bata, ko yaya ummi?"

Kamar gunki ummi ta sake sandarewa, dan ba ta san ta aka yi noor ta riƙe sunan raihan haka ba ma.

Dr. Ya durƙusa ya tsince kayan, ya mayar cikin ledarsu, ya miƙe tsaye ya kalli farida ya ce "Bani mukullin da ki ka rufe mata ɗaki"

"Ban gane ba, me ka ke nufi?"

"Abun da ki ka gani, ba budurwa ba ce ba? Ke abubuwan da ake kawowa kausar cikin gidan nan zama ki ke ki tuhume ta?"

"Amma tsakani da Allah ka taɓa ganin wani yayi sallama da ita da sunan yana sonta, da zai saya mata wannan kayan masu tsada?"

Ya wuce É—akin farida, tabi bayansa tana cigaba da masifa, ya É—aukko mukullaye, ya dubi ummi ya ce "Mu je"

Tabi bayansa hawaye na zuba daga idonta, ya buÉ—e É—akin nata, duk an hargitsa shi.

Ya ajiye mata kayan, ya kalleta ya ce "Mamana, na yarda da ke É—ari bisa É—ari, na san ba zaki aikata wani abu na Allah wadai ko a bayan idona ba, goya miki baya baya nufin, ki aikata abun da bai dace ba, ba zan matsaki a kan lallai sai na san me ki ke ciki ba, ni uba ne, kuma malamin makaranta, na san yadda zan tafiyar da tarbiyar yarana.
Kin mai munzalin da bin diddigin rayuwarki, ba shi ne mafita ba, amma dai ina sake yi miki tuni, da ki ji tsoron Allah, ki kuma kare mutuncinki, amma har ga Allah ni bana zargin ki, ki goge hawayenki ki samu ki huta, ni ban gaji da zamanki da mu a gidan nan ba, saniya ba ta taɓa gazawa da ƙahonta, dan haka ki kwantar da hankalinki komai mai wucewa ne, kuma in sha Allah zaki sha mamakin abokin rayuwar da Allah zai zaɓa miki, ke dai ki cigaba da tsare mutuncinki"

Ummi ta jinjina masa kai, ya fita daga ɗakin, ta zauna a hankali tana kallon kayan, tayi shiru tana nazari, idan har zargi zai shiga zuciyar dr. Game da ita, gara ta nemi duk mai yiwuwa ta rabu da raihan. Tabbas kaya ne masu tsada da ta cancanci a tuhumeta a kansu, da kawu ya matsa ta ina zata fara yi masa bayanin wannan alaƙar ta su, da ba kowane mai hankali ne zai sanyata a gurbi mai ma'ana ba.

Ya zama dole ta nesanta kanta da raihan, duk da abu ne mai wahala a wurinta, daga haɗuwarsu zuwa yanzu, ya gina wani tarihi da ba zai rushe ba a rayuwarta, raihan na daga cikin mutane masu muhimmanci da ba zata taɓa mantawa da su ba, zuciyarta ta saba sa shi, ta shaƙu da shi, ya bata ƙarfin gwiwa daban-daban, ya sanya ta jin ita cikakkiyar mace ce ɗan Adam da zata iya gogayya da kowa, tabbas raihan ya cancanci a kira shi ƙaraminsu babbansu, domin kuwa a manyan ba kowa ne za a samu da irin qualities ɗin sa ba.

A hankali ta tattare kayan, ta gyara É—akinta, ta rama sallolin da suka tsere mata, ta cigaba da tunani.

Ta ɗaukko wayarta ta duba, missed call ɗin sa duk a wayar, har da saƙo yana tambayarta meyafaru ba ta ɗaga wayarsa?.
Ta kashe wayar gaba É—aya ta ajiye, tana son fara koyawa kanta janye wa raihan.

Ta yinƙura ta fito daga ɗakinta, amma ta jiyo hayaniyar kawu da farida, kuma duk a kanta, jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, da tana da wurin zuwa da zata bar wa farida gidanta, ko kawu ya samu sassauci daga wulaƙancin da farida ke yi masa.

***
Anty Rakiya ta cigaba da matsa lamba, da ƙarfafa mami, a kan lallai a haɗa auren nan na zumunci, ita kuma mami ta cigaba da matsawa raihan, tare da ziga Alhaji a kan lallai a takura raihan yayi aure.

Abun ya fara damun raihan, dan haka ya samu hajiya da maganar, Hajiya ta ce "Babban mutum, menene a ciki dan ka yi aure, gaskiyar maminka ne shi ne cikar kamalarka ai".

"To hajiya sai in yi aure su yaya ba su yi ba, kuma nema ake fa a sakani na auri wadda ba na so, ni bana son yarinyar nan"

"Raihan, dan ka riga su Salim aure babu laifi a ciki, bujirewa umarnin mahaifiyarka ba shi da fa'ida, ko ba ka auri wadda take so ba, ka yi ƙoƙari kai ka kawo musu wadda ka ke so"

Yayi shiru yana nazari, sannan ya kalli hajiya ya ce "Shikenan hajiya na gode sosai da sosai"

Ya tashi ya fita, yana nazarin maganar Hajiya.

Gefe guda kuma yana mamakin kasa samun ummi a waya, har ta what's app, ya fara tunanin ko dai wani abun ya sameta ne.

Yaje wurin aikinsu Ummi, ya tambayi mai yi musu shara, ya ce masa ba ta je ba.

Ita ma ummi a lokacin da take ƙoƙarin ƙauracewa kiran raihan, headmastern su ya kunno kai, sai ya din ga kiranta a waya, wai su gaisa, wannan satin har da bata dubu biyu wai ta hau mota, saboda ɗawainiya da take yi da ɗalibansu.

Hankalinta ba a kan wannan yake ba, kamar ta fi raihan azabtuwa da ƙauracewar da ta yi masa, gashi pressure cikin gidansu, ta ƙara yawa, dan kuwa farida kullum cikin masifa da tashin hankali take a cikin gidan nan.

Babu tsammani dr. Ya samu ummi ya ce mata "Mamana, wani mutum ya zo wurina, ya ce mini yana sonki, kuma babu daÉ—ewa yake son ayi auren, na bashi damar ya zo ku gana, sai dai ba ina nufin lallai sai kin aure shi bane ba, bana son yi masa karambani, ganin babban mutum ne, amma duk yadda ku ka yi sai ki gaya mini"

Ummi ta amsa masa da to ne, amma ta shiga cikin fargaba da zullumi, tare da tunanin, waye wannan? Kai tsaye ya tafi wurin dr.?

Abun yayi ta bata mamaki, sai dai sam ba ta É—okin abun, domin kuwa bayan saka wayarta a flight mode, sai ta koma tana duba messages É—in raihan.

Gaba ɗaya ummi ta manta da dr. Ya ce za ta yi baƙo, saƙon raihan na ƙarshe ya tsaye mata a rai.

"Ummi na bincika kina lafiya, amma you are avoiding me, ban sani ba ko nayi miki laifi ne, idan na yi miki laifi ne dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, ina cikin damuwa sosai wallaahi, ban zaci shaƙuwarmu ta kai in shiga damuwa haka ba, dan Allah ki yi mini reply ummi, zan tafi italy gobe in Allah ya kaimu da asuba, dan Allah ki yi mini magana"
Ajiye wayar ummi tayi, idonta na cika da hawaye, "Ban kyauta maka ba raihan, amma yanzu ko na yi maka bayani ba zaka gane ba, buyagi zaka yi mini" tayi maganar a hankali, tana sake kallon wayarta.

"Yaya ummi, wai baƙonki ya zo" noor tayi maganar ba tare da ko sallama ta yi ba.
Chapter 70 · 0% Book details