← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 134

Sashe 61

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta saka takalmanta, ta tashi zata tafi, farida ta zabga mata wata irin ashar ta ce "Dawo nan ina magana zaki wuce, sai na tsinke ki da mari tukuna, ƴar ƙauyen banza daga zuwa cin arzki kin zaƙe, baya ganin kowa da gashi sai ke, zan yi maganinki, in dai ina numfashi wallahi sai kin bar mini gida. Ya kai ki duk in da zai kai ki, tun da su dangin mahaifiyarki da ƴan ƙauyen naku ba su da hankali, da ma neman maraba suke yi da ke".

Ummi ta danƙe wayarta da take vibrating na kiran raihan, zuciyarta na wani irin zafi, idanunta suka cika da hawaye, yanzu meye laifinta a saɓanin da suka samu yau ɗin, da har aka huce a kanta haka da cin mutunci.

Sai da farida ta gama, sannan ta juya ta kamar hanyar fita, ta goge hawayen da suke shirin zuba, saboda kar raihan ya gane, ya matsa mata da tambayoyi.

Kallo É—aya ya yi mata ya kawar da kai, dan ko gaishe shi ba ta yi ba, kawai ta zauna, tana ta murza yatsunta.

Ya kunna motar sannan ya ce "Yau kin shanya ni fa, ga kuma kulolinki na abinci na gode sosai, Allah ya ƙara zaƙin miya".

"Amin" ta faÉ—a a hankali.

Tsit har suka kusa zuwa ya gaji da shirun yana ta son ya tsokane ta, amma gaba ɗaya ko in da yake taƙi kallo, waje take kallo, tana fargabar kar Allah ya jarrabeta da abun da zai mayar da ita gagarawa.

Unexpected taga har sun je tana can tana tunani, ta kalli gefe ta ce masa thank you.

Ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma ta ga ya saka lock, ta waiwayo ta sanya idonta cikin nasa, bai ce komai ba ya zuba mata ido.

Idonta fal hawaye ta ce "Zan sauka"

"Are you ready to tell me?" Yayi maganar very serious.

Ta ɗan sake yin shiru, tare da sunkuyar da kanta ƙasa.

"Salma" ta saci kallonsa sannan ta sauke idonta, tana ta kokowa da hawaye kar su zubo.

"Yanayinki ya bayyana komai, kuma kin saka ni a damuwa nima, dan Allah gaya mini, idan ba haka ba zan yi ta kokwanto".

Kawai hawaye ya fara gangarowa daga fararen idanuwanta, wani na bin wani.

Tun tana yi a hankali, har sautin kunkan nata ya fara fita sosai da sosai, ta sanya tafukan hannayenta, tana wata irin sheshsheƙar kuka mai ƙona zuciya.

Ji ya din ga yi ina ma kowace irin damuwa ce, ya É—auke mata ita duka, idan ba zai iya ba su raba damuwar biyu.

Ya saka hannayensa ya sauke nata, ya zira hannu a aljihunsa ya É—aukki handkerchief, ya saka mata a hannunta ya ce "Ya isa haka, goge hawayenki"

Ya kira manager a waya, ya ce masa ummi ba ta da lafiya, ba zata shiga shago ba yau.

Ummi ta kalleshi, ya ce "Mu je yau ki tayani aiki a namu office É—in yau"

Za ta yi magana ya ce "Mata shhh" ya ja motar ya bar wurin.

Ta É—an yi shiru tana kallon hanya, ta rasa dalilin da ya sa ba ta iya yi wa Raihan musu.

"Mu je ki ga wurin aikina, sai mu je shopping É—in, daga nan zaki gaya mini meyasaki kukan?"

Tayi ajiyar zuciya tana kallon fuskar sa, "Ko haryanzu ban kai in san damuwarki ba?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"To idan kin huce, sai ki gaya mini"

Suna tafe yana ta É—an jan ta da hira, ta fara sakewa.

Ummi ta sha mamakin ganin wurin aikin su raihan, kuma nan kawai babban office ne na gudanar da ayyukan kasuwanci, ba wurin da suke gudanar da kasuwanci ba.

Yadda raihan ya wani maze, ake ta girmama shi, har mamaki ya bata, kamar ba raihan É—in da suke hira da wasa da dariya ba, ya wani maze.

"Raihan wai me ku ke sayarwa ne?"

"Mutane, da masu kukan banza, da matsorata, da ragwaye, sai kuma mun kai sai kawunan mutane mu sayar, kin ga kamar ke ɗin nan, na ajiye ƴan china zan sayar musu da idonki ne, da ƙafafuwan ki a cire a saka mini" handkerchief ɗinsa da yake hannunta ta kwaɗa masa, yayi gaba yana dariya.

Sagir suka tarar a cikin office É—in a zaune, yana jiran zuwan Raihan.

Ummi ta gaishe shi ya amsa, raihan ya ce "Yaya ya na ganka a nan kuma, lafiya dai ko?"

"Kai haka ka ke yi sai ka ga dama zuwa wuri kake zuwa? Ka shanya mutane suna jiranka?" Ya jefa masa takarda ya ce "Signing zaka yi mini"

Raihan ya ƙarewa takardar kallo ya ce "Wannan Alhaji yakamata ka bawa yayi maka".

"Shi ya turo ni wurinka"

"Amma yaya meyasa zan yi Signing ka fitar da wannan kuÉ—in haka? Me zaka yi da su?"

Abun ka da mai shaye-shaye a kusa, ya daki tebur ya kalli raihan ya ce "Wai kuɗin nan nake ne? Ina ruwanka ne, ya gani ya ce in zo ka saka mini hannu, business zan fara, kar ka ɓata mini lokaci"

Raihan ya juya takardar ya ce "Sana'ar me?"

"Ban sani ba" ya bashi amsa.

"Ba zan saka hannu a wannan takardar ba yaya ka yi haƙuri, sai dai ka zo mu yi aiki tare a din ga biyan mu, sai ka tara kuɗin da ka ke buƙata, amma yana shan wahalar tara dukiyarsa bai kamata a din ga yi masa ɓarna ba".

Kan kace kwabo, sagir ya shaƙe raihan, yana zazzaga masa bala'i.

Nan da nan ummi ta rikice, saboda ba ta son faɗa ko tashin hankali, take ta fara kuka, tana basu haƙuri.

Yinƙuri ɗaya Raihan yayi, ya hankaɗa Sagir, sai da ya kai ƙasa.

Ya É—auki takardar ya yayyaga, ya watsa masa cikin kurari da zafin rai ya ce masa "Get out" ya É—aga murya ya ce "Idan da wani a waje, ku kirawo mini security su fita da shi".

Ummi ta ce "Raihan yayanka ne fa, ya zaka yi masa haka?" Kallon da ya yi wa ummi ne ya sanya ta jan bakinta ta tsuke, dan gaba É—aya tsoro ya bata jikinsa har tsuma yake yi, kamar wani zaki.

*Khadija ƴar gatan mama, ina gaisuwa 😂 Autar manya tamu ta gargajiya, Allah ya bar zumunci, ɗaukacin jama'a masoya littafin CUTARWA! ubangiji Allah ya bar ƙauna*

Ayshercool
08081012143.
                   *CUTARWA!*

26

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

26

Sagir ya miƙe cikin zafin rai ya ce "Ni ka yi wa haka raihan?"

"Na yi maka ɗin, da na lallaɓaka meyasa ka kai ni bango? Ai sai ka bari na kammala masa aikinsa na bar office ɗin, sai ka sake rubuta masa wata takardar shi ya sanya hannu ba ni ba".

Cikin zafin rai Sagir ya nuna kansa da yatsa, yau shi raihan ƙanin ƙaninsa ya yi wa wannan cin mutuncin.

"Zaka ga abun da zan yi maka, komai ya faru ka kuka da kanka"

Raihan ya ce "Get out from here, ko na sanya security su fitar da kai".

Ummi ta ce "Dan Allah raihan kar ka yi haka, zaku zubarwa da mahaifinku mutunci a gaban ma'aikatansa, kuma kar hakan ya shafi zumunci da mutuncinku"

Sagir ya fice daga office ɗin rai a ɓace, Raihan ma rufa masa baya ya yi, ummi ta bishi da sauri za ta yi magana, ya ce "Ki jira ni a nan" ya fice shi ma.

Zama ta yi zuciyarta babu daÉ—i, tana ta tunani, yanzu ace Æ´an gida É—aya ciki É—aya suna wannan abubuwan, abun da mamaki.
Sai kuma ta tuna ba abun mamaki bane ba, duba da yanayin na su familyn suma.

Ummi har ta fara gajiya da jiran raihan, ta kira shi a waya, amma ta ga wayar ta sa a office É—in tana ringing.

Ta sauke hannunta a hankali, tana cigaba da kallon hanya, Raihan ya dawo office É—in, hannunsa É—auke da leda, ya ajiye a kan table ya kalleta ya yi murmushi ya ce "Afuwan na bar ki kina ta jira, bari mu ci wani abun"

Miƙewa ummi ta yi ta ce "Tafiya zan yi, ka rakani na samu abun hawa na tafi"

Cikin mamaki ya kalleta ya ce "Meyasa?"
Chapter 61 · 0% Book details