Sashe 110
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kuma da ya sake ki ki rasa ina zaki zo sai gagarawa? Garin da ki ka ce ba zaki sake zuwa ba? Amma ke dai an yi mai ƙashin tsiya, a yadda ki ke Allah ya rufa miki asiri ki auru da ƙyar ki kaso auren? Kodayeke kin gaji tsiya da rashin arzki a wurin uwarki, wallahi sai dai ki koma can wurin yahayan, ko ki koma wurin uwarki ba ki da wuri a gidan nan, ke ko kunya ma ba ki ji ba?"
Ummi ta ce "Dan Allah iya ki yi a hankali, ki rufa mini asiri ko sati na yi zan yanke shawara idan bai mayar da ni ba shikenan, ba a san ransa ya rabu da ni ba, na san zai neme ni da.....
"Dan Allah ki rufe mini baki, kin manta iskancin da ki ka din ga zubawa saboda zaki auri mai kuÉ—i? Wallahi sai kin bar gidan nan"
Kasancewar dare ne, tuni kwaroroton iya ya sanya wasu tasowa, suka taho sashin iya dan jin ba'asi.
"A daren nan fa zaki bar gidan nan"
Babar auwwalu ce ta fara roƙon iya "Haba Iya, ko korarta zaki yi, ki fara bari gari ya waye mana, a daren nan ina za ta je yanzu?"
"Ta koma in da ta fito, irin tsiyar da yarinyar nan ta shuka, idan tana da mutunci ba zata sake waiwayar gidan nan ba, ta koma in da ta fito, dama ba kowa take gani da gashi ba".
Ana tsaka da bawa iya haƙuri, ummi ta nufi ɗakin da mamanta ta zauna, da kayanta a hannu, ba tare da ta tankawa kowa ba.
Iya ta biyo ta ta riƙe ta, "Babu in da zaki je, tun da ba ɗakin uwarki bane ba yanzu, amaryar ilyasu ce a ciki yanzu, sai fa kin bar gidan nan".
Ummi ta ƙwace hannunta ta ce "Ban damu ba ko ɗakin waye, abun da na sani shi ne akwai gadon ubana a cikin gidan nan, dan haka dole a sama mini wurin zama. Tabbas yau tura ta kai bango, na gaji, na gaji Iya shekara ashirin da shida ban yi ƴanci daga ƙangi da ƙuncin da ki ka jefa ni ba, na ɗau layin da ki ke son na hau, babu ragowar mutunci ko kimar ki da nake gani a yanzu, tun tuni yakamata na yanke alaƙa da ke, saboda tsanar da ki ke yi mini da mahaifiyata, amma kullum ina duba mahaifina ki ka haifa, nake baki girmanki saboda haka. An zo kunyar ƙarshe, ba zaki taɓa canzawa ba, zan bar gidan nan amma ba a yanzu ba"
Tayi gaba ta shige É—akin amaryar kawu ilya, ta ajiye kayanta.
Daskarewa iya tayi a wurin, ummin da ko buɗe baki ba ta iya yi idan za ta yi magana, amma yau ita ta yaɓawa maganganu haka.
"Iya ki rufawa kanki asiri a ƙyale yarinyar nan zuwa safiya" suka yi ta lallaɓa iya suna ba ta haƙuri.
Ummi ta yi alwala ta yi salla, ko yunwa ba ta ji saboda baƙin ciki da tashin hankali.
Amaryar kawu Ilyasu ta rasa me za ta ce, haka ta shiga É—akin ta tarar da ummi ta haye mata kan katifa ta kwanta.
Raihan bai gaji ba, ya cigaba da kiran wayar ummi, kawai ya ga wayar a ɗakin kwanansu a ƙasan pillow.
Hankalinsa ya tashi, ya É—auki wayar ga tarin missed calls É—in sa da ya yi mata, ya ajiye wayar ya zauna, kansa yana wani irin sarawa sosai.
Gidan ya ƙara yin shiru, bayan gama hayaniya a kan ummi.
Ko kusa ko alama, bacci bai yi yinƙurin ɗaukarta ba, ta din ga tunanin ita kuwa meye laifinta haka, da kowa yake gudunta sai ka ce annoba?.
Ta tashi a hankali ta tafi tagar É—akin, ta buÉ—e tagar, wani sanyi ya daki fuskarta, ta É—aga kai tana kallon sararin samaniya, tana tuna abubuwan da suka wakana a rayuwarta.
Tabbas zamanta a gagarawa ba zai yiwu ba, akwai matsala, sai dai kan ta bar gagarawa sai ta amayar da abun da sai dai zumuncin ya watse, ta lura wannan duniyar kowa yayi ta kansa kawai, kar ka ce lallai sai ka dogara da wani, ko sai kowa ya so ka, kamar yadda raihan yake yawan gaya mata.
Ummi ta ƙara ƙaryata azancin hausawa, na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, da ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba.
Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashitna fita cikin huci.
A hankali ta furta "Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni, da masu baƙin cikin ganina cikin walwala. Tun da babu sani babu sabo.
Zan aikata abun da zuciyata ke raya mini, ko da zai yi sanadain tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa.
Raihan, tabbas ina sonka amma dole zan ɓacewa duniyarka, tun da zamana da kai barazana ne gareka da mahaifiyar ka, duk wanda ba sa buƙata ta, zan gusa daga rayuwarsu.
Yadda ta ga rana haka ta ga dare, haka ɓangaren raihan ma, tun da ta idar da sallar asuba take zaune a wurin da ta yi salla, tana tufka da warwara.
Mami tun da ta koma gida kuma ta fara fargaba da addu'a Allah ya sa kar raihan ya tona mata asiri, gashi Alhaji sai tambayarta yake yi ya aka yi ya ganta kamar mara gaskiya, ko wani abu na faruwa ta ce masa babu komai.
Ƙarfe bakwai raihan ya ɗauki mota ya tafi gidan su ummi, ya kira Abdul a waya. Mintuna kaɗan Abdul ya fito suka gaisa, Abdul ya ce "Ka zo da kanka, ai mun yi magana da ummi, ta ce ka ce na je, jira nake dama kamar ƙarfe takwas na zo na sameka".
Raihan ya ce "Abdul ba wannan ba tukuna, yanzu ina ummi take? Dama dr. Ba ya ƙasa ai ko?"
Cikin rashin fahimta ya ce "Ban gane ba, ummi kuma a gidan nan?"
"Eh, jiya ba nan ta zo ba?"
Abdul ya É—an yi shiru ya ce "Ai ni ban ga ummi a gidan nan ba"
Kamar raihan zai yi kuka ya ce "Dan Allah ka duba mini"
Abdul ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, noor tana ta shirin makaranta, ya kalleta ya ce "Noor, wai ummi ta zo gidan nan ne? Ga raihan can a waje"
Noor ta ce "Jiya ta zo, a waje muka haÉ—u ma, ta ce mini wai yaya raihan ya saketa, ina ga su maama korarta suka yi, wai ba zata zauna a gidan nan ba".
Abdul ya ce "What! Saki kuma, sai kuma a kore ta daga gidan nan? Ina ta tafi to?"
Noor ta ce "Nima ba ta gaya mini ba"
Abdul ya fita da sauri, ya tarar da raihan na ta zagaye motarsa.
Yana ganin Abdul ya ce "Yauwwa tana ciki ko? Ka ce ta zo mu tafi"
"Me ummi ta yi maka zaka saketa? Ba abu ne da za a iya sasantawa ba? Har ta kai ga saki? Ka bani kunya raihan"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ce muku ta yi na saketa? Abdul ban saketa ba"
"Ba ka sake ta ba, me ta zo yi gida?"
"Ba ta fahimci meyafaru bane? Ka tsaya ka ji, wallahi ba laifina bane ba"
Abdul ya ce "To, koma laifin waye ummi ba ta gidan nan"
"Ba ta zo ba? Ina ta tafi?"
"Ta zo, amma a jiya ta bar gidan nan ban ma san ta zo ba"
Raihan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ummi meyasa zaki yi mini haka? To ina ka ke ganin za ta tafi, ko gagarawa?"
Abdul ya ce "Bana tunanin ummi za ta je gagarawa, tun da ba shiri suke yi ba, sai dai ko maiduguri"
"Maiduguri ta tafi a daren jiya? Meyasa ta bar nan gidan? Wallahi ban sake ta ba. Dan Allah Abdul ka yi mini wani taimako mana".
"Ina jinka"
"Dan Allah kar ka gaya wa dr. Halin da ake ciki zan nemo ta, dan Allah kar ka gaya masa"
Sai tausayin raihan ya kama Abdul, lallai akwai maƙarƙashiya, sai dai ya san idan dr. Ya ji to ba raihan ba, har maama tana cikin matsala korar ummi da ta yi.
"In sha Allah ba zan gaya masa ba, zan saka a bincika gagarawa, amma ka kira wayarta?"
Raihan ya ce "Wayar a gida ta bar ta"
Abdul ya ce "In sha Allah tana nan lafiya, zan kira gagarawa ka tuntuɓa can maidugurin".
A rikice raihan ya juya ya koma mota, yana salati tare da tunanin in da ummi ta tafi.
A cikin motar ya kira Anty maryam ta can Maiduguri suka gaisa, sai dai yanayin yadda suka gaisa É—in ya tabattar masa da ummi ba ta je maiduguri ba.
Abdul kuwa da ya koma cikin gida, ya tarar mami ta fito, ya gaisheta sannan ya ce "Mami wai jiya da gaske ummi ta zo?"
"Eh" ta amsa a taƙaice.
"To tana ina?"
"Na koreta, dan ba zan riƙe bazawara har a karo biyu ba, ta koma gidan ubanta".
Ya kalli farida ya ce "Haba maama, da ki ka koreta ina za ta je, ina take da shi da ya wuce nan?"
Farida ta ce "Ta koma gidan ubanta, ko wurin uwarta ta barni na huta a gidan mijina na sake, kuma kar sake yi mini maganarta, kan ranka ya ɓaci" bai sake cewa komai ba, ya fito ya ɗau wayarsa ya kira yaya Hashim can gagarawa.
Suka gaisa sannan ya tambaye shi ko ummi ta je.