Sashe 22
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta cire kayan jikinta, ta ware gashin kanta, ta nannaɗe shi ta tufke, ta kawo tsumma da take ɗaure kan da shi, ta ɗaure yadda ba zai jiƙe ba.
Ta cire wandon da yake jikinta, subhanallah, wani irin ragargazajjen wando ne, kusan da shi gara babu, duk roba-robar jiki ta zaro, har da in da aka yi ɗinkin zare da allura a jikin phant ɗin, haka ta rataye shi a jikin ƙofar banɗaki, sai tsami yake mara daɗi.
Ta koma gefe É—aya, ba tare da ta tsuguna ba, ta fara sakin fitsarin da ya cika mata mara fam, a tunanin ta hakan zai sanya ta kaucewa faruwar abun da take gudu.
Sai dai kash! Tamkar ta zuba ruwan barkono a gabanta, wani irin raɗaɗi da azabar zafi, ya ratsata tun daga kanta har ƙafafuwanta, ta toshe bakinta tana jin zafi kamar ana kekketa mata wurin, ga mararta da ta ƙulle kan fitsarin ya fita.
Ta shafe tsawon lokaci, kan ta motsa, saboda tsananin azaba da wahalar da ta shiga.
A hankali ta motasa, ta tsuguna wani irin ƙarni mai haɗe da wari ya daki hancinta, ta ɗebo ruwan nan da sanyinsa da komai, ta zuba a wurin ta fara wankewa, wani irin ruwa mai ƙarni mara daɗi ya din ga fitowa daga jikinta. Zuba ruwan sanyin da tayi, ta ji tamkar ta zuba karara a wurin, wani irin ƙaiƙayi kamar ta kurma ihu, duk yadda ta so ta daure, ta kasa ta din ga sosawa, ƙurajen da suka feso a gabanta suka yi jawur, tun tana jin daɗin susar sai da ta koma jin zafi, dan da gask take yi iya ƙarfin ta, saboda azabar ƙaiƙayi, sai da ta yi wa kanta rauni, har da jini.
Ta yi shiru ta jingina da jikin bangon banÉ—akin tana tunanin haka kowa yake yi? Ko ita kaÉ—ai ce take fama da wannan masifar da bala'in, to idan ma haka ne wa zata tambaya?
Da ƙyar ta samu ya lafa, ta zuba ruwa a cikin ledar omon nan, ta zuba a jikinta tayi wanka, sai dai a ƙarshe ta rasa yadda za ta yi ta wanke wandonta, dan babu omo, dan haka ta wanke shi a haka, da zallar ruwa, ta yarfe shi ta mayar shi jikinta a jiƙen, ta fito daga wankan tana tafiya a hankali, tana ɗan buɗe ƙafarta, saboda raɗaɗin da wurin yake yi mata.
Man kaɗanyarta da na'ima ta aiko mata, shi ta shafa abun ta, ta sanya uniform ɗin ta, ƙungun wandon saboda rashin roba, da leda take kama wani sashin ta ɗaure, hakazalika takalminta ma, kasancewar ya mutu dan a tsinke yake, ta samu leda shi ma ta yi masa cunan leda, ta ɗaure shi da shi, ta saka.
Haka ta tafi makaranta tana kaffa-kaffa da jikinta, ko yaya ta saki jiki za a iya ganin tsiraicinta, saboda yadda kayanta suka mutu. Ga wannan bala'in da take ciki, na sanyi da yayi mata mugun kamu.
Iya kuwa hankalinsu yana kan bikin Idiris da za ayi, ana ta shirin biki a gidan, shi yaƙi karatun boko yaƙi na islamiyya, ya ce shi aure yake so, Hashim ya kaɗa ya raya, ya ce shi ba zai iya wannan wahalar banzar ba.
Kawu Yahaya ma sai da yayi mitar idiris É—in nawa yake, da har zai ce zai yi aure me yake da shi? Iya ta goya masa baya, ta ce su haÉ—u su yi masa aure.
Aka kama masa hayar wani gida mai ɗaki biyu da kitchen da banɗaki, ginin ƙasa ne dai, amma an yi floor, da plastar ƙasa an shafa farar ƙasa.
Wata yarinya ya nema a can gaban unguwarsu, yake ta yi musu sintiri yana son ta, babanta ya ce idan da gaske yake ya fito, shi ne ya zo ya saka Iya a gaba, lallai shi aure yake so, aka je aka nema masa auren Æ´ar mai suna Hindu.
Kawu yahaya ya ce lokacin auren, yayi dai-dai da lokacin zuwansa umara, ba zai samu zuwa ba sai dai matarsa za ta zo, ya kuma aika musu da gudunmawa mai tsoka.
Albarkacin bikin Idiris, Iya ta sayawa ummi atamfa, da takalmi na kayan fitar biki, ummi duk da ba shiri suke yi da idiris ba, ta ji dadin zai yi aure ya bar gidan ko ta samu ta sarara.
Ana ta shirye shiryen biki, gida ya É—au harama, Æ´an uwa na nesa tuni sun fara zuwa, ummi na ta aiki kamar jaka, É—an wannan idan yayi kuka a bata rarrashi, É—an wancan yayi kashi ta wanke, haka dai ba ta da sukuni.
Yau kusan tun bayan azahar, yanayi ya nuna akwai matsala, duba da yadda Iya ke ta shiga tana fita ita da mahaifin su magaji, kasancewar ba abun da ya shafi ummi bane, ya sanya ko a jikinta, ta cigaba da sabgoginta.
Shi kansa yanayin Idirs ya nuna hankalinsa a matuƙar tashe yake, alamu suka tabattar da akwai matsala.
Ba a tsaya da shirye-shiryen biki ba, dan magana ake ta bai fi saura kwana huÉ—u a shiga hidimar biki ba.
Da yamma hashim ya shigo, ya tarar ummi na cikin mutane ana ta aiki, yayi mata nuni da ta zo.
Ta wanke hannunta ta bi shi, ya kalleta ya ce "Ke ina naki shirin bukin, ki ke ta fama da aiki haka, ko gajiya ba kya yi?"
Murmushi ta yi masa, sai da fararen haƙoranta suka haska fuskarta, fiƙarta da ta karye tana nan a yadda take, sai ƴar siriryar wushiryarta ta ce "To yaya magaji wani shiri zan yi? Ina da atamfata sabuwa da takalmin da zan saka"
"Ke ba zaki yi É—an lallen da ake yi na zamani ba?"
Ta kalli hannunta, ta É—an rausayar da kai ta ce "Bana so, ba zai yi mini kyau ba"
Ya kamo hannunta ya ce "Jan nan da ake yi tafin hannunki fari ne masha Allah, ko kitson ma ba ayi miki ba, kin cukurkuÉ—e gashi kin É—aure"
Yayi maganar yana kallon yadda É—ankwalin kanta yake cike fam, ko ba a gaya maka ba, ka san wannan uban gashin nata ta É—aure.
"Ai ka san ni ba a iya yi mini kitso, duk sanda na cewa yayi mini kitso, sai ya ce wai bs zai iya ba kaina ba zai yi ba, lalle kuma ai sai an biya ɗari biyu huwaila take yi hannu da ƙafa" tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa da Iya take cewa sangarta.
Ya ce "To shikenan, da safe zan baki kuÉ—in lallen, kitson kuma sai na yi miki"
Tayi dariya ta ce "To mata ne kawai suke yi wa mata kitso ban da maza"
Ya ce "Shikenan, je ki sai goben in Allah ya kaimu"
Cikin murna ta tafi ta cigaba da aikin, tana matuƙar son lalle, amma rabon da ayi mata, tun kan na'ima tayi aure, da take yi musu, yanzu yaran na'ima biyu a gidan miji.
Da magariba Saminu baban su Idris ya shigo hankali a tashe ya ja hannun Iya suka fita, wata duhuwa ya ja ta ya ce "Iya muna cikin tashin hankali da masifa, Idris ya zubar mana da mutunci"
Cikin kaÉ—uwa ta ce "Menene? Meyafaru?"
"Ban da masifa da bala'i, saura Æ´an kwanaki a É—aura maka aure, a ganka kana watsewa da wata, saboda rashin mutunci"
Iya ta ce "To ba mun gama wannan maganar ba? Har wurin maude mai babban carbi na je, ya yi mini aiki ya ce maganar an bar ta har abada, ba zata fasu ba, ko ta fasun ne?"
"To yanzun nan ƙanin baban yarinyar da zai aura ɗin, ya dawo da kuɗin auren, sun ce aje a karɓi kayan auren gobe da safe, ba za su bawa mutumin banza ƴa ba" yayi maganar yana nuna mata kuɗin.
Iya ta dafe ƙirji ta ce "Mun shiga uku, amma mutanen nan basu da mutunci, basu san tsautsayi ba?"
"Koma menene ai shi ya janyo wa kansa, da bai yi ba wa zai ce yayi, ni wannan mutanen da muka tara ne, ban san ya zamu yi da su ba"
Iya ta ce "Ni kuma tashin hankalina, garin Allah ya waye a dawo da kayan nan, kowa ya ji abun da ya faru, da sassafe ka je da kanka ka karɓo kayan, ka kai mini gidan kuluwa".
"Ni kuma Iya? Ni zan je É—aukko kayan?"
"To kar ka je tsaya asirinmu ya tonu, sai ka ji daÉ—i, santolo kawai".
"To Shikenan zan je in sha Allah "
"Kai ka ga idan da hali, ka tafi yanzu cikin daren nan, ka tafi da babur ba wanda ya ji balle ya gani"
"To bari sahu ya ƙara ɗaukewa, amma Iya yaya zamu yi da wannan mutanen, ta yaya zamu ce musu an fasa auren nan?"
Iya ta ce "Nima shi nake tunani, dama ga akuyarsa tayi kuka a dangi, dan ma ana tsoro na ne, ya sanya ba a magana, amma jeka na san abun yi "
"Meye abun yin to?"
"Ka tafi na ce, idan ka dawo sai ka ji" ya jinjina mata kai ya tafi.
ÆŠakin samarin ta shiga, neman Idris, amma ba ta tarar da shi ba, dan haka ta juya ta tafi.
A daren saminu yayi yadda Iya ta ce, ya je ya karɓo kayan a daren.
Sosai Saminu, ya din ga yi wa idiris faÉ—a, a kan tashin hankalin da ya sanya su a ciki.
Washegari kamar yadda Hashim ya yi wa ummi alƙawari, ya bata kuɗi ta je aka yi mata lalle.
A ƙofar gida ta gan shi ya karɓo kayan guga, tun daga nesa take ɗaga masa hannu ta ce "Yaya ka ga lalle na?"
Yayi murmushi ya ce "Inyee an sha kyau, lalle yayi kyau, ki yi sauri ki shiga gida, Iya ta fara faɗa ana nemanki"
Cikin faÉ—uwar gaba ummi, ta ce "Bari na yi sauri" ta yi cikin gida da gudu.
Cikin damuwa Saminu ya kalli Iya ya ce "Iya kina ganin babu matsala, ba fa son yarinyar nan yake yi ba, kuma shekarar ta goma sha uku ne kawai"
"To yaya ka ke son mu yi? Asirinmu da nasa ya tonu, idan ba haka ba kawo wata mafitar"
Ya girgiza kai ya ce "Ba ni da wata mafitar".