Sashe 113
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kar ka damu, akwai isashshen kuÉ—i a hannuna".
Ana idar da sallar asuba, Ummi ta ɗebi kayanta ta bar gidan iya, sai dai ba ta bar gagarawa ba sai da ta je ta shigar da ƙara a kotu, sannan ta tafi gidan magaji da ba a cikin gagarawa yake ba.
Ko da magaji ya dawo ummi ta kwashe komai ta gaya masa, sai dai ya ji zafin kora da wulaƙanci da Iya ta yi mata, sai dai ba ta gaya masa batun kai ƙara kotu ba, dan haka da ya je gagarawa bai nuna musu ya san meyafaru ba.
Sai dai tun da ya ji ta'asar da Iya ta aikata, ya kasa komawa gidansa, saboda damuwa da fargaba, ya kasa komawa gidansa ya kalli ummi, ashe duk tsawon lokacin nan kallon da take yi masa kenan?.
Ganin ba shi da wani zaɓi, ya sanya ya koma gidan, ya tarar da ummi da matarsa suna hira.
Kamar baƙon munafiki haka yayi sallama idonsa yayi jawur.
Ummi ta ce "Yaya menene? Wani abun suka yi maka?"
Ya girgiza kai ya ce "Ashe kin kai ƙara kotu?"
Ummi ta ce "Eh, dama ina son zan yi maka bayani, na san zaka fuskance ni"
Ya ƙarasa gaban ummi ya zube a kan gwiwoyinsa, sai ga hawaye ya ce "Wallahi! wallahi! wallahi ummi ban aikata abun da Iya ta gaya miki ba, bani bane ba ummi, ban taɓa sanin abun da ta gaya miki ba kenan, dama da abun ki ke kallona? Wallahi ummi Idris ne, nima ban san an yi ba sai lokacin da za ta yi miki auren huce takaici da shi, na nuna mata illar yin hakan, saboda kina da ƙananan shekaru kuma ba ya ƙaunar ki, amma ta gaya mini ga abun da ya faru shekarun baya, aurensa shi ne rufin asirin ki, wanda a kan haka sai da ta haɗa ni da babanmu kamar zai tsine mini, kuma still bayan auren da ya zo yana faɗar maganganu a kan an bashi ragowa na tuna masa koma menene shi ya fara, ya je ya gaya wa Iya ta sake ci mini mutunci da barazanar na sake ɗaga maganar sai ta tsine mini, ina ji ina gani yayi ta yamaɗiɗin ragowa aka bashi ke, ga kuma larura kina da ita, ba yadda na iya, amma ko Alqur'ani aka bani zan rantse wallahi ummi bani bane ba"
Ummi cikin sheshsheƙa ta ce "Ka yi haƙuri yaya magaji, nima zuciyata ta daɗe tana yi mini wasi-wasi a kan hakan, amma ba yadda na iya tura ta kai bango, na gaji da abun da Iya take yi wa rayuwata, shiyasa na zaɓi fesar da abun da yake zuciyata ko da kuwa zumuncin zai tarwatse. An cutar da ni da yawa me nayi da na cancanci haka yaya magaji?"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ummi ba zan hana ki ba, ba zan dakatar da ke ba, Iya ita ta rusa duk wani tubalin soyayya da ƙauna da tarwatsa kan iyalanta, ta hanyar fifita wasu a kan wasu saboda zunzurutun tsagwaron son zuciya da abun duniya, ta yi miki CUTARWA ma fi muni wallahi kowane mataki zaki ɗauka ba ruwana, ni dai ki yafe mini wallahi bani bane ba"
Ummi ta share hawaye ta ce "Ni yakamata na nemi yafiyarka yaya, amma ba zan ɓoye maka ba har iyayenmu dr. Kawai na cire amma suna kallon yadda rayuwata ta wulaƙanta cikinsu ɗaya da mahaifina saboda bai mutu ya bar mini komai ba, aka rasa wanda zai kula da rayuwata, aishikenan"
Cikin sanyin jiki matar magaji ta ce "Ummi abun da haƙuri bai bayar ba, akasin ba zai bayar ba ki yi haƙuri ki yafe musu mana"
Ummi ta ce "Ai da fari na yafe musun, sai na ga idan ba rayuwata ce ta ƙare ba, ba za a daina cutar da ni ba. Mijina yana yawan gaya mini in tsaya da ƙafata a rayuwa in fuskanci kowane irin ƙalubale".
Yayi nisa a zurfin tunani, ya ji ana bugun ƙofar falo kamar za a karyata, babu shiri ya tashi ya je ya buɗe a fusace, sai dai ganin Mami a tsaye ya sanya shi haɗiye masifar da ya ƙunso ya saukewa mai bugawar.
"Raihan, meye haka? Amai da gudawa ka yi ne kayi wannan mummunar ramar?" Ya girgiza mata kai tare da shigewa falon.
Ta bi bayansa, tana ƙare masa kallo.
"Ya aka yi na je office ba ka je ba? Me ka ke yi a gida?".
"Mami ba a san fa in da Ummi take ba"
"Shi ne me? Ƙaramar yarinya ce ita? Saboda haka ne nake ta kiranka a waya kashe wayoyinka?"
Yayi shiru bai ce komai ba.
"Alhaji yana nemanka, za ku yi magana a kan kai kuɗin Safiyya, kuma a yau ba sai gobe ba, ka je ka ji me take buƙata na shirin biki, kuma idan ka kuskura ya san na saka ka saketa sai na yi mummunan ɓata maka rai" bai ko ɗaga kansa ba, balle ya tanka mata, tayi ta gama ta tafi.
Me zai yi da wata safiyya? Ya tuna yadda take yawo da wani ɗagaggen mayafi tana gantsare-gantsare kamar an banƙare kaza, gaba ɗaya baya ganin kyan kowa idan ba Salmansa ba.
Bai san lokacin da ya ja wani guntun tsaki ba.
Gaba ɗaya gidan yayi ƙura saboda ba ummi, ya tara wanke-wanke a kitchen, da ƙyar yake iya yi. Daga baya ma sai dai ya sayo fruita ya ci duk ya zubar a wurin.
Yayi wanka ya shirya ya je gida ya samu Alhaji.
Shi kansa sai da ya tambayi raihan ko ba shi da lafiya ne? Ya ce masa lafiyarsa ƙalau.
"To kai babarka ta ce wannan juma'ar kai kuÉ—in aure, ni ban ganka ba. Ka zo ka kawo mini kuÉ—in, da sauran shirye-shirye amma ba ka ce komai ba, na san ba so ka ke yi ba amma ka daure ka yi mata biyayya".
Raihan kamar zai yi kuka ya ce "Ni fa bani da kuÉ—i"
Alhaji ya ce "Kai babban mutum, ba ka da kuÉ—i kuma? A auren Salma ne ka ke da kuÉ—i kenan?" Yayi shiru.
Alhaji ya kira mami a waya, ta zo ta same su, ya sanar mata raihan ya ce ba shi da kuɗin ƙara aure a yanzu.
Mami ta ce "Duk dan ya kaucewa umarnina ne, ni ina da kuÉ—in zan bashi"
Alhaji ya ce "Dakata tukuna, me za a yi wa ƴa ta wanda zai kwantar mata da hankali? Ba zai yiwu watanni takwas da yin aure, ba dan ta gaza ta ko ina ba ace za a ƙara mata kishiya ba tare da yi mata wani abu da zai kwantar mata da hankali ba".
"Alhaji me kuma za ayi mata? Ta ci nata rabon ai"
Alhaji ya katse ta da cewa "Da ki ka hana ayi mata lefen sai ta ɓarauniyar hanya ya yi mata? Ke ma da ban bayar da kayan faɗar kishiya ba, duk da Hajiya na da haƙuri, da ba ki shigo ta daɗin rai ba, gara ita ta daɗe na aure ki? Wannan fa?. Na gargaɗe ki kar ki yi abun da zaki zo ki na dana sani, amma kin ƙi. Kar ku jefa yarinya a halaka ƙiyayyar ɗa namiji masifa ce, kin ƙi ai shikenan"
Ta ɓata fuska ta ce "Ba wata ƙiyayya, iskanci ne kawai da kuma asiri da yake ɗawainiya da shi"
Alhaji ya kalli raihan ya yi murmushi ya ce "Ba wani asiri, ta iya kiwo ne kawai, ke ba abun alfaharinki bane a. Mallake É—anki ana kula da shi, nan ya zo ana bani labarin hannunta akwai maggi, ta iya girki, nima shaida ne ta iya girki. Dan haka ko dai a samu wadda ta fita ko kai É—aya da ita idan ana son zaman lafiya, amma shawara ce na bayar. Babban mutum, me zaka bawa ummi da zaka kwantar mata da hankali?" Raihan ya ji kamar Alhaji yana shiga zuciyarsa yana karanto damuwarsa ne.
"Alhaji ban san kan abun ba, ban san me ake bayarwa ba".
"Eh to, ka ga recently kun fita waje, amma wannan cikin honeymoon É—inku ne, kyauta zaka yi mata ta bajinta, ka gane me nake nufi ai kyauta mai sunan kyauta.
A samu danƙareriyar mota a bata, idan da hali gidan da ke ciki a bata takardunsa, ita amaryar sai a nema mata haya a wani wurin, gidan ya zamana nata ne"
Cikin tashin hankali mami ta zabura ta ce "Alhaji wannan kyautar ai sai kai? Idan ya bata gidansa shi shikenan ko oho? Wai meyasa kamar goya masa baya ka ke yi ya bujire mini ne?"
"Yanzu ya ce ba shi da kuɗin aure kin ce zaki bashi, ita wannan saboda ba ƴar ki ba ce ba, kin hana a bata kyauta, ta samu kwanciyar hankali, ba zan so raihan ya rabu da gidansa ba, amma muddin kina so na tsaya yadda yakamata ya ƙara aure, sai an yi balancing, tun da ba shi da kuɗi, ke ki biya masa kuɗi yayi aure, ni kuma zan yi mata kyautar da zata sanya hankalinta ya ɗan kwanta ya rage mata zafin kishi". Raihan yayi murmushi ya ce "Alhaji na gode sosai da sosai"
"Wallahi ba zai yiwu ba, ƙarya yake yi yana da kuɗi, kuma sai ka fito da su"
"To ya rage naku dai, ni dai idan aka yi wa Ummi kishiya, in sha Allah zan yi mata kyautar ban mamaki, sirikata ba ta yi laifin komai ba, marainiyar Allah ba zan bari a cutar da ita ba"
Duk maganar da yake yi, yana observing É—in raihan da ita kanta mamin, dan yana sane yake faÉ—ar wasu abubuwan.
Ya sake nisawa ya ce "To duk kun yi shiru, kai babban mutum ka fito da kuÉ—i mana, kuÉ—i fa akwai su"
Raihan ya karkace kai ya ce "Dan Allah Alhaji a bar maganar auren nan yanzu, nifa ba ni da lafiya ma"
Gaba É—aya suka kalle shi.
Mami ta ce "Kamar yaya ba ka da lafiya?".
Ya ce "Ba zan iya ƙara aure ba, a bari na nemi magani" ya bata amsa kansa tsaye.
Alhaji ya sunkuyar da kai kamar ya kece da dariya, raihan ba saiti wasu lokutan.
Ya maze ya ce "me yake damunka?"