Sashe 30
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin taƙi magana, ya sanya likitan tura su wurin wata nurse, tun da mace ce, za ta fi iya sakin jiki tayi mata bayani.
Sai dai ba ta sauya zani ba, nan ma ummi kasa magana ta yi.
Nurse ɗin ta kalli kawu yahaya ta ce "Yallaɓai me yake damunta ne? Ta ƙi magana".
Ya ce "Kina ji ƴa ta ce wannan, a ƙauye take hannun mahaifiyarmu, aka yi mata aure na je na tarar da matsala mijin ya ce ba ta da lafiya, sanyi yayi mata yawa, auren ma dai ya mutu"
Nurse ɗin ta kalli ummi sannan ta kalle shi ta ce "Bawan Allah kai gaka wayayye, ya zaka bari a yi wa wannan yarinyar ƙarama aure a yanzu, kalli fuskarta ma kamar shaidar duka, ni wannan yarinyar ai ba ta fi in saka zani in goye ta ba".
Ganin za ta fara yi masa faÉ—a, saboda yadda ta É—au zafi, ya sanya ya yi mata bayanin komai.
Jikinta duk yayi sanyi, tana jinjina lamarin, gaba ɗaya tausayin ummi ya kamata, wannan ƴar ƙaramar yarinyar ita ce aka yi wa aure, har ya mutu.
Ta kalli ummi ta ce "Gaya mini menene yake damunki a wurin?" Ummi ta sunkuyar da kai tare da jin ta a takure.
Ta kalli kawu yahaya ta ce "ÆŠan bamu wuri" ba musu ya fita waje.
Ta haÉ—e rai ta kalli ummi ta ce "Ke dan gidanku ki gaya mini nan asibiti ne, idan baki warke ba haka zaki yi ta aure yana mutuwa, saboda wannan matsalar".
Ummi murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ƙaiƙayi yake yi mini".
"Tun yaushe?"
"An daÉ—e"
"Ya aka yi aka daÉ—e, wasa ki ke da wurin?"
Ummi ta girgiza kai alamar a'a.
"To ya aka yi yake ƙaiƙayi, kafin ayi miki auren ya fara ko bayan an yi mikk auren?"
"Kafin ayi mini ne?"
Nurse É—in ta numfasa ta ce "Sau nawa ki ke canza wando a rana?"
Ummi ta kalleta ta ce "Kan ayi mini?"
Auren ne ba zata iya faÉ—a ba, tana jin nauyin haka.
Ta ce "Eh, kan ayi auren"
"Wandona É—aya ne, idan na wanke sai na saka"
Tayi ƙuri da ido tana kallon ummi, da ta ji ta ce wando ɗaya.
"Yaya ki ke tsarki?"
Amsar da ta bawa nurse ɗin ta girgiza ta, dan ciwon sanyin ummi, yana da alaƙa da rashin iya tsarki, da tsugunawa a banɗaki barkatai, da kuma rashin kyakywar kulawa na uwa da wurin bai samu ba.
Ta dubi ummi ta ce "Daga yanzu, wando sau uku zaki din ga canzawa a rana, kuma idan ki ka yi bayan gida, sai kin fara wanke wurin fitsarinki, sannan ki wanke wurin bayan gida, ba haÉ—e tsarkinsu.
Kar ki kuskura ki yi fitsari kina ɗigar da ruwan tsarkin, ki mayar da wando jikin ki, ko ki saka jiƙaƙƙen wando, ki samu ɗan tsumma mai kyau, ki din ga wankewa kina ajiyewa a banɗakin da ki ke, idan kin yi tsarki, ko kin yi wanka, ki din ga tsane wurin kan ki saka wando.
Idan fitsari ya kama ki a wani wuri daban ba gida ba, ki yi fitsarin a tsaye, idan kin gama sai ki wanke ƙafarki, da jikinki, ki daina shiga banɗaki barkatai" ta din ga yi wa ummi bayanin yadda za ta din ga kula da tsabtar wurin, dan babu wanda ya taɓa zaunar da ita yayi mata wannan bayanin.
"Kin fara al'ada ne?"
Ummi ta ce "A'a"
Nurse ɗin ta a aika ummi ta kira kawu yahaya, ta ce masa "Yallaɓai gaskiya sanyi ya yi mata yawa, kuma na lura rashin tsabta da kula ne ya haddasa mata hakan, dan haka dole ku kula, tun da yanzu ka ce ta dawo hannunka. Ku dawo ranar lahadi akwai gynea doctor ɗin da yake zama, sai ka kawota ta ganshi.
Na so ace da mace ku ka zo, sai ta fi fahimtar bayanina, amma kai ɗin ba ta ɓaci ba, ai uba ne kai. A yanzu, abu na farko a sama mata isasshen wanduna, a ƙalla shida zuwa dozen. Sai kuma a sama mata flask mussaman na ruwan zafi, na ta ne ta din ga kama ruwa da ruwan ɗumi.
Banda tsarki da sabulu, a samo mata ganyen magarya, a tafasa shi ta din ga kama ruwa da shi.
Kuma ka san shi ciwo ne mai naci, dan haka a kula sosai, sai kuma ku nemi kanumfari, tafarnuwa ba mai yawa ba, da namijin goro, a jiƙa su a robar ruwa mai murfi, ta din ga tsiyaya tana sha, ta yawaita amfani da kanumfarin nan.
Sai kuma a samo saiwar zogale a din ga tafasa mata da jar kanwa, ta yi amfani da ko guda ɗaya kafin ku zo ku ga likitan, zata samu sauƙi in sha Allah. Wannan na ɗan gaya muku ne dabarunmu na cikin gida na gargajiya, kafin Allah ya sa ku zo ganin likitan".
Ya ce "To shikenan, na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da alkhairi"
Ummi ta bi bayansa suka fito, suna tafe a hanya yana jaddada da mata ta riƙe abubuwan da aka gaya mata, ummi kuwa gaba ɗaya jikinta sanyi yayi, wata irin kunyarsa ta rufe ta.
Shi kansa yayi mamaki da nurse É—in ta ce masa ummi ta ce wando É—aya ne da ita.
"Ummi"
Ta amsa da"Na'am"
"Ki kwantar da hankalinki, magnunnan nan zan saya miki zuwa gobe in Allah ya kaimu, har kayan da zaki yi amfani da su, duk zan yi miki har makaranta zan mayar da ke da yardar Allah, ke dai ki nutsu ki manta da komai, ban yi miki alƙawarin gidana babu ƙalubale ba, amma na san bai kai na ƙauye ba. Ki dage ki yi amfani da shawararin da ta baki kin ji ummana"
Ta ce "To na gode sosai"
Ya shafa kanta ya ce "Yauwwa Allah yayi miki albarka"
Can gagarawa kuwa, Hashim ya sha zagi da cin mutunci da wulaƙanci a wurin Iya, ba Iya kawai ba, har da mahaifinsa suka ƙare masa tas, a kan ya kasa rufa wa ɗan uwansa asiri, da har ya iya sanar da kawu yahaya halin da ake ciki.
Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, amma har cikin ransa yake jin wannan abun da yayi shine mafita ga rayuwar ummi, kuma hakan da yayi bai saɓawa shari'a ba.
Sirikan iya wasu sun jiye wa ummi rabata da gidan nan, saboda azaba da masifar iya ga ummi.
Iya kuwa ta ji baƙin ciki da takaicin ɗauke ummi da yahaya yayi, dan yanzu ta san abu ne mawuyaci idan asirinsu da take ta ƙoƙarin rufuwa bai tonu ba.
Shi kansa Idris tun da aka tafi da ummi, bai dawo gidan ba, dan ya san zai sha faÉ—a a wurin Iya da iyayensa, shi kuma har ga Allah, ya tsani yarinyar nan hakan da yayi shine dai-dai.
Horn yayi, wani matashin yaro, da zai É—an girmi ummi ya zo ya buÉ—e gate É—in, ummi ta san yaron amma da daÉ—ewa dan wasu lokutan ya kan zo da shi gagarawa.
Ya shiga da motar harabar gidan, ba laifi harabar mai ɗan girma ce, dan aƙalla za a yi parking ɗin motoci uku a ciki.
Wasu ƴan mata ne ƙanana su biyu farare tas da su, an yi musu kitson ƙari, ɗaya tafi ɗaya girma, suka nufo motar suna faɗin oyoyo Abba.
Ya buÉ—e motar ya fita ya rungumo su, sannan ya juya ya buÉ—e wa ummi motar ta fito.
Duk da duhun magariba ya fara yi, hasken fitilar da take harabar gidan, ta basu damar tsayawa suna ƙarewa ummi kallo.
Ya buÉ—e bayan motarsa ya cewa yaran su É—aukko wa ummi kayanta.
Ba laifi gidan mai kyau da shi, ummi sai kallon gidan take yi.
A falo ya kalli yaran ya ce "Intee ina maama ne?".
"Ta fita da muka dawo daga tahfee, bamu tarar da ita ba"
Ya ce "Ok, ga sister É—inku nan, sunan ta Salma, amma ummi ake ce mata, you can call her yaya ummi, ku nuna mata toilet É—in ku ta yi alwala".
Cikin ƙyama intee ta bi ummi da kallo, sannan ta yi gaba, ummi ta bita a baya.
Ummi ta yi salla ta idar, tana ta kallon ɗakin, da gani na ƴan matan ne, kowacce da gadonta, ga ƙatuwar wardrobe, ga shoe rack ɗin su ɗauke da takalmansu na makaranta da na fita, duka-duka babbar da ake kira da intee ba ta fi shekara goma ba, ɗayar kuma bakwai.
Ummi ta fito daga ɗakin, ta koma falo ta zauna a ƙasa.
Ya shiga kitchen da kansa, ya haɗowa ummi tea mai kauri, ya saka intee ta dafawa ummi noodles ta ɗora mata ƙwai uku a kai.
Duk da yanayi na rashin lafiya, ummi ta ɗan ci, dan bata taɓa cin indomie ba, duk da ta na burgeta.
Yaran suka kunna tv suna kallo tare da mahaifinsu, ummi ma kallon take yi, suna ta yi wa babansu surutu, yana ta ƙoƙarin saka ummi a hirar, ta dai yi shiru ba ta cewa komai.
Bayan magariba sosai sannan wata mata tayi sallama, ita da wata matashiyar budurwa.
Ya amsa ya É—aga kai yana kallonsu, yaran kuma duk suka tashi suka nufeta.
Cikin iyayi ta ce "Abba ka dawo kenan?" Tayi maganar tana zama da tsohon cikinta.
"Eh" ya amsa mata a taƙaice.
Ummi ta kalleta ta ce "Ina wuni?"
Ta bi ummi da kallo, ta ce "wannan fa?"
Ya ce "Ki fara amsa mata gaisuwar mana"
"Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan yatsune.
Ya kalli su inteesar ya ce "Abdul, intee, shalele ku bi anty rahama maza, ummi ki bisu ki samu ki huta, a haɗa mata ruwa tayi wanka"
"Wai ban gane ba, ita wannan É—in wacece?"
Ya ce "Kya tsaya na yi miki bayani ai, yanzu dai daga ina ki ke?".
"Gidan gana na je, wata Æ´ar aikin nake so ta samo mini, saboda su intee wahala tana yi mini yawa".
"Amma ba kwanan nan ki ka rabu da wata ba, kina ta surutun tayi miki laifuka ba, shi ne zaki sake rakito wata?".
"To Abba yaya zan yi? Ga tsohon ciki, da na haihu zan koma school, ga ayyukan gida ba zan iya ba wallahi. Ka yi haƙuri kawai ni dai".