Sashe 45
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakazalika ta na ta shirye-shiryen haÉ—a saukarta ta biyu, domin kuwa bayan ta yi sauka ta cigaba da zuwa makaranta, Æ´an ajinsu galibi duk sun yi aure, dama duk sun girme mata.
Wuri É—aya ta samu ta zauna a ajin, jikin window ne in da take, hakan ya bata damar kallon shige da ficen É—alibai, tsofaffi wanda sun kusa fita ma, da masu rawar kai wanda yanzu suka shigo jami'a.
Shigowar wani babban mutum ajin ne ya sanya É—aliban ajin nutsuwa, tare da gaida mutumin.
Ya amsa musu, tare da gabatar da kansa a matsayin HOD É—in su, ya nemi da kowanne daga cikin É—aliban, ya tashi ya gabatar da sunansa da kuma garin da yake.
Haka nan gaban ummi ya faÉ—i, dan kuwa ba ta son mutane, da duk wani dalili da zai sanya a takurata da kallo.
ÆŠalibai suka din ga gabatar da kansu É—aya bayan É—aya, kan azo kan ummi gaba É—aya jikinta yayi sanyi, sai wata irin fargaba take yi.
Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye, fuskarta sanye da facemask, malamin yayi mata alama da ta sauke facemask ɗin.
Gabanta ya sake faɗuwa a karo na biyu, hannunta har rawa yake yi, ta sauke facemask ɗin tana jiran jin ƙanan magana kamar yadda ta saba, sai dai ba ta ji hakan ba.
Sai dai ta kasa magana, sai da ta ɗan sauke numfashi, sannan ta ce "My name is.... Sai dai ta kasa ƙarasawa, saboda yadda gaba ɗaliban suka juyo suna kallonta.
Ummi na da murya mai matuƙar ɗaukar hankali, duk wanda bai santa ba, idan har tayi magana dole zai waiwaya domin ganin mai muryar.
Ko a islamiyya idan ana musaffa, Alla-Alla suke yi a zo kan ummi, saboda ta iya ƙira'a mai daɗin sauraro.
Ganin ta diririce saboda kallon da ake yi mata ne ya sanya malamin takowa zuwa gabanta, ta ko ƙara sunkuyar da kanta ƙasa, tare da wasa da yatsun hannunta a cikin hijjabinta.
"Kin manta sunan naki ne?" Ta girgiza masa kai.
Ya sake cewa "Ko ba turanci ne?" Nan ma ta sake girgiza masa kai.
"Oya ya sunanki?"
"Salma Muhammad Bashir"
Yayi murmushi ya ce "What a beautiful name, na ga duk a tsorace ki ke, but mark you, this is university idan malamai suka gane kina jin tsoron magana a public, za su yi ta takura miki da tambaya, ke kina jin tsoron amma ki ka zaɓi aikin jarida? Ai harkar jarida na masu baki ne. But you can do it when you overcome your fear"
Ta É—ago a hankali ta ce "Thank you sir"
"Ƴar wace ƙasar ce ke?"
"Jigawa" tayi maganar muryarta na É—an rawa.
"Ƙasa fa"
Ta ce "Au Nigeria"
"Are you sure? Ko dai ta ɓarauniyar hanya ki ka shigo mana ƙasa? Kin yi kama da baƙaƙen larabawan Afrika"
Ummi a ranta ta ce 'Amma kuwa an cuci larabawa, ko kuma ni aka cuta, maybe ba'a yake yi mini'
Ƴan ajin kuwa dariya suka hau yi, ya ce "Kalar idonta da complexion ɗin ta, ba irin na ƴan Nigeria bane, dan haka zamu bincika idan baki da lasisin zama a Nigeria mu mayar da ke ƙasarku" yayi maganar cikin zolaya.
A dole ummi ta ƙaƙalo murmushi.
Ya ce "Yi zamanki, Allah ya yi albarka" kan ta zauna ta risuna ta ce "Na gode sosai Allah ya jiƙan magabata" ya ɗan ƙurawa ummi ido, yadda take amsa masa magana ma, kawai ya isa ka gane tana da tarbiyya sosai. Ya ce "Amin" sannan ya suce gaba.
Yayi musu nasiha sosai da sosai, a kan kula da ilimi da kuma tarbiyarsu, da ba su shawarar su riƙe addinansu, kar su lalace saboda kawai sun ga sun shiga jami'a.
Kowa harkarsa yake ba ruwan wani da wani, dan haka ummi ta ji daÉ—in hakan, da babu wanda ya matseta balle ya takura mata.
Baki har kunne ta koma gida tana murna, duk da tana zuwa gidan ta tarar da uban kwanukan wanke-wanke, da wankin kaya, kuma an cinye abinci tas, kuma ana jiran ta É—ora na dare.
Hijjabi kawai ta canza ta hau aiki, noor ta din ga bin ta, tana tambayarta "Anty, kin yi magana a gidan radiyon?"
Ummi ta ce "A'a mamana, sai an kwana biyu tukuna"
"To ta ina zaki din ga shiga radion kiyi magana?"
Sai dare yayi kin yi bacci, zan buÉ—e gurin batirin in shiga ta ciki.
Noor ta buÉ—e baki cikin mamaki, sannan ta ce "To zaki shiga da ni nima?"
"Sai kin ƙara girma sosai tukuna, noor ta dinga tsalle tana murna.
***
"Bilki, ki kira Bauchi ki gaya musu ba fa haka muka yi da su ba, ni fa ba bar musu ɗa na na yi ba, haba sun riƙe mini ɗa ko leƙo ni baya yi".
Ta kalleshi ta ce "Taɓ, ba ruwana kun fi kusa, ka kira su ka gaya musu mana"
Yayi murmushi ya ce "Shima zan gamu da shi ne, ko a waya baya nema na"
Ta É—an yi murmushi ta ce "Wai É—azu da ina bacci, da wa ka ke magana ne, ka ke ta faÉ—a?"
Ya É—an ja guntun tsaki ya ce "Salim mana, wai zuwa yayi na bashi kuÉ—i zai yi gyaran mota".
"To meyasa ba ka bashi ba?"
"A kan me zan bashi? Duk iya ƙoƙarin da zan yi na yi wa yaran nan, dan su zama na gari, amma abu ya gagara. Yanzu daga shi har ɗan uwansa da a nutse suke, da yanzu yaushe zan din ga wannan zirga-zirgar?"
Bilki ta ɗan yi ajiyar zuciya ta taɓe baki ta ce "Laifin babarsu ne, da ta bari suka lalace".
Yayi saurin girgiza kai ya ce "No, Hajiya na iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar yara, dan har ta fiki tsanantawa ma wasu lokutan"
Ta tsuke fuska ta ce "Eh, nice mai sake da tarbiyya kenan?"
"A'a mai gado ba haka nake nufi ba, ai kin ga matan duk lafiya ƙalau, gashi duk sun yi aurensu suna zaune lafiya, su ɗin ne dai, kuma shima na san jarrabawa ce, ba a barin ɗan Adam haka".
"Allah ya kyauta, amma nikam ba zan bari auta ya riƙa ba yazo na kasa contrilling ɗin sa ba, aure zan yi masa yana dawowa"
"To hakan ma yana da kyau, Allah ya zaɓa abun da ya fi alkhairi mai gadon zinari" yayi maganar yana jan hancinta.
"Ba wata mai gadon zinari, ka koma wurin dattijuwar matarka"
Kwashewa yayi da dariya, ya ce "Bilkisu, hajiyan ce dattijuwa Allah ya sa ta ji ki, ai shekarunta ba sa nunawa, saboda gayunta, kuma ni bana ganin girmanta, ba ta fi fifty fihe ba, amma idan ta É—aura É—ankwali kamar Æ´ar 30yrs. Ai da yake ni na mayar da ita tsohuwar, ganinta nake kamar Æ´ar 16 lokacin da na aurota, hajiya ba ta tsufa"
Wani irin haushi ya kama bilkisu, ta yinƙura za ta tashi ta bar masa wurin, ya riƙeta yana dariya ya ce "Danne kishin nan kar ki bari ya fito".
Alhaji Tahir kenan, tsohon É—an boko, kuma babban É—an kasuwa, da yake juya naira yadda yake so.
Mutum ne mai sauƙin kai da matuƙar son iyalinsa, mussaman ƴaƴansa, dan mutum ne mai biyewa ra'ayin yaransa, duk abun da suke so muddin bai saɓawa addini ba, zai yi musu shi, yana bawa iyalansa ƴancin yin abun da suke so, ba tare da ya takaura musu ba.
***
Rashin wayar hannu, yana daga manyan abubuwan da suka zama barazana ga ummi, a harkar karatunta, gashi ita ba kowa take raɓs ba, balle idan an bayar da assignment ko class work tayi, idan assignment ne ta gwammace ta kai yamma a makaranta, ta je Library ta yi.
Gashi farida ta tsiro da sababbun hanyoyin muzguna mata, ta hanyar ƙirƙirar mata abun da za ta sanya ta makara, wataran har ma ta rasa lectures baki ɗaya.
Daga baya ne take iya roƙon Abdul aron wayarsa, tayi assignment da ita.
Abdul ne ya gaya wa dr. Yakamata a saya wa ummi waya, saboda makaranta.
Da ya tashi dawowa ya taho mata da sabuwar waya, mai kyau da tsada, amma farida ta ƙwace ta bawa kausar, kuma ya kasa magana a kai.
Ba waya kawai ba, hatta undeas ummi na fuskantar matsala a kan su, sai dai idan ta tara ƴan kuɗi da ƙyar, idan farida ta aiketa kasuwa ta sai na gwanjo.
Daga baya Abdul ya saya mata wata ƴar ƙaramar waya, gionee take amfani da ita.
Makaranta ma da nata irin ƙalubalen, domin kuwa ƴan ajinsu, akwai yaran masu kuɗi, akwai ƴan ƙarya da yaran talakawa masu jin cewa su wasu ne.
Gani suke ummi ba tsararsu ba ce da za su yi mu'amala da ita, mussaman ganinta babu suturar kirki, kullum cikin hijjabi, hijjaban nata da guda biyu ne take zuwa da su, sai takalminta É—aya É—an wambai.
Banda masu zunɗen halittar ta, ko tambaya za ayi a aji, idan za a tanbayeta, sai malami ya ce dark skin girl.
Ummi ta sanya a ranta babu wani ƙalubale, da zai sanya ta kasa haƙuri ta cimma burinta.
Yunwa da tafiyar ƙafa a kan karatun nan suka zamewa ummi jiki, ko lissafasu ba ta yi a cikin wahalar rayuwa, handout kuwa ba kowanne take iya saya ba, wataran idan har zata sayi handout, sai ta yi trecking, domin samun kuɗin sayen handout.
Ta wuni a makaranta ba cin abinci, ta koma gida ta ci uban aiki, a ƙarshe ba godiya sai zagi da muzantawa.
HOD kuwa ba ƙaramin mutunta ummi yake yi ba, saboda idan ta ganshi sai ta kai ƙasa take gaishe shi, idan ta ganshi da jaka, sai ta bishi ta karɓa.
Yana jinjinawa tarbiyyar ta, da bayar da misali da ita, dan shi rabon da yaga É—alibi mai biyayyarta tun a zamaninsu, shima zamanin na su ba kowa ba.
Ummi ta dawo daga masallacin makaranta, tana ta sauri ta ƙarasa aji, saboda malamin da zai shiga, ko da minti ɗaya ya rigaka shiga aji, ba zaka shiga ba.
Abun da kunnuwanta suka jiyo mata wani ɗan ajinsu ya faɗa ne ya tayar mata da hankali matuƙa.
"Kai ishaÆ™, ka yi sauri mu tafi kar malamin nan ya rigamu shiga, ga gorillar ajinmu can na ta sauri".