Sashe 92
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce "To shikenan, in sha Allah zan kawota da kaina, amma saura sati biyu biki, zan zo na kaita gagarawa, ta je ta yi musu sallama, ta kuma basu katin bikinta"
Yaya maryam ko sunan garin ba ta ƙaunar ji, balle wani abu da zai sake haɗa su da garin, ta kasa jurewa ta ce "Amma ba a iya aika musu ba, dole sai ta je"
Dr. Ya ce "Na san abun da yake cikin zukatanku, amma ba a canzawa tuwo suna, dangin mahaifinta ne dole ku yi haƙuri"
Ta ce "To shikenan, Allah ya kaimu ƙarshen watan, sai kun zo ɗin"
Ya amsa mata da Amin.
Raihan daga shi sai Hajiya da kuma Hajiya Aisha suke ta shirin bikin, sai Alhajin sa, tausayin É—awainiyar da yake ta yi, ya sanya Salim É—an shiga lamarin, yake taimaka masa da shawarwari, dan shi abokansa duk sun yi aure, raihan kuwa age mate É—in sa wasu ma ba su kammala makaranta ba.
Saura watanni biyu bikin ummi, dr. Ya ce ta haɗa kayanta, zata tafi maiduguri kamar yadda ya yi alƙawari.
Ummi murna kamar ta taka rawa, dan dama jin ta take yi a matse a gidan nan, farida ta sakata a gaba da masifa iri-iri.
Ta rubuta takarda ta kai wa manager na barin aiki, manager kamar yayi kuka, saboda sun saba da ummi sosai da sosai, kuma suna jin daɗin aikinta, ba ƙyuya babu ganin ido komai na ta tsakani da Allah, sai dai sun yi mata fatan alkhairi sosai da jin ummi za ta yi aure.
Tana ta shirin tafiya maiduguri, raihan ya kirata a waya, ya ce mata manager yana nemanta, tayi mamakin yadda aka yi manager bai kirata ba, ya kira raihan, kai ka ce shi ma ma'aikacin su ne.
Ko da suka je, manager ya ce yayansa ne yake son ganin ummi, su É—an jira shi zai zo. Manager sai cewa yake "Shikenan tayi aurenta ta huta da nacinka, ko gidan nata zaka din ga bin ta kana takura mata?"
Raihan yayi wani irin murmushi ya ce akwai wanda ya isa ya raba ni da ummina ne? Kullum ina gidanta, ko kuma ka bani ƙanwarka na aura a haɗa mu biyu"
Manager ya harare shi ya ce "Aikuwa da mijinta ya zaneka saboda hayyatarka, in baka ƙanwata kai wa zai maka aure yanzu? Raihan da kana ganin ka fi ni girma gani ka ke kai wani babba ne ko? In sake jin ka yi maganar auren nan, sai na zaneka"
Wata irin kunya ta kama ummi, ta san da kunya idan ya bayyana raihan za ta aura, dan manager ya É—auka kawai É—an uwanta ne, irin sako da sakon nan.
Raihan kuwa ya din ga dariya, ya ce "Zan baka mamaki kwanan nan"
Shugaban wurin ne ya yi sallama, da yaransa suka amsa masa, ya samu wuri ya zauna suka gaggaisa, ya É—an yi musu raha kasancewar sa mutum mai barkwanci.
Ya ce "Ummi yanzu haka zaki tafi ki barmu, mijin ba zai bari ki cigaba da zuwar mana ba?" Ummi ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Raihan ya zuba mata ido ya ji me za ta ce, amma tayi shiru.
Ya yi ta yi wa ummi nasiha a kan zaman aure, ba tare da sanin da angon a wurin ba, sai dai raihan ya fara jin haushin yadda manager ya tsare ummi da ido, yana yi mata faÉ—an kamar mai rarrashinta.
Bayan sun gama ya ce ya bawa ummi kyautar sabon fridge babba, da kuɗi dubu hamsin da certificate na karramawa saboda gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙoƙarin da tayi wurin cigaban wurin.
Raihan cikin girmamawa ya ce "Masha Allah, mun gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya sa afi haka"
Ummi ma godiyar take yi masa, ta san kuÉ—in fridge É—in nan ba kaÉ—an ba ne ba, ga kuma kuÉ—i da ya bata.
Manager ya ce wa raihan "Ka gani, haƙuri mai tarar da rabo, da ba ta raina 15k ba, ga rabon da ta tarar nan, ka canza hali raihan. Ko kuma tun da ta tafi kai ka zo mu baka aikin"
Ya harari manager ya ce "Ba zan yi ba"
Har da masu kai fridge É—in aka haÉ—a ummi, masinjojin su.
Ummi ta kira dr. Ta gaya masa, ya din ga murnda sanya albarka ya ce zai je yayi musu godiya.
Ana gobe ummi za ta tafi maiduguri, raihan kamar yayi mata kukan ba ya son ta tafi, saboda zai daina ganinta a kai-a kai, sai dai yayi mata alƙawarin zuwa ya gaida mama.
Haka zalika ya tura mata kuÉ—i a account É—in ta, ya ce idan ya tashi zuwa maiduguri zai taho mata da kayan fitar biki.
Suna zane suna hirar, wayar ummi ta fara ringing, ta É—aga wayar, sai ya ga ta yi shiru tana kallon sa, amma ba ta ce komai ba.
Kawai sai ya tsargu, ya karɓi wayar ya saka a hansfree.
Muryar Safiyya ya ji, tana ta zazzaga rashin mutunci, da kalaman muzantawa ga ummi.
Jin ummi ba ta ce komai ba ya sanya safiyya cewa "Malama ba magana nake yi miki ba?"
"Da raihan É—in ki ke magana ba ummin ba" hankali a tashe ta kashe wayar, tana salatin Allah ya rufa mata asiri.
Ya kalli ummi ya ce "Dama haka take kiranki tana ci miki mutunci ba ki gaya mini ba?"
Ummi ta ce "To me zan ce, kullum sai in ƙare a kan ƙara, ni ba zan iya ba tun da ka ji yanzu da kanka shikenan, dan Allah idan zaka aureta ka aureta amma ni ta daina zagina"
Ya jinjina kai ya ce "Ina fatan dai ba shiru ki ke yi mata ba?"
"Ni mu bar wannan zancen bana so" tayi maganar tana zumɓura baki, ya ɗan ƙura mata ido, kishin ne yake damunta, dan haka yayi mata shiru kawai.
Daga wurin ummi da niyyarsa ya je gidan su safiyya, sai dai ya fasa ya tafi gida kawai.
Ummi ta tattara muhimman kayanta, ranar tafiya ta je yi wa farida sallama, amma ta ka da baki ta ce mata Allah ya raka taki gona.
Mami na ta sake maimaitawa raihan idan ya kuskura ya kashe kuÉ—i sosai a harkar auren ummi, sai ta ci masa mutunci fiye da yadda yake zato.
Kwana biyu da tafiyar ummi maiduguri, Raihan ya je gidan su safiyya, anty rakiya har ta fara yashe baki, tana cewa "Babban mutum barka da zuwa, yau kai ne a gidan namu?"
Ya ce "Eh, safiyya fa"
Ta ce "Ahh wurin mutuniyar aka zo kenan, to bari na yi mata magana"
Kasancewar Safiyya ta san abun da ta aikata, ya sanya gabanta faÉ—uwa ta ce ba zata ba.
"Dan ubanki abun da muke neman zaki ce ba zaki ba?"
Kamar za ta yi kuka ta ce "Ni fa tsoro nake ji, na gaya miki abun da ya faru"
"To sai ki bari kanki ya kulle, ba mace ba ce ke? Guda nawa raihan É—in yake banda ma ya jajibo aure? Tashi ki je dalla"
Har ta shiga falon tv yake kallo, bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, sai da ta zauna ta fara gaishe shi ya amsa, ya tambayeta ya makaranta ta ce masa lafiya ƙalau, sannan ya kalleta ya ce "Safiyya na san kin san abun da ki ka aikata, to ki sani, ba zuwa na yi bin ba'asi ba, kuma ba wani ya gaya mini ba, ta gaya mini na farko na kawar da kai, ban zaci irin wannan zagin ki ke yi mata ba, to ba sa'arki ba ce ba, kuma hakan da ki ke yi ba zai canza komai na batun aurena da ummi ba, wallahi idan ki ka sake kira mini mata ki ka ci zarafinta sai na gwada miki waye raihan, ba ruwana da wani zumunci sai na ɗaureki an ci tarar ki, na gaya miki. Ni ba ƙyale-ƙyale nake bi ba, mutunci, tarbiyya da soyayyar da nake yi mata ya sa zan aureta, kalli jikinki kowa ya gama gani, ba shigar mutunci a tuninki wannan ce wayewa safiyya? Dan an ce miki matar da zan aura kidahuma ce, ni a wurina hakan ne wayewa, kar ki bari abun da ki ka yi ya taɓa zumuncinmu, dan bana magana biyu, idan kuma Anty na da kuɗin belinki ki cigaba da kiran Salma kina ci mata mutunci tun da baki da kunya" bai ko tsaya yin sallama da anty rakiya ba, ya tashi yayi tafiyarsa.
Aikuwa kan ya je gida, tuni sun sanarwa da mami, yan zuwa ta dirar masa da masifa tare da kashedi iri-iri, ciki har da barazanar sanyawa a fasa auren sa da ummi, tare da jaddada masa cewar aurensa da safiyya ba fashi.
Ummi kuwa yadda su yaya maryam suke kula da ita da gyarata, har gajiya ta fara yi, a murza mata wancan, a shafa mata wannan, gashi aka hanata aikin komai, kullum tana kauwwame a wuri É—aya, daga ci sai sha, banda kayan magungunan gyaran da ake ta yi mata.
Tulin turarukan wutan da ake ta haÉ—awa kuwa, kai ka ce ci za ayi, ga uban kayan kitchen.
Ummi har hawayen daɗi tayi, saboda irin so da ƙaunar da dangin mahaifiyarta ke nuna mata, gashi dai ba wani ƙarfi ne da su ba, amma sai zuciya da ƙoƙari.
Ga isasshen lokaci da ta samu tare da mama, ga isasshen abinci mai kyau, komai na ta daban.
Saura wata guda biki, raihan yana ta shirin zuwa maiduguri, yana zaune suna shawara da hajiya, a kan yadda abubuwa zasu gudana, ya haÉ—a akwati guda na kayan fitar biki kawai.
Salim yana zaune sai dai bai tsoma musu baki ba.
Sai daga baya ya ce "Wannan akwatin É—aya kawai zaka kai sai ka ce tsiya, ba zaka yi lefe ba?"
Cikin sanyin jiki ya ce "Mami ta hana, ta ce bazawara ce, wai kuÉ—in auren da aka kai ya isa, shi ne na ce bari na yi mata kayan fitar biki, lefen idan ta je gidana na yi mata, amma kalli kayan ka gani masu kyau ne fa" yayi maganar yana buÉ—e masa akwatin.
Tabbas manyan kaya ne sosai da sosai na alfarma.