← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 134

Sashe 28

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hashim ya numfasa, cike da damuwa da takaici ya ce "Biyayyar da iyayenmu ke yi wa Iya, ta samo asali ne ga wasiyyar mahaifinmu, na lallai su yi mata biyayya. Bayan haka ban san dalilin da ya sanya bayan biyayyar suke rufe idonsu a kan gaskiya ba, su kasa nuna mata hanyar da ta dace ba.
Nayi iya yi na a kan auren nan, sai dai sun fi ƙarfina, ni dama ba wani shiri muke yi ba, saboda bani da kuɗi, Idris kuma sunan mahaifinta ne da shi. Ƙiyayyar ummi kuma, dama ba ta son mahaifiyar ummi, saboda kawu Magaji yana matuƙar son ta, har wasu lokutan baya iya ɓoye son da yake yi mata, bugu da ƙari, baban ummi ba shi da komai, bai mutu ya bar komai ba, duk da haka dai, ban san dalilin da ya sanya ta tsananta ƙiyayyar ummi haka ba.
Zan cigaba da yi wa idiris nasiha, duk da ba jin shawara yake yi ba, zan kuma biya ta gidan yanzu, in ga halin da take ciki".

Jiki a sanyaye na'ima ta ce "Yakamata kam, ummi na buƙatar kulawa da jaba jiki, har ga Allah ina jin tausayinta sosai da sosai, dan Allah yaya magaji ka din ga zagayata".

"Kar ki damu, in sha Allah, ba zai gagara ba, ina godiya sosai da gudunmawar da ki ke bawa ummi".

"Bakomai yaya magaji, ummi ƙanwata ce, ba zan manta karamcin iyayenta a gare ni ba, da yadda suke girmama iyayena ba"

"Haka ne, ki gaida gida, da maigidan"

Suka yi sallama, kowa ya tafi.

Kasa wucewa gida magaji yayi, ya wuce gidan Idris da bai taɓa zuwa ba.

Sallama yayi ya tsaya a waje, ummi ta leƙo, tana ganinsa tayi murmushi ta ce "Laa yaya magaji, shigo baka zo ba sai yau"

Ya kalleta duk da tana da duhu, amma ga shaidar mari nan a gefen idonta.

Ta yi gaba ta ce masa ya shigo, ya ce "A'a bani abun zama, na zauna a nan"

Ta shiga ta É—aukko masa tabarma, ta shimfiÉ—a masa ta ce "Yaya yaya na'ima ta zo fa"

Ya ce "Haba?"

"Wallahi, duk ta sai mini kayayyaki ta bani, ita ta bani tabar nan ma"

"Masha Allah, Allah ya saka mata da alkhairi"

Ta ce "Amin"

Ya ɗan dube ta, ya ce "Ummi babu wata matsala? Komai lafiya ƙalau?"

Ta jinjina masa kai ta ce "Eh".

"Na san ko baki faÉ—a ba, akwai matsala ummi, amma dan Allah ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce in sha Allah"

"Yaushe zai wuce yaya? Gobe ko jibi?" Tayi maganar idanunta na tara hawaye.

"Lokaci ne ummi, zai zama tarihi"

Tuni idanuwanta suka fara zubar da hawaye.

"Ki dake ummi, ki ƙarfafi zuciyarki, na san a cikin matsala ki ke, ki yi haƙuri ummi, ki share hawayenki, zai zama murmushi wataran" goge hawaye take yi, sai dai tana gogewa wasu suna zubowa.

Idiris ne ya bankaÉ—o babu ko sallama, yadda ummi ta zabura kawai ya isa ya baka tausayi.

Ko kallonsu bai yi ba, ya shige ya buÉ—e É—akin da yake kwana, ya shiga.

Hashim ya tashi ya bi bayansa, ummi ta karkaÉ—e tabarmar, ta É—aukko tsintsiyar da na'ima ta bata, ta yi shara, hayaniyar hashim ta din ga ji, da idris.

Hashim yana ce masa "Ka ji tsoron Allah wallahi, idan ka cigaba da biye wa Iya, wallahi Allah ba zai barku ba, kuna ta azabtar da marainiyar Allah ba gaira babu dalili".

"An azabtar da ita ɗin, ni na ce a aura mini ita? Ko na ce ina son ta ne, kai meya hana a aura maka ita? An bani saura ƙazama mummuna, Wallahi ba zan zauna da ita ba, sai ta gudu da ƙafarta".

"Amma ita ma ai ba cewa tayi tana sonka ba, haɗin Iya ne, ita tayi haƙuri, kai me zai hana ka yi haƙurin?"

Idris ya ce "ba zan yi haƙurin ba, ka fita daga harkata, ko kai ma na karta maka rashin mutunci"

Haka suka yi baran-baran, hashim ya fito, ummi tana ce masa kai gaida gida, kai kawai ya jinjina mata ya tafi.

Yana fita, Idris ya dirar mata da duka da zagi da cin mutunci kamar yadda ya saba, yana iƙrarin ƙararsa ta kai wurin magaji.

Maƙwabciyar su da ta kasance dattijuwa, yau ta kasa jure ihun ummi, ta shigo kawo mata ɗauki, ta din ga bashi haƙuri, amma mursisi ya ce ta fita ta bar masa gida, ganin idiris bai yi kalar mutunci ba, ya sanya ta fita ta bar gidan tana tausaya wa ummi.

Tun daga ranar ya ƙara tsananta azabtarwar da yake yi mata, gashi ya tula mata wankinsa, ya ce tayi masa, idan tayi bai fita ba, ya kamata ya zane ta, ban da zagi da cin mutunci.

Abinci kuwa ko tumatir bai taɓa kawowa ba, sai dai ta aika wa iya, Wataran ta bata, wataran ta ce ba ta da shi.

Ƙarshe sai da iya tayi ta mata faɗa, wai ba zata iya rufawa Idris asiri ba, ta san dai ba wata cikakkiyar sana'a ce da shi ba, ranar da ya kawo su ci, idan ba shi da shi ta din ga haƙuri.

Dattijuwar matar nan ta fuskanci halin da ummi take ciki, ta ɗauki ragamar ciyar da ita, idan ta cewa ummi ta gudu ta je gida ta kai ƙarar abun da yake yi mata, sai ummi ta ce ko ta je dawo da ita za ayi.

Da ya kalli ummi, ya tuna a yanayin da ya sameta, sai ya ƙara ƙaimi wurin cutar da ita, haɗi da zaluntar ta.

Idan aka zo ana sallama da shi abokansa, sai ta jiyo suna kiransa da angon É—oÉ—É—oya, ba ta kawo komai a ranta ba, sai ranar da ta jiyo suna tambayarsa ina amaryarsa É—oÉ—É—oya, ya ce musu kar su sake haÉ—a shi da wannan jakar yarinyar.

Duk da ƙarancin shekarun ummi, a lokacin ta fuskanci asiri ya tona mata a wurin abokansa, hakan ya sanya ta yin kuka da har kanta ya yi ciwo.

A haka a wannan baƙar azabar, tayi wata guda cir a gidan sa, tun tana tsoronsa har ta fara dakewa da duk abun da zai yi mata yayi mata.

Yau ta tashi da wani irin zazzaɓi mai zafin gaske, wanda baya rasa nasaba da dukan ruwa da kuma azababben sauron da yake cizonta a wannan ɗakin.
Ga gudawa da take zugawa babu ƙaƙƙautawa, jikinta duk yayi weak.

BankaÉ—a labulen yayi, ya tarar da ita a kwance, ya watsa mata kayansa ya ce ta wanke masa.
Shiru tayi ba ta motsa ba, ya daka mata tsawa ta ce "Yaya bani da lafiya"

"Ina ruwana, dalla fito"

Ta janyo jikinta ta kwaso kayan ta fito, ya fita sayen omo, ta kwanta a kan kayan, tana jin ɗumin ranar dake ratsata, wanda hakan ya sa zazzaɓi ƙara rufeta.

Azabar zafin dukan da yayi mata da ƙafarsa yasa ta tashi da sauri, tana riƙe hannunta.

"Bacci na ce ki yi?" Shiru tayi tana sunkuyar da kai.

Wani irin yawu ya haɗiye, yana ƙare wa ummi kallo, duk baƙin fatar nan ta ta fatar tana da ɗaukar ido.

A wurin yayi yinƙurin sake afka mata, sai dai ba ta sauya zani ba, duk da ta samu sassauci, na ciwon saboda yanzu sau biyu take sauya wando a rana, kamar yadda Na'ima ta gaya mata.

Amma duk da haka tana wannan ƙarin mara daɗi, duk da jikinta baya wari yanzu, saboda ta samu sabulun wanka.

Zura masa ido kawai tayi, saboda a galabaice take da ciwo

Wata mummunar ashar yayi mata, yana zubar da yawu, ya É—agota ya din ga kifa mata mari.

Kukan ma ba ya iya fita, saboda azaba da masifar idiris, da yake abu kamar dabba ba É—an adam ba.

Ya din ga tsine mata albarka, da ita da iyayenta, dan har Iya sai da ya zaga.

Ƙarshe ma ya danƙara mata saki a wurin.

Ƙafarta ko takalmi babu, ta gyara suturar jikinta ta fice daga gidan a haka, ta tafi gida ga hannunta ɗaya kamar ba a jikinta yake ba, saboda takata yayi a hannun.

Iya da ke iza wuta ta miƙe tana faɗin "Ke lafiya?"

Kan ummi ta yi magana, jiri ya ɗebe ta ta faɗi ƙasa.

Da sauri Iya ta ƙarasa kanta ta ce "Ke, menene wai?".

"Iya zan mutu, yaya idris zai kashe ni, dan Allah kar ki mayar da ni, ya ce ya sake ni" tayi maganar cikin gunjin kuka.

Ta taɓa jikin ummi ta ji zafi, ga fuskarta shaidar yatsun Idris kwance a fuskar ta har idonta yayi taruwar jini.

"Lallaɓa ki tashi ki shiga ɗaki ki zauna, daga yin aure ba a kashe shi ba, bari dai ya zo mu ji me ki ka yi masa" Iya ta tashi ta fita.

Kuka ummi ta din ga yi, tana jin dama ta mutu ta huta, idan aka mayar da ita gidan idris ta san sai ya kashe ta.

Da ƙyar Hashim ya nemo idris, aka nemo babansu, domin jin menene yake faruwa.

Sai dai daga mugun kallon da yake yi wa ummi, ka san babu Allah a ransa.

Babu zato babu tsammani sai ga kawu yahaya ya dira a gidan, kuma bai tsaya ko ina ba sai sashin Iya.

Sai dai babu walwala ko fara'a a tare da shi, suka gaisa da Iya da É—an uwansa, da su Hashim. Sannan ya kalli Iya ya ce "Iya dan me za a aurar da ummi, ba tare da na sani ba? Sai shekaranjiya magaji yake gaya mini?"

"Saboda kai ne ubanta? Uban waye ma ya ganka balle ya gaya maka, tangarÉ—a aka samu da wadda zai aura, na saka aka yi da ita dan rufuwar asirinmu".

Ummi da baccin wahala ya ɗauka, kamar a mafarki ta ji muryar kawu yahaya, miƙa hannu ta fara yi ta ce "Kawu"

Cikin azama ya nufi ummi ya ce "Na'am mamana"

"Dan Allah ka kai ni wurin mama, idan na koma gidan Idris kashe ni zai yi" ganin tana ƙoƙarin tashi ta kasa, ya sanya ya ɗago ummi.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya faÉ—a a razane.

Fuskar ummi ya gani a kumbure suntum, ga hannunta É—aya ma ya kumbura ba ta iya motsa shi sosai.

"Meyafaru haka?"
Chapter 28 · 0% Book details