Sashe 132
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanan ummi arba'in da biyar, ita da raihan da noor suka tafi yawon arba'in, a motar da Alhaji ya bata.
Suka fara da zuwa gidansu raihan, da suka je gwiwa a ƙasa ummi ta durƙusa ta din ga yi wa Alhaji godiyar mota da ya bata.
Yara sun cika hannu, sun ƙara kyau sosai, babu yadda za ayi ace yaran hausawa ne a yadda.
Alhaji ya ce "Su wannan larabawan ba su fara dariya ba ne? Ko ni É—in ne ba su gane ba" yayi maganar yana yi musu wasa.
Har wurin mami suka je, sai dai Nihal ce kawai ta ɗauki yaran, tana hangen yaran abun ka da jini, zuciyarta na son ɗaukarsu, amma sharrin zuciya da ƙiyayyar ummi ta saka ta share su.
Ana ta shirin bikin Nihal, saboda an kusa kawo kayan lefe, da an kawo kuma ba za a saka da yawa ba, za ayi bikin.
Daga nan kuma ta ce su tafi can gidan farida, daga nan ma ta duba jikin rahama, tun da an ce a gidan take jinya.
Raihan ya ajiye su, ya ce awa uku ya basu, zai dawo ya É—auke su, su tafi gidan mama.
A falo suka tarar da inteesar, kamar aljana ta rame, hasken nan babu shi, duk ta fita hayyacinta.
Ummi ta zauna tana faÉ—in "Anty intee kwana da yawa, ya ki ke ya gida?"
"Lafiya lau" ta amsa jiki a sanyaye, tana ƙarewa ummi kallo, da shigowarsu kawai ƙamshin kabbasar kayanta, ta gauraye ɗakin. Wata irin danƙareriyar lafaya ce a jikinta mai tsada, hannunta yatsu uku duk gold ne, haka kunnenta, har da chain na gwal a ƙafarta. Kai ba sai an gaya maka ba ka san ummi a hutu take.
Noor ta ce "Anty intee baki da lafiya ne? Duk kin rame" inteesar ta girgiza kai.
"Ina su Antyn su ke da rahama?" Da hannu kawai ta nuna musu É—aki.
Ummi ta kwantar da iman, a kan kujera noor ta ajiye aiman suka shiga É—akin da sallama.
Ɗakin sai warin gyambo yake, sai ɗan zani aka yafawa rahama, duk ta ƙone.
A gigice ummi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Anty rahama sannu ya jiki" rahama ta sunkuyar da kai sannan ta amsa.
Ta kalli farida ta ce "Anty ina wuni, ya mai jiki?".
"Dalla rufe mini baki, kin zo munafunci ki ga a wani hali nake ciki, ko na haukace na fara bin bola kamar babarki, to ina nan daram. Dangin maita bakin da ki ka yi mata ya kama ta.
Jiki a sanyaye ta ce "Astagfirullah, ƙaddara ce daga Allah, kuma ke ki ka hasala ni, ɓacin rai ya sanya na yi wannan furucin. Sannu Anty rahama, yadda Allah ya jarabce ki da wuta a duniya, Allah ya haramta mata namanki a lahira, Allah ya baki lafiya da akwai wani abu a raina ba zan zo duba ki ba, Allah ya baki lafiya"
Rahama ta riƙo hannun ummi ta ce "Ummi ba zan musa ba, idan aka ce alhakinki ne ya kamani, na san mun azabtar da ke, wallahi tun da na yi aure ko amarci ban gama ci ba, na fara shan wahala har yau ban samu kwanciyar hankali a gidan aure ba. Dan Allah ki yafe mini"
Ummi ta shafa hannun rahama ta ce "Na yafe miki wallahi, Allah ya yafe mana baki ɗaya, Allah ya baki lafiya bari na je falon na ji kamar kukan aiman" ta miƙe ta fita.
Farida ta kalli noor ta ce "Sannu sallalamammiya, ashe kin canza uwa ko?"
Noor ta ce "Idan na yi miki laifi fa ce wa ki ke yi na nemi wata uwar, dama ke ba uwata ba ce, ki yi ta hantarata da zagina, ni kuma bana jin daɗi ni ki ka tsana ban san me na yi miki ba" sai jikin Farida yayi sanyi, ta tuna maganar ummi, ba ta taɓa zaton abun da tayi zai yi tasiri a zuciyar noor ba.
Ta basar ta ce "Da uban wa aka saka miki rana ban sani ba?"
"Yayan yaya raihan ne, yaya salim"
Kausar da ke gefe tana danna waya ta ce "kutt wannan gandamemen mutumin, me yayi miki zafi?"
"Ni kar ki yi mini hassada, haka kurum in tsufa a gida, ke da ki ke kyau ma baki yi aure ba, balle ni ba zaki zigani ba" suka hau faÉ—a kasancewar kwana biyu ba su haÉ—u ba.
Farida ta tsawatar musu, sannan ta koma kan rahama da masifar, uban me suka yi wa ummi da take neman yafiyarta.
"Ashsha! Yaya ki farga kema kan lokaci ya ƙure. Kin san mun azabtar da ita, ke ki ka gaya mini halin da Iya take ciki, ni dube ni wallahi hakki ne"
"A'a ni ban É—auki hakkin kowa ba, dan haka ba wata yafiya da zan nema, ta daÉ—e ba ta yafe ba".
Ummi kuwa na komawa falo, ta tarar da inteesar tana zaune ta zuba wa yaran ido, ta saka hannu ta É—auki aiman da ya tashi ya fara kuka.
Tana ɗaga kai ta ga ummi ta ajiye shi, tana basarwa. Ummi ta yi murmushi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ajiye mata shi a cinyarta ta ce "Haba ɗan gidan babban mutum, mamanka ce da ba ka santa ba, ka buɗe ido ka kalleta" Inteesar ta saka hannu ta rungume shi, ta fashe da kuka.
Ummi ta san kukan me take yi, ta dafa ta ta ce "Haba Anty intee, Allah ya baki rai da lafiya, kar ki yi masa butulci, rashin haihuwa jarabta ce, ki gode masa ki yi addu'a idan ki na da rabo, Allah ya baki naki kema. Zan taya ki Addu'a in sha Allah zaki ga É—anki, Allah ya baki rabo a satin nan, ni na yi biyu ke ki yi uku, mu tarawa kawu abokan wasa"
Cikin kuka ta ce "Aurena ya mutu ummi, uwar mijina ta saka ya sakeni, wai bana haihuwa sai ci da kashi. Sun wulaƙanta ni, sun tozarta ni, Abba ya ce babu ruwansa na ƙarata na nemi wani uban. Zuciyata za ta fashe ummi, gashi tun da na dawo kausar ta mayar da ni kamar maƙiyiyarta sai raini da wulaƙanci ita kanta maama tayi ta hantarata, wallahi ji nake kamar na sha guba na mutu"
Da sauri ummi ta toshe mata baki, fuskar ummi ɗauke da hawaye ta ce "Haba anty inteesar, mutuwar aure ba kan ki aka fara ba, ba kuma yana nufin ƙarshen rayuwarki bane ba. Abba kuma kun yi masa laifi yana gaya mini, kun tafka kuskure da kuka daina kula shi, ko gaishe shi ku ka daina yi, dan ya auri mamana. Ku ka manta da duk ɗawainiya da hidima da ya yi mana a rayuwa.
Ki kwantar da hankalinki, ki nemi afuwarsa nima zan taya ki roƙonsa, na san zai yafe miki. Abu na gaba kuma, ki yi ta addu'a da miƙa wa Allah lamuranki, idan ki ka gama idda, ki roƙi Abba ya bar ki, ki koma karatu, ko ki fita ki koyi wata sana'ar hakan zai rage miki lokacin da ki ke spending a cikin gida da su Anty farida, amma dan Allah kar ki sake cewa zaki kashe kanki"
Inteesar ta kwanta a jikin ummi ta ce "Ba ki san me nake ji ba"
"Na ɗanɗani fiye da abun da ki ka ɗanɗana, da ko maƙiyina bana fatan ya ɗanɗana. Sai da ta kai a duniya ina jin kamar nikaɗai aka tsana, na sha jin nima kamar na kashe kaina, a lokacin da bani da kafaɗar kashingiɗa na yi kuka, noor ce kawai take tayani kuka, sai zuwan Baban su iman rayuwata, ya nuna mini ita rayuwa yadda ka ɗauke ta, haka take zuwar maka. Dan Allah ki daina wannan kukan".
Ummi ta yi ta rarrashin inteesar, Farida ta fito tana faÉ—in "Ke Inteesar kukan me ki ka yi mata?"
Inteesar ta share hawayen ta, ta ce "Babu abun da tayi mini, miƙo mini macen na ganta"
Ummi ta miƙa wa inteesar iman, ta haɗa su ta rungume, tana cigaba da zubar da hawaye.
Duk yadda farida ta bugi cikin noor, a kan ta gaya mata shirye-shiryen da ake ciki a kan aurenta, amma tayi mursisi tayi shiru.
Sai da suka yi faÉ—a, ta ce noor ba za ta bi ummi su tafi ba.
Sai ga inteesar ta sake da ummi, tana ta bata labarin irin zaman da ta yi a gidan aurenta.
Ummi ta ce "Babu auren da ba shi da ƙalubale" nan ita ma ta din ga ba ta labarin irin ƙalubalen da take fuskanta.
Ummi ta din ga jaddada mata, ta nemi yafiyar dr.
Raihan ya kira wayar ummi ya ce yana waje.
Noor ta kwashi takalmanta da gudu, ta yi waje saboda farida ta ce ba zata bar gidan ba.
Ummi ta je ta ajiye wa rahama kuÉ—i, suka yi waje.
Inteesar ta raka ummi da jariran nan, kamar kar ta bawa ummi su, har ta yi wa ummi alƙawarin zuwa har gida ta yi mata barka.
Daga nan suka wuce gidan mariya, tayi murna sosai da sosai da zuwansu, aka yi sa'a dr. Yana nan, ummi ta yi masa maganar inteesar.
Ya ce "Inteesar tsakanina da su ai sai ido, ni da ban ishe su kallo ba"
Ummi ta ce "Mun yi magana da ita kawu, dan Allah ka yi haƙuri, za ta baka haƙuri ma. Ta fara iƙirarin shan guba ta kashe kanta, dan Allah ka yi haƙuri ka ja ta a jiki dan Allah. Mun yi hira da ita sosai, ta fuskanci ƙalubale sosai a gidan aure, sai dai anty farida ba ta din ga ba ta shawara ta kirki ba"
Ummi ta cigbaa da lallaɓa shi, har ya amince.
Noor tun da aka saka ranar aure, take wani irin jin nauyin Salim, idan ya zo duk surutun ba ta iya yi masa.
Kausar kuma hankalinta ya tashi, noor za ta yi aure ta bar ta, duk samarin nata babu na aure sai Æ´an sharholiya.
Mariya kuwa, Abdul ne zai kai ta maiduguri, ummi kuma da ita da noor, raihan ya tafi da su bauchi, daga can idan suka kwana biyu su tafi maiduguri.
Hajiya Aisha ta din ga murna, dan dama raihan bai taɓa kai mata ummi ba.