← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 134

Sashe 3

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Za su daina Ummi, yarinta ce take damun su"

Ummi ta ce "To"

Hargowar iya ta jiyo a tsakar gida"Sai ka ce mayya, kamar a duniya babu wanda ya taɓa haihuwa sai ke, ai ba a banza ba wannan kalar idon na ƴar ki, na fara zargin akwai masu lashe-lashe a danginku, dan baƙar masifa, sai da ki ka tafi yawon ɗaukotta, shafaffiya da mai" Mariya ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Sa'adatu matar Sagir, da tayi sallama a sashin ta tarar da iya tana ta zuba tijara, ta ce "Iya ke da wa kuma a tsakar ranar nan?"

"Wacece idan ba mariya ba? Duniya kamar babu wani mai É—a sai ita, in dai aka wannan mummunar yarinya ce, ba ta ji ba ta gani".

"Iya kenan, mutum da É—an sa ai sai Allah, sauran kunu na zo idan akwai in bawa yaro, ya fara yi mini kukan yunwa"

"Shiga ciki ki duba, ni fita zan yi" tayi maganar tana saɓa mayafinta a kafaɗa ta fice.

Sai da iya ta fita, sannan ta lallaɓa, ta fito yi wa ummi wanka.

"Maman ummi, ashe ummi kuma an shiga makaranta"

Mariya ta ce "Wallahi kuwa, ummi an shiga Ecc"

"Masha Allah, Ubangiji Allah ya yi jagora, ya sa an shiga a sa'a"

Mariya ta amsa da "Amin"

Ummi ta É—an samu sassauci, daga laluben da samarin gidan suke yi mata, saboda shigarta makarantar boko, tun safe sai sha biyu na rana, daga nan kuma ta kwanta tayi ta bacci, wasu lokutan yaran gidan da Æ´an sa'anninta, su zo su tafi da ita makarantar allo.
Duk da kuka wasu lokutan kuka take ba ta so, haka mariya ke tursasa mata ta tafi, saboda shi ilimi, dole a tsayawa yaro yayi shi, ko da kuwa ba ya so, mussaman ma na addini.

Duk da a hakan wasu lokutan ba ta tsira ba, ba ya hana azo har sashin su a É—auke ta, idan mariya zata hana, iya tayi ta masifa.

***
Yau Mariya ta yi yamma wurin girki, tana ta aiki a tsakar gida, iya tana zaune a kan kujera ƴar tsuguno, ta kasa ta tsare, sai waƙe-waƙenta take yi na mutanen da, waƙoƙin daɓe wasu kamar na batsa,wasu kamar habaici.

Wata mata ce tayi sallama, suka amsa baki É—aya, matar ta gaida iya, Iya ta amsa mata cikin sakin fuska har da yi wa É—an matar wasa.

Mariya ta ce "Mai koko ke ce da yammacin nan? Bari na baki abun zama"

Mai koko ta ce "Wallahi kuwa, haja na kawo miki"

Mariya ta shimfiɗa mata tabarma ta ce "Haja kuma, to Allah ya sa ba ta fi ƙarfin talaka irin mu ba".

Mai koko ta kwance kaya, kayan yari da sarƙa ne da mayafai a taƙaice dai kayan koli ne.

Mariya ta yi ta ɗaɗɗagawa, kayan sun yi mata kyau sosai, ta san idan ta ɗauka baban ummi ba zai ce komai ba, amma ba ta son takura shi, dan haka ta ce "Mai koko muna da ɗan kunne, maɗaurin gashi na so saya wa ummi, sai dai wannan sun yi ƙanana ba zai riƙe gashinta ba, sai dai idan muna buƙata zan yi miki magana da yardar Allah"

Ita ta ce "Ke ma dai mai koko, ke da ki ke neman arziki, ina ke ina kawo wa wannan kaya, ba su da komai sai tsiya da babu, ki kai sashin Sagir, ko gidan iliya, wannan ai da kin taɓa su babu".

"Na ga alama kam, ban taɓa kawo kaya mariya ta saya ba, kullum sai aukin idan tana buƙata ta aiko ta saya".

"Kema tun da aka yi É—aya biyu, ai ba kya bari ayi uku ba, da dai hidimar Æ´ar ta ce, nan tafi kauri, ta kanainaye mini É—a ta hana shi arziki"

Tuni mariya ta tashi, ta koma kan aikinta.

Mai koko ta É—aure kayanta ta ce "Aikuwa iya ki dage da nema masa magani, Æ´an uwansa duk suna da rufin asiri ban da shi, sa anjima"

"Yawwa ki gaida gida"

Ba ta sake bi ta kansu ba, kamar kullum yau da wuri ummi tayi bacci, bayan mariya ta kammala girki, ta É—ebi gawayi, ta goge wa ummi uniform É—in ta, ta gama komai, tana jiran dawowar baban ummi.

Kamar mai kiran kurma, Iya ta ƙwala mata kira, ta fito da sauri a ɗan razane ta ce "Iya gani"

"Maza yafo mayafinki, ƴaron wurin iliyasu ne, ƙaramin ya haɗiye ƙaya, ku ɗauki yaron ki raka Sa'adatu ku je gidan sarkin suu, ya bashi magani"

ÆŠan jimmm mariya tayi, so take ta huta, tun safe take aiki a gidan kamar jaka, yanzu kuma iya ta tsiro da wani abun.

Ba yadda ta iya, ta ce "To, bari na goya ummi, dan tayi bacci"

"Wai ke wace irin mace ce, har yaron ya mutu baki gama goyon wannan buhun sumuntin yarinyar ba, ban da rashin kara, ai ke yakamata ki goya mata yaron, dan Allah ki hanzarta ku tafi, ina nan me zai samu ummin, hanzarta maza".

Haka nan mariya ta ji gabanta yana faÉ—uwa, kamar wani abu zai faru idan ta tafi, ga Iya sai É—aga mata murya take a kan tayi sauri.

"Iya zan iya goya ummin, sai in É—auki yaron a hannu"

"Wai mariya meyasa baki da kunya, ina faÉ—a kina faÉ—a? Salon ki je ki kayar da yaron, ga wannan uwar Æ´ar ta ki, kaya guda a haka zaki É—auki, yaron ba zaki hanzar ta ba, ko dan ba É—an ki bane ba, ko da yake ina mai É—a É—aya ya san ciwon É—a ma"

Ta ce "To ko in kawo ta É—akin ki, sai in kwantar da ita, idan na dawo na É—auke ta?"

"A'a ba zaki kawo mini ita ta yi mini fitsari ba, wannan samgartacciyar yarinyar, É—uwawunta ba shi da saiti. Uban meye ma zai kamata a É—akin, ki wuce ku tafi"

Jiki a sanyaye mariya ta shiga É—aki, ta É—akko mayafinta, ta na ta kallon ummi, tana fatan Allah ya sa babanta ya shigo da wuri.

Ta fito tsakar gida wasu daga cikin jikokin iya suka shigo, shigowar su bai sanya iya yin shiru ba, ta cigaba da yi wa mariya masifa.

Duk mutanen da ke cikin gidan, iya ta rasa wanda zata saka yayi rakiyar kai yaron sai ita, saboda dai kar ta huta, kuma kar ta zauna lafiya.

Suna tafe a hanya tana goye da yaron, sai kakari yake yi, saboda yadda ƙayar take sukansa. Ga gidan sarkin su da nisa sosai, haka suke tafe da fitila.

Sai dai zuciyarta sai harbawa take yi da sauri, hankalinta yaƙi kwanciya, ji take tamkar ta juya da gudu, ta koma wurin ƴar ta.

Sai wajen tara da rabi suka dawo, gudu-gudu sauri-sauri ta nufi sashin su, ba ta bi ta kan iya ba, ta nufi É—akinta.

Sai dai ta kai kai zata shiga É—akin, shi kuma ya fito da sauri, jikinsa yana tsuma.

"Me ka ke yi mini a É—aki yanzu? Me ka yi?" Shiru yayi yana tsuma tare da kallon ta, ta hasken farin wata.

"Me ka yi mini a ɗaki i yanzu? Me ya kai ka ɗakina?" Tayi maganar cikin ƙaraji.

Iya ta ce "Wai lafiya kuwa? Kun dawo kenan ya jikin yaron?" HankaÉ—e shi ta yi daga gabanta, ta shiga É—akin da sauri, tana kiran sunan "Ummi"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Iya! Iya! Zo ki ga? Iya zo da sauri"

Da sauri iya ta taho da gudu tana cewa "Wai meye ne?"

Ta shiga É—akin, ta tarar da ummi a kwance, tana ta numfarfashi, jikinta sai rawa yake yi, an tura mata hularta a bakinta, ga wandonta a yashe a gefe gabanta duk jini.

Iya ta dafe ƙirji ta ce "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, wace irin masifa ce wannan, me yaron nan ya zama, kar dai ki ce mini yaron nan ne?"

Cikin kuka mariya ta cirewa Ummi abun bakinta ta rungume ta, cikin É—aga murya ta ce "Haba iya, da idonki fa kin gani, kina gani fa, waye ya fita daga É—akin nan idan ba shi ba, na shiga uku na lalace an cuce ni, an cuci Æ´a ta"

"Dalla ki rufewa mutane baki, idan kuma kururwar zaki cigaba, ki tonawa kanki asiri shikenan, idan ba wata ƙaddara ta Allah ba, waye ma zai aure ta, balle a san me ya faru da ita" sororo mariya ta bi iya da kallo, wanda hakan yayi dai-dai da sallamar baban Ummi.

Iya ce ta iya amsawa, ya shigo ya same su, mariya rungume da ummi tana kuka.

"Maman ummi, Iya meyafaru ne? Ummin ce babu lafiya?"

Mariya ta ɗaga masa ƙafar ummi, tana kuka ta sanar masa da abun da ya faru.

Salati ya saka ya durƙushe a wurin.

Iya ta ce "Da ki ke É—orarwa ke kin tabattar shi É—in ne? Sai ki jirani in bincika in tabbatar ai". Ta tashi ta fita daga É—akin.

"Mariya, kina me? Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru"

Cikin kuka mariya ta ce "Wallahi iya ce baban ummi, iya ce na shiga uku an lalata mini rayuwar Æ´a ta, ina zan saka kai na"

Iya ce ta dawo riƙe da hannunsa, zuwa cikin ɗakin ta kalleshi ta ce "Uban wa ye ya yi wannan aikin? Me ka yi mata, ba sallama ka yi mini ka ce zaka tafi shagonku ba?"

Jiki a sanyaye ya ce "Wallahi iya tsautsayi ne"

A fusace balarabe ya tashi ya shaƙe shi, ya ce "Tsautsayin ka kasa sauke shi a ko ina, sai kan ƴa ta".

"Zaka cika shi ko sai na É—auke ka da mari? Ba É—a yake a wurin ka ba kai ma? Idan É—an ka ne ya aikata hakan, tona masa asiri zaka yi? Ko idan ka tayar da maganar wani abun hakan zai amfanar, aikin gama ya riga gama.
Kuma bari ka ji in gaya maka, wallahi tallahi, muddin ku ka ɗaga maganar nan, wani ya ji ta, bayan mu ɗin nan, Allah ya isa ban yafe ba, kowaye sai na tsine masa. Ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta. Idan baku rufa musu asiri ba? Waye zai rufa musu ko salon zumunci ya lalace? Ƙuruciya ce da ƙaddara da bai wuce kan kowa ba"
Chapter 3 · 0% Book details