← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 134

Sashe 53

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana ajiye wayar farida na shigowa, ta cigaba da yi masa bala'in idan ma yana da burin ƙara aure ne, to ya san abun da yake ciki, dan taga kamar ya ɗau maganar noor serious.
Gaba É—aya ma dariya ta bashi, dan haka ya shareta ta cigaba da banbaminta

***
Haka nan ummi ta É—an damu, kwana biyu shiru ba Raihan babu labarin sa, ya daina nemanta a wayar ma, kamar za ta damu, kuma ta basar ta manta, ta cigaba da sabgoginta.

"Hi dear" taga message ta what's app ɗin ta, what's app ɗin da ta fi ƙarfin sati uku ba ta buɗe shi ba saboda rashin data, sai yau da ta samu ta saka ɗari biyu.

Baƙuwar lamba ce, ba ta san waye ba, dan haka tayi replying da Assalamu alaikum.

Ta tsaya ta ƙurawa message ɗin ido, hi dear, dear kalma ce da ake iya gaya wa kowa, amma mussman wanda yake da muhimmanci.
To ita akwai wani wanda take da muhimmanci a gare shi, da har zai ce dear.

Tayi guntun tsaki da ta tuna, akwai mutanen banza a what's app, wanda ba su sanka ba, amma su yi maka maganar banza.

Ta cigaba da shirinta na tafiya wurin aiki, ba ta taso ba sai ƙarfe huɗu da rabi, a hankali take tafiya, sai dai wata mota ta cika mata kunne da horn. Ta matsa gefe amma ya cigaba da yi mata horn.
Gefe ta koma ta bar wa motar hanyar, ta cigaba da tafiyarta.

"A wannan yangar da iyayin naki, sai kin fusata mutum ya ture ki" cak ta tsaya, ta waiwayo da mamaki ta ce "Laa raihan, yi haƙuri ban san kai ne ba".

"Eh shi ne ki ka bar mini hanyar, wato na ci kaina, ban isheki kallo ba"

Ummi ta ce "Eyya ba haka bane ba, ban san kai bane" tayi maganar tana kallon sa, idonsa yayi ja, kamar daga wani wurin yake.

"Wucewa na zo yi, na san sai yamma ki ke tashi, na tsaya ki fito mu tafi".

ÆŠan shiru ta yi tana kallon sa, ba ta son shiga motar nan tasa, kar a fara zargin wani abu.

Ya É—an marairaice ya ce "Nayi awa a wurin nan ina jiranki, dan Allah kar ki ce a'a".

Ta ce "To" tabi bayansa, suka nufi motarsa.

Suna tafe a hanya, har lumshe ido take yi, saboda gajiya.

"Yaya ummi kwana biyu ko ki neme ni, anya za ayi zumuncin nan da ni kuwa? Na yi busy sosai kwana biyun nan, ko waya bamu yi ba, kuma baki nemi in da ƙanin naki yake ba".

"Yi haƙuri ba haka bane ba, zan din ga kiranka in sha Allah".

"Allah ya sa, ya karatu ya É—alibai?"

Ta amsa da"lafiya ƙalau Alhamdilillah"

"Masha Allah, nima kwana biyu Alhaji ne ya sakani aiki, ya ga ina sararawa bana aikin komai, ina ga gani yayi sharholiya ta yi mini yawa, ya sani aiki ko cikakken lokaci bani da shi, duk na rame na zama baƙi"

Ummi ta ɗan yi murmushin yaƙe, cikin fargabar abun da ka iya biyo bayan maganar sa, wataƙila cin zarafin kalar fatarta.

Bai damu ba ya cigaba da maganar sa, "Ni fa yunwa ma nake ji, ko mu tsaya mu ci abinci?"

Tayi farat ta ce "A'a, na ƙoshi ma ai, a ƙoshe nake ai"

"Yaya ummi kenan, da abinci ki ke zuwa kenan? Tun safe fa kina wurin nan, to idan kin zo da abincin ki din ga ci kina rage mini, dan ni yau tun da aka kirsheni a wuri É—aya tun ina ganewa har na daina, bari na yo takeaway a wannan wurin abincin". Ta ce "To".

Ta kai mintuna sha biyar a motar, sannan ya dawo da manyan ledoji, ya tarar ta sauke facemask É—in ta.

"Sannu na bar ki kina jira ko? Tuwo na so in samu, babu sai shinkafa ni kuma damuna take yi"

Tayi murmushi ta ce "Kana cin tuwo kenan? Abdul É—in gidanmu baya son tuwo"

"Haba dai, ai yaya tuwo abun so ne, ni a bauchi na saba, Alhajin Bauchi da shi yake karyawa, ga kwanonsa ga nawa, amma shima fa tuwon bana jera kwanaki ina ci yake isata"

Tayi dariya ta ce "Ka fi son dai a din ga ccacanzawa"

"Yauwwa, ba kullum abu É—aya ba"

Yau dai yayi sa'a, ta É—an saki jiki kaÉ—an, dan yau har da dariya.

Ya ƙarewa hijjabinta kallo, duk yayi fari takalmin ƙafarta ma ya tsufa.

"Ummi"

Ta ce "Na'am"

"Me ya fi burgeki a rayuwa? Wanda yin sa yake yi miki daÉ—i, ko samunsa, abun da dai yake saka ki farinciki?"

Tayi shiru tana tunani, oho, ita akwai wani abu da take jiran samuwar sa ya sanyata farinciki ne? Duk abun da ya zo mata a rayuwa kawai, karɓa take yi.

"Babu"

"Ban gane babu ba? Kawai haka ki ke rayuwa ba farinciki?"

Ta sunkuyar da kai ta yi shiru.

"No dole akwai, ki tuna sai ki gaya mini"

"Babu" ta sake bashi amsa.

Bai sake ce mata komai ba suka cigaba da tafiya, in da ya ajiyeta wancan karon, ta sake cewa ya ajiyeta.

Ya yi parking sannan ya kalleta ya ce "A nan zaki sauke, ba zaki bari na ga gidan ba?" Ta hau wasa da yatsun hannunta bata ta kula shi ba.

"Bayan Æ´an uwa let's be true friends ummi, ki tuna abun da yake saki farinciki ki gaya mini, mu zama Æ´an uwa kuma abokai saboda Allah"

"To in sha Allah"

Yayi murmushi ya ɗauki leda ɗaya, ya ce "Ungo naki" ta kalleshi zata yi magana, ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa ya ce "Shhh".

"Idan zan wuce gobe in Allah ya kaimu zan jira ki mu tafi tare" ta jinjina kai, ta fice daga motar.

Addu'a take yi, tana fatan Allah ya sa kar wani ya ganta, cikin ikon Allah babu wanda ya ganta, har security gidan yana banÉ—aki, ta wuce ta shiga har É—akinta ba ta haÉ—u da kowa ba.

Ta sauya kaya ta fito, ta dudduba gidan babu kowa, ta koma É—akin ta duba ledar da Raihan ya bata.

Rabin kaza ce guda a cikin ƙatuwar roba, sai shinkafa da salad.

Jikin ummi har rawa yake, duk wannan kazar ita kaÉ—ai?.

Sai kuma ta yi shiru tana tunani, anya ba ta zura jiki ba? Kasa ci tayi ta tashi ta shiga aikin gida.

Abdul ne ya shigo yana waya, ya kammala ya tsaya yana mita.

Ummi ta ce "Yaya Abdul kana nan dama?"

"A'a yanzu na shigo, wani É—an rainin hankali ne ya kirani, wai babansu ne ya buÉ—e shago a tal'udu, suna neman casheir, wanda zai din ga zauna musu da safe zuwa azahar, ko azahar zuwa magariba".

Ummi ta ce "Dan Allah yaya Abdul zan yi, ina so"

Ya kalleta ya ce "Zaman jiran shagon, shagon furnitures ne fa da kayan kitchen"

"Eh yaya Abdul dan Allah, dama na gama SIWES, kawai dai sun buƙaci na cigaba da zuwa ne, dan Allah zan yi"

Abdul ya É—an yi shiru sannan ya ce "Zan yi magana da Abba, idan ya yarda shikenan".

"Yauwwa zai yadda ma in sha Allah" tayi maganar tana addu'ar Allah ya sa Abba ya amince, ita ko kuɗin babu yawa tana so, atleast ta din ga samun na sayen wasu abubuwan da take buƙata.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye da kazar nan a ɗaki, dr. Gidansa ba ya rabo da nama da kaji, amma tsaf ummi za ta yi aikinsu, farida ta karɓe idan ta ga dama ta sanmata idan ba ta ga dama ba, sai ummi ta zo wanke-wanke ta ɗan tsinci sauran hanta, da diddiga ta lasa abun ka da zuciya.

Hankalinta bai kwanta ba, sai da ta saka noor a gaba, ta gaya mata yadda aka yi, kamar sa'arta.

Noor ta din ga murna ta ce "Yaya ummi kar ki gaya wa kowa mu cinye abunmu".

Ummi da noor suka cinye takeaway tare, suna ta murna, dan kuwa ummi ba ta taɓa cin kaza mai yawan haka ba.

Masu nema daga farko dan Allah ku duba a watpad
Ayshercool
08081012143

    *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P23

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

23

Murmushi ummi ta yi ta sauke wayar, tana sake gazgata maryam da take yawan faÉ—ar Raihan rigiamamme ne.

A ɓangaren sa shima ajiye wayar yayi yana murmushi. 
Chapter 53 · 0% Book details