← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 134

Sashe 67

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata blueblack ta ɗaukko mai matuƙar kyau, matar ta nunawa ummi in da zata shiga ta gwada rigar.

Tsayawa ta yi a gaban mudubin ɗakin, tana ƙarewa kanta kallo sanye da rigar, yau dai sau ɗaya a tarihin rayuwarta, ta saka doguwar rigar abaya da take matuƙar burgeta.

Ta riƙe ɗan kwalin rigar a hannunta, ta zubawa mudubin ido, ta tafi tunani, ta zubawa mudubin ido, tana hango rayuwarta ta baya a ciki, cike da tozarci da ƙasƙanci, da rashin galihu kamar mara amfani, shigowar raihan rayuwarta ya bata lokacinsa, duk hankalinsa saboda kawai ya sakaya farinciki. A ranta take addu'a 'Allah idan ina da rabon yin aure a duniya, Allah ka kawo mini miji na yi aure, kar na yi aure na kasa rabuwa da raihan' saboda sosai take jin sa a jikinta.

Ummi bata san adadin daÉ—ewar da ta yi a tsaye ba, saboda gaba É—aya ta bar cikin hayyacinta.

Raihan gajiya yayi da zaman jiran ummi, kawai ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin amma shiru, kawai ya tura ƙofar da sallama.

Kamar gunki ya ganta a tsaye hannunta riƙe da ɗan kwalin rigar, hawaye ya wanke mata fuska.

Sandarewa yayi a tsaye, ta saka siririn ribbon ta É—aure gashin, ta sake shi har tsakiyar bayanta.

Ganin raihan ta cikin mudubi daf da ita ne, ya sanya ta dawo hayyacinta a razane, kokowar rufe kanta ta fara yi.

A hankali ya saka hannu ya É—aure zaren rigar ta baya.

Ya saka hannu ya kamo gashin da ya sauka a bayanta, tsigar jikinta ce ta tashi, ta waiwayo da sauri, ƙare mata kallo yake yi. Rigar ta yi cif a jikinta, dirarriyar mace ce ta gaske, baƙar fatarta kawai mutane suke kallo, amma daga ƙirjinta zuwa ƙugunta komai dai-dai jikinta, kasa daina kallonta yayi, karo na farko kuma da yau ta kalli raihan a wani abu daban ba ƙaninta da take yawan faɗa ba.

(Team a bamu daga farko, ku yi Allah ku din ga dubawa a watpad Please 🙏)

Ayshercool
08081012143
What's app only
*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P28

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

28

Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannunsa a aljihunsa, ya ciro wayarsa.

Ya shammaceta ya fara É—aukar ta hoto ta cikin mudubi.

HaÉ—e rai ta yi ta ce "Meyasa zaka shigo mini ba izini? Ni ka fita"

"Na yi knocking, na kuma yi sallama, duk baki amsa ba, kin bar ni a tsaye ina ta jiranki, kin shigo kina kuka, idan ma dan in bar miki rigir ne ki ke kuka, ba zan baki ba, fito mu tafi"

Ba tare da ta saki fuska ba, ta ce "Ni ka fita na cire rigar"

Ya basar ya ce "Ki batta a jikinki, ki zo mu tafi".

"Dan Allah ka fita na cire" tayi maganar a raunane tana ɓoye jikinta.

A hankali ya taka ya nufi hanyar fita, ya sake waiwayo wa, tana tsaye jiran ya fita ta canza kayan.

Ya fita ya koma reception.

Ba ƙaramar kunya ce ta kama ta ba, ganin da yayi mata a haka, gashi dai doguwar riga ce, amma ta kasa manta irin kallon da yayi mata, da ya sanya ta shiga wani yanayi da ba ta san menene ba, gaba ɗaya sai ya canza mata, kamar ba raihan ɗin da ta sani ba.

Ta mayar da hijjabinta, ta fito da rigar a hannunta, matar ta kallesu ta ce "Rigar ta yi?"

Ya ce "Eh, bamu wasu kalolin a haÉ—a da wannan, su zama biyar sai takalmi uku da zai shiga da kowacce" komai da ummi aka gwada, kuma ba ta kawo komai a ranta ba.

Ɗan nazarinta ya din ga yi, ko fushi take yi da shi, amma ya lura kawai ta tsorata ne, ta kasa sakin jiki ma tayi masa magana, dan abu ne mawuyaci ka ga ummi ta yi fushi, dan zai iya cewa bai taɓa ganin tayi ba, idan ma abu bai yi mata daɗi ba, sai dai ta yi shiru.

Suna tafe a hanya ya cigaba da yi mata hira, kamar bai ga komai ba, yana koÉ—a kyan da kayan suka yi.

Sai dai gaba É—aya shima jikinsa yayi sanyi, basarwa kawai yake yi.

Wani restaurant suka je, yayi reserving VIP, aka kawo musu abinci kala-kala, amma ummi ta ce ba za ta ci ba, ya gama kawai su tafi ita hankalinta yayi gida.

"Amma mussman saboda baki je walimar nan ba na shirya mana wannan"

"Sai ka ce wani film, ni ka yi sauri mu tafi, kar na je gida na kasa kare kaina".

"Da na san zaki watsa mini ƙasa a ido, da ban kashe kuɗina ba, i did all this because of you"

Ta ɗan kalleshi ta ce "Ni ban taɓa cin abinci a waje ba, dan Allah ka yi haƙuri"

Raihan ya ce "Zan fita na baki wuri ki ci, amma idan ki ka yi mini haka ba zan ji daÉ—i ba".

Ƙarshe dan kar ya ji haushi, da ƙyar ta cakala ta ci, suka tafi gida.

A hanya yake ta ce mata tayi ƙoƙarin rarraba CV ɗin ta, ko Allah zai sanya ta samu wani aikin da ya fi wanda take yi.
Ta ce masa zata jarraba yin hakan.

Raihan ya dage sai ya mayar da ummi ƴar gayu, ta hanyar kaita wurare da zasu ɗebe mata kewa, ba tare da ƙetare iyakar addini ba.

A É—an fitar nan da ummi suke yi, take ganin mata kala-kala, masu dressing kala-kala, ba ta sani ba ko rashin shiga cikin mutane ne ya sanya ita duk ba ta iya wannan abubuwan ba, hatta É—aurin É—an kwalin da ta kan gani a kan mata yana burgeta, amma ita ba yi take yi ba, daga aikin gida sai makaranta ba ta da wani hope balle tayi tunanin wata kwalliya.

Da Raihan yaje gida ya duba ledar da ummi ta bashi, sabon agogo ne kar, da links sai littafin azkar babba, da carbi counter.

Ta yi rubutu kamar haka "Allah ya taya riƙo mai girma MD, wannan ce gudunmuwata, ban san me kake buƙata ba, amma ina fatan ba zaka raina kyautar yayarka ba, Ummi"

Ya yi murmushi a hankali ya ce 'Kin rama kenan, a taƙaice kin dawo mini da kuɗina'

Ya kirata a waya, sai dai wayar a kashe.

Ya kashingiɗa yana tuno ummin, mussaman ɗazu da ta saka doguwar rigar abaya, tayi wani irin kwwarjini da kyau, daga cikin abun da ya ɗau hankalinsa dogon gashin ta har tsakiyar bayanta, ya fara tunanin anya ummi ba ta haɗa dangi da wani ahali na yankin ƙasashen ƙetare ba? Idonta da gashinta, sun nuna hakan.

"You are beautiful fa ummi" ya faÉ—a a fili ba tare da ya shirya yin hakan ba.

Dubu talatin É—in nan da ya bata, dubu biyu ce tayi saura, dan sai da ta saya wa kawunta turare, ta saya wa Abdul, sai Æ´ar É—akinta wato noor, har da su farida, amma kausar ta yatsuna fuska ta ce Allah ya kiyaye ta shafa wannan abun kamar Æ´ar bori, suka bar ta da abun ta.

Duk da abun da suka yi mata, ummi ta ji daÉ—in murna da addu'a da dr. Yayi mata, hakazalika Abdul ma yayi mata addu'a sosai, mutuniyarta kuwa kasa zama wuri É—aya tayi, dan Æ´ar tsana ta saya mata.

Ummi ta yi mamakin yadda aka yi kuɗin ma suka isheta, ba ta taɓa tunanin haka yi wa mutum kyauta yake da daɗi ba, ayi ta yi maka addu'a.

Kwanaki biyu da fitar su ita da raihan, tana É—akinta tana tilawa Abdul yayi sallama, ta kaste karatun tare da amsa masa.
Ya miƙa mata ledar hannunsa, ta karɓa tana kallonsa bakinta fal tambaya.
Kan tayi masa tambayar ya ce "Wani guy ne muka haÉ—u a waje ya ce na baki, wani É—an dogo mai haske" gaban ummi ya faÉ—i, ta san ba wani bane face raihan.
Abdul bai sake yi mata wani bayanin ba, ya fita daga É—akin.
Jikinta na rawa ta hau duba kayan, dogwayen riguna nan ne da suka sayo, har takalman da komai.

Da sauri ta tashi ta leƙa ƙofar ɗakin, ta tabattar babu kowa, me raihan yake nufi ne? Wannan kayan idan aka tanbayeta ta ce a ina ta samu?

Layinsa ta fara kira, ya É—aga a nutsensa tare da amsa sallamar da tayi masa.
Chapter 67 · 0% Book details