Sashe 108
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raihan ya sosa kai yana murmushi ya É—ago ummi daga jikinsa ya ce "Abubuwa da yawa mana, next time karki sake shiga wurin ma'aurata anyhow please, ba girman ki bane"
Ummi ta yi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Maryam, yau ina da babbar baƙuwa"
"She ruin my enjoyment" yayi maganar a taƙaice.
Maryam kuwa ta ɓarke da masifa ta babu gaira babu dalili, tana alwashin sai ta raba auren nan, dan asiri ummi ta yi wa raihan.
Ummi ta yi shiru, zuciyarta na yi mata zafin cin zarafin da maryam ke yi mata, kuma ta ƙi ɗaga jikin raihan.
A hankali ya ce wa ummi "Go and get some rest, kin san baki gama warkewa ba" ta jinjina masa kai, ta nufi É—aki.
"Dubeta dan Allah, ko kunya ba kya ji" sai dai abun da Maryam ba ta sani ba, har da hassada ta kamata, gidan da raihan ya saka ummi ya fi nata haɗuwa, kuma gaba ɗaya yau ta nemi munin ummi ta rasa, a dire take ba abun da wata ƴa mace za ta nuna mata. Ga wani irin ƙamshi da take yi, yau ta ga ainihin kyawun surar da Allah ya yi wa ummi. Dan da ta juya baya ma tana tafiya, ga gashin ta ya kwanta a bayanta, kamar ba bahaushiya ba, dole yaro ya rikice ta faɗa a ranta.
Ummi na barin wurin ya haÉ—e rai ya kalli Maryam ya ce "Idan har kin san zaki zo gidana ki ci mutuncin matata kar ki sake zuwar mini gida ki É—aga mini hankali, Mami idan tayi ta isa ne, ke kuwa kin yi kaÉ—an duk rashin mutuncin da na yi miki ke ki ka saya".
"Ni ka ke cewa kar na sake zuwar maka gida? Kodayake ba laifinka bane ba, an kai sunanka gaban bokaye an mallakeka"
"Bakomai, ni bokan ya taimakeni da ya mallake mata ni, kar ki sake zuwar mini gida ki É—aga mata hankali, definitely na san sai ta yi kuka cin mutuncin da ki ka yi mata".
Maryam ta ja numfashi ta jinjina kai ta ce "Bayan cin mutuncin da ta yi mini, kai ma ka É—ora naka, sai na nuna wa Salma haryanzu kanta a kwano yake, yarinyar da na taimakawa a baya mara galihu irint...
"Kema ta taimaka miki, dan a irin daƙiƙancinki, ba dan taimakon nata ba asarar kuɗin tara za ayi a banza, dan haka juna ku ka taimaka" suka yi wa juna kaca-kaca suka yi faɗa ta tafi ta bar gidan.
Ummi kuwa ta din ga saƙe-saƙe a ranta, tabbas yanzu tun da har ta riga ta yi aure ta bar gida, raihan ne kawai ya rage mata source of happiness, idan ba ta yi da gaske ba, Maryam za ta iya aikata abun da ta ce, dan ba mutunci ta cika ba, dan haka a wannan karon ba ta tunanin za ta iya ɗaga wa maryam ɗin ƙafa.
Raihan ya bi ta É—aki ya din ga rarrashin ta. Sai dai ta kasa daurewa, sai da ta din ga yi masa kuka yana rarrashinta.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga sunan Yaya Salim, ya É—aga suka gaisa, Salim ya ce "Ina waje"
Raihan ya ce "Yaya ka shigo falo, gani nan" ya ajiye wayar ya É—auki jallabiyarsa ya ce "Yaya ne ya zo, ki wank fuskarki ki zo"
"Allah ya sa ba laifi na yi masa ba"
Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, yaya Salim ya ce ke ƙanwarsa ce, da ya karɓo amanarta a wurin mama, idan ban kula da ke ba, ni da shi ne" Ummi ta yi murmushin yaƙe, ta sanya kaya suka fito.
Sai dai tun da suka fito yake bin su da kallo, suka zauna ummi ta gaishe shi, ya amsa tare da cewa idan ina ganinku taren nan, sai na ji kamar nima na yi auren nan.
Da sauri Raihan ya ce "Yaya da gaske, dan Allah ka yi"
Salim yayi murmushi ya ce "Ya ƙarfin jikin naki" raihan ya ce "Ta ji sauƙi sosai"
"Kai na tambaya?"
Raihan ya ce "Allah ya baka haƙuri".
"Meyafaru ne? Na ga kamar fuskar ku da damuwa, mussaman ummi".
Ummi ta ce "A'a yaya, komai lafiya ƙalau"
Salim ya gyara zamansa ya ce "Yadda ku ke ɗin nan gwanin sha'awa yayi wuri ace kun fara samun saɓani, duk da ma bana tunanin hakan ne, na san akwai abubuwa marasa daɗi a ƙasa, amma ku yi haƙuri da juna".
Raihan ya ce "In sha Allah babban yaya"
Ya ce 'Masha Allah, dama zan wuce ne na ce bari na zo na sake dubata, amma Maryam ta zo gidan nan ko?"
Gaba É—aya suka kalle shi a tare.
Raihan ya ce "Eh ta zo"
"Tun da na ganta a gida jiya na san za ta zo, kuma yanayin ta ya nuna mini ba zuwan arziki tayi ba, ta yi miki wani abu mara daÉ—i ko?"
Ummi za ta yi magana raihan ya ce "Haka ne yaya, amma in sha Allah i can handle it"
Salim ya miƙe ya ce abun da nake son ji kenan, bai sake ce musu komai ba ya fice.
"MD meyasa zaka gaya masa haka?"
"Wai dan kin ga yana shiga sabgar aurenmu? Idan na yi masa ƙarya a gabanki zai zageni, ba a ayi masa musu, na gaya miki kallon ƙanwa yake yi miki,ko na ɓoye masa idan ya gano na kaɗe"
Ummi ta ce "Ni dai duk da haka da baka gaya masa ba, ai na san da ta tafi shikenan.
Salim kuwa fitar maryam ya gani a mota, ya samu nihal ya ritsata ya tambayeta ina maryam ta tafi daga zuwanta jiya? Ba ta ɓoye masa ba ta gaya masa gidan raihan ta tafi.
Maryam kuwa bayan komawarta gida, ta samu mami ta zayyane mata abun da ya faru da wanda bai faru ba, wanda hakan ya ƙara tunzura mami, mussaman da maryam ta gaya mata baƙaƙen maganganun da ummi ta faɗa wanda suka ba ta mamaki.
Bayan la'asar Salim ya shiga sashin mami, wanda rabonsa da sashin, yayi shekaru. Mami na cin abinci maryam kuma na kallo yaranta na ta wasa a falon.
Ya tsaya a kan Maryam ya ce "Zuwa na yi nayi miki gargaɗi, idan ki ka sake taka ƙafarki a gidan raihan, ki ka ci zarafin matarsa wallahi sai na casa ki, ba soja ba ko bindiga ki ke aure tun da ke mahaukaciya ce"
Mamk ta miƙe tsaye ta ce "Saurara kai a wa?".
"Ni a wanta, wanda na isa na saka na isa na hana, wallahi ba zan yi kaffara ba, na sake jin labarin kin je masa gida kin yi masa hauka, sai na ci.... Ya É—irka mata ashar mai zafin gaske.
"Shaye-shayen ka yi zaka zo ka sauke iskancinka a nan?"
Salim ya ce "Ras nake, sai dai da sannu zaki gane manufata, let her make another scene zaku gani" fuuu ya fice kamar zai tashi sama.
"Yaushe yaron nan ya samu kusanci da raihan, har yake shiga cikin lamarinsa haka?"
Maryam kamar tayi kuka ta ce "Mami ƙarata suka kai masa kenan? Mami raihan ya fifita matarsa a kaina, mami ki yi wani abu a kai tun kafin raihan yafi ƙarfin control ɗinki".
Babu tunanin komai, ta hau kan maganar ta zauna.
Ummi tana sallar magariba a bedroom ɗin ta, ta ji yo hayaniya a falo, wanda ko tantama ba ta yi muryar mami ce, mamin da tun da aka yi bikinsu ba ta taɓa takowa gidan ba.
Bayan ta idar da sallar, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ummi ta fita falon, raihan yana ta ƙoƙarin shawo kanta daga masifar da take yi.
"Mami sannu da zuwa" riƙe sannu da zuwanki, idan kin so ma ki kirani da bilki, dan ban haifeki ba, saƙon da ki ka bawa maryam na ji, na zo kuma in nuna miki na isa da ɗa na, kai kuma ka aiwatar da abun da na ce"
"Mami dan girman Allah ki yi haƙuri, mai zai sanya na aikata haka babu wani dalili".
"Ni ka ke gaya wa haka? To ka saka a ranka zaka canza wata uwar bani ba, kai ba ka isa ba ma, wallahi sai ka saketa raihan na riga na rantse maka, ko in yi maka abun da ba ka zata ba" tayi maganar tana watsa masa biro da takarda.
Tuni jikin ummi ya fara rawa, ta ji numfashin ta kamar zai ɗauke, da sauri ta bar falon, ta tafi ɗaki, lallai tsuguno ba ta ƙarewa rayuwarta ba.
Ta ɗauki ƙaramar akwatin ta, ta zuba kayanta, ta buɗe wurin da raihan yake zuba kuɗi ta ɗiba ta zuba a jakarta ta ɗauki ATM ɗin ta ta fito, tana zubar da hawaye.
Ta tarar da raihan a zaune ya dafe kansa, cikin tashin hankali bai yi zaton mami zata aikata masa haka ba.
Tana ganin ummi ta ce "Ita akwatin ai na san ba daga gidan ubanki ki ka zo da ita ba, dan haka ajiyeta" ummi ta durƙusa ta kwashe kayanta ta ajiye akwatin.
Raihan ya miƙe yana kiran sunanta.
"Wallahi ka taka ka bita ban yafe maka ba!!!. Ummi ko waiwayawa ba ta yi ba ta fita.
"Kuma ka san duk yadda zaka yi ka kareni a wurin babanka, wallahi ka kuskura ka gaya masa umarnina ne ka rabu da ita sai na saɓa maka, ba zan zuba ido ka zama soko ba"
Zuciyar sa na tafasa ya ce "Mami kina ganin wannan hukuncin shi ne farincikin ki ko? Ni kuma kin ƙuntata mini, shikenan tun da haka ki ka yanke kin isa ne, na gode"
Ƙura masa ido ta yi ta ce "Raihan kuka zaka yi dan na rabaka da masifa" ya kalleta hawaye na gangarowa daga idonsa, ya san komai zai ce mata ba zata fuskanci irin son da yake yi wa ummi ba.
A falon gida ummi suka yi karo da farida, da ita da kausar da alama ba su daÉ—e da dawowa daga unguwa ba.
Ta ƙarewa ummi kallo da kaya a hannu ta ce "Lafiya?"
"Ya sake ni ne" ta faÉ—a a hankali.