← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 134

Sashe 41

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya girgiza kai ya ce "Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya É—ebo da zafi bakinsa, kin riga kin sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaÉ—ai ne É—a a dangi ba".

Ba ƙaramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ƙiri-ƙiri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaɓi tonuwar asirin su.

Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaɓa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da ita.

Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuÉ—in motar, ya basu kuÉ—in kashewa, suka tafi.

Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur'ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da aka yi.

Duk da kuÉ—in da yahaya ya bawa Iya sun saka ta É—an sassauta fushinta, amam ta sha takaicin rashin amincewa ya É—auki Idiris a mayar da aurensa da ummi, ta din ga zagin ummi tana tsine mata, tamkar ba ita ta haifi baban ummi ba, tare da janyo mata jafa'i kala-kala.

Ko da suka koma gida ta sanarwa Idris da babansa cewa yahaya ya goya wa ummi baya, yaƙi yadda da magabar da ta je masa da ita.

Hankalin Idris ya tashi, dan kuwa baban hindu ɗan bala'i ne, ya ce ba zai yadda ba, ba za a zubar da cikin jikin hindu ba, sai ta haife shi, kuma sai sun karɓa sun riƙe, hindu na da wani yaya da yake soja, kurtu nema a cikin sojojin, amma ya zamewa su Iya barazana, dan kuwa shi ma cewa yayi sai ya saka bomb a gidan su iya, ko ya kama Idris ya harbe shi, tun da aka taɓa ƙanwarsa.

Magaji ya san duk barazana ce, babu ɗaya da zai faru, amma yayi shiru da bakinsa, saboda sun cancanci koma menene ya same su, dan da idris bai taɓa ƴar mutane ba, babu mai ɗaga musu hankali, kuma ya danganta hakan da alhakin ummi

Babu yawon da Iya ba ta yi wurin malamai ba, a kan a rufe bakin baban hindu, da ita kanta hindun da yayanta, amma abu ya ci tura, dan har barzanar kai su gaban hukuma baban hindu yayi idan suka cigaba da takura masa a kan maganar cikin nan, ko kuma ya saka É—an sa ya É—auki duk matakin da ya ga dace a kan su.

***

Tafiyar rahama daga gidan dr., Bayan an yi mata aure bata sauya zani da komai ba, daga wahalar da ummi take yi, dan har undeas É—in su intee ba zasu wanke ba, sai a haÉ—a mata a kayan wanki, duk ta haÉ—a ta wanke su.

Sai dai tun ba aje ko ina da tafiyar rahaman ba, ta fara sintirin kawo ƙara wurin kawu yahaya, dan dama mahaifinsu ya rasu, duk wani abu na jin daɗi da ta sanya ran samu a gidan mijin, sai ta ga akasin haka, yana da hali ba bashi da shi ba, amma hatta shinkafa da man da za ta ci, sai ya ƙulla mata, ba yadda da zuwan baƙi gidansa ba, sai an kira shi ya bayar da iznin a zo, idan bai bayar ba kuwa babu mai zuwa.

Kawu yahaya ya kira shi, dan a samu masalaha amma ya nuna shi tsarin gidansa ne a haka, dan haka dole a bar shi yayi yadda yake so.

Haka nan kawu yahaya ya ce sai dai tayi haƙuri, yace shi tsarin gidansa ne a haka.

Tun da shekaru goma sha shida, samari suka fara bin intee, hakan ba ƙaramin farantawa farida yayi ba, tana ganin intee mai goshin arziki ce, shekara goma sha shida, samari sun fara sintiri, dan ma dr. Yana korarsu ya ce yarinyarsa tayi ƙanƙanta sai ta fara karatu idan ma auren zai yi mata.

Lokacin da ummi ta fara period babu wanda ta gayawa, dama ta riga ta san shi tun a karatuttukansu na makarantar islamiyya da na boko ana gaya musu shi, sannan an koyar da su tsabta a lokacin da mutum yake cikin jinin  haili. Dan har wata ƙungiya ta je makarantar su suka wayar musu da kai, a kan jinin haila da tsafta, dan haka babu wanda ta gayawa da ya same ta.
Ta samu kayanta da suka É—an kwana biyu, ta yayyanka É—ankwalin, take amfani da shi.
Idan kuma Allah ya sa dr. Ya bata kuɗi, babu abun da take fara saya sai pad, tana iya haƙura da kowace irin buƙata ce da ita, ta sai pad ɗin da za ta yi amfani da ita da kuma farin muski.

Sintirin samari zuwa wurin intee, ta din ga wani iyayi tana yauƙi, ya sanya aka fara yi wa ummi gori da habaici, domin kuwa babu wanda ya taɓa zuwa ƙofar gidan ya ce yana sallama da ita, ko a hanya ma babu wanda ya taɓa biyota ya ce ya na so.
Su yi ta yi wa ummi wulaƙanci, wai farar mace Alkyabbar mata, baƙar mace bolar maza.
Kodayake bolar akwai wadda ake iya recycling, wata ta riga ta zama waste gaba É—aya bata da mamora.
Ko sai sun ga ummi su fara wankan baƙi asarar ruwa, ko yayi ma kamar bai yi ba, blaki kalar dauɗa, su din ga yi suna tuntsura dariya.
Ummi kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta cigaba da sabgoginta, duk da a ƙasan zuciyarta kalaman na su na tasiri a cikin zuciyarta, tana jin babu daɗin cin mutuncin halittar ta da suke yi.

Haka Maryam ma, kasancewar ta kyakykyawa, kullum ba ta da aiki sai bawa ummi labarin saurayinta kaza yayi mata kaza, ko ya bata abu kaza.
Ba maryam kawai ba, Æ´an ajinsu ba su da aiki, sai hirar samari, ita kuwa da ta san ba ta da kowa, ta rungumi litattafanta yadda yakamata.

Idan suka so yin dariya kuwa, sai su yi ta zungurar ummi, suna tambayarta wai ita waye nata saurayin, ta gaya musu fari ne ko baƙi, dogo ko siriri.

Kawai sai tayi murmushi ta yi musu shiru, taƙi kula su.

Maryam ce ta fara bata shawara "Ummi, yakamata ko ɗan mayukan nan na zamani ki ɗan din ga shafawa, ko kema kya yi haske, maza ba sa son baƙar mace, ummi kin yi duhu da yawa, duk kwatancen baƙin da za ayi a makarantar nan da ke ake yi, idan ki ka shafa mai ki ka ɗan yi haske, ko yaya zaki samu saurayi, ko zaki ji daɗi duk mu yi aure mu bar ki? Ni fa mami ta ce ina candy aure za ayi mini, na cigaba da karatu a gidan mijina, amma ke kullum kin ƙi wayewa, ga uban hijjaban da ki ke sawa, ba kya kwalliya kamar mu, bayan hijjabi har da wani uban niƙab, to waye zai ce yana son ki, kalli ranar da muka je barkar gidan su Saratu, kowa yayi kwalliya amma ummi ke kin zunduma over size hijjab fisabilillahi. Ranar da babu school, ki zo gidanmu akwai wata mai mayukan gyaran jiki, muje ta haɗa miki mai sai na biya"

Ummi shiru tayi tana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai ɗacin gaske, da yake yi mata kai komo tsakanin maƙogwaronta da ƙirjinta, wannan shawara maryam take bata ko ci mata fuska.

"Ina magana kin yi mini shiru" Maryam ta yi maganar a É—an hasale, dan daga abun da maryam ta tsana a halin ummi bai wuce miskilanci da shariya ba.
Wanda ba wai miskilancin bane kawai, tana gudun shiga harkar mutane, kar tayi wani abun da za aci mata mutunci.

Ummi ta ɗago ta kalli maryam, hawaye har ya zagaye cikin fararen idanuwanta, ta ɗan juya brown ɗin ƙwayar idonta ta ce "Maryam, I won't bleach my skin, ko a so ni a haka, ko a ƙyale ni, banbancin fari da baƙi a wurin Allah, wanda yafi tsoronsa mu ƴan adam mune muke ɗorawa kanmu".

Cikin ƙuluwa maryam ta ce "Au dan na baki shawara ina nema miki mafita, shine ki ke kuka, har ki ke nema ki kafirta ni? To ki ƙarata ummi, amma zaki ce na gaya miki, wallahi babu wanda zai aureki da wannan baƙin da gidadancin"

Ummi tayi murmushi mai ciwo hawayen na zubowa ta ce "Ba ke ki ka fara faÉ—ar haka ba maryam, an daÉ—e da gaya mini ba zan auru ba ni mummuna ce, dan haka ban sa aure a ka ba dama, nima na san maza farare suke so masu kyau, in dai ubangijina yana sona shikenan maryam" tayi maganar cikin sanyin halinta.

Sai kuma jikin maryam yayi sanyi, ta ce "Am sorry please, ba ina nufin na ɓata miki rai ba ummi, mafita nake nema miki"

Kawai ummi ta tashi ta bar ajin, domin kuwa an kaɗa ƙararrawar tashi.

Kai tsaye gida ta nufa, tana tafe tana hawaye ta cikin niƙabinta.

***
Babban mutum ne zaune mai cike da nutsuwa da kamala,kallo ɗaya zaka yi masa ka san a cikin hutu yake, falon da yake zaune kawai ya ƙawatu dai-dai gwargwado.
A hankali yake zuƙar tea ɗin da yake hannunsa, yana kallon ƙatuwar plasma tv da ke manne a jikin bango, sai dai kana gani ka san ba kallon yake yi ba, zancen zuci yake yi.

"Alhaji ya dai?"

Wata mata tayi maganar tana ƙoƙarin zama a kusa da shi.

"Bakomai" yayi maganar yana murmushi.

"A'a da komai mana, zancen zuci ka ke yi, shekaru sun ja, yakamata a din ga rangwatawa kai, kar wani ciwon ya kama ka"

Ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ce "Da ciwo zai shigeni saboda tunani, da tuni ya shige ni hajiya. Lokaci yayi da yakamata na huta, huta nake buƙata amma ki duba ki ga haryanzu ban huta ba, ni nake fama da harkar kasuwancina, gaba ɗaya yaran nan basu saka komai a gaba sai shashasha. Na tara dukiya, suna ta bushashasha, gaba ɗaya babu hankali ko nutsuwa a cikinsu da zai tallafe ni yanzu, su karɓi ragamar kasuwancin ni na huta.
Chapter 41 · 0% Book details