← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 134

Sashe 93

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salim ya yi ajiyar zuciya ya ce "Idan ka kai musu sai dai ka yi musu bayani, na ji ka ce maiduguri zaka kai mata, ana yi wa iyaye akwati fa su ma, dole ka yi ƙoƙarin fitar da su kunya, aurensu da tsada sosai"

Hajiya ta ce "Kai a ina ka sani?"

Ya amsa mata da "Abokina umar É—an can ne ai, kuma Æ´ar can ya aura, ni da shi muka din ga shirin bikin ai"

Cikin marairaicewa raihan ya ce "To ka taimaka mini mana nima"

Ya girgiza kai ya ce "Bana son babarku ta zo ta ce ba a kyauta ba"

Hajiya ta ce "Ba ƙaninka bane ba? Babu abun da za ta ce"

Haka kuwa aka yi, dan sai da suka sake sayen akwati, aka zuba atamfofi da shadda, wanda ake yi wa iyaye, sannan ya gaya masa zai bayar da kuÉ—in turaren wuta.

Gwiwar raihan ba ta yi sanyi ba, dan shi a ganinsa komai zai kashe wa ummi bai faÉ—i ba.

Yadda raihan ɗin ya din ga yi wa salim biyayya, ya sanya da Hajiya ta lallaɓa shi ta ce su tafi tare maidugurin bai yi musu ba.

Can Maidugurin ma da ummi ta ce musu raihan zai zo, aka din ga shirye-shiryen tararsa, dan bai gaya mata da Salim zai zo ba ma.

Mami ta so hana tafiyar nan, amma Alhaji ya taka mata burki, ya ce babu abun da zai hana raihan zuwa maiduguri, tun da matarsa a can take.

Kasancewar ana idar da sallar asuba suka tafi, ƙarfe sha ɗaya na safe suka sauka.

Suka bi adress É—in da ummi ta basu har gidan suka je.

Kasancewar sun yi shigar kamala, daga shi har Salim, hakan ya ƙara musu kima a wurin ƴan uwan ummi.

Sai rarraba ido kawai yake yi ya ga ummi, aka kawo musu abinci na alfarma.

Sun kai a ƙalla awa guda, yaya maryam ta tsare ummi, ta hana ta zuwa, sai daga baya ta shirya cikin lafaya mai kyau, sai ƙamshin turare take yi, hujin hancin da suka yi mata, ta saka barimar azurfa, sai ƙyalli take yi a kan baƙar fuskarta.

Da tayi sallama tare suka É—aga kai suka kalli ummi, babu kunya raihan ya kafe ta da ido.

Salim ya jinjina kai a ransa ya ce "Lallai yaron nan akwai tsaurin ido"

Ummi ta wani ƙara cika sosai, ga wani irin ƙamshi da ya cika ɗakin.

"Oyoyo sweetheart" yayi maganar cikin sanyin murya.

Durƙusawa tayi har ƙasa ta gaida Salim, ya amsa mata fuskarsa babu yabo ba fallasa.

Ta juya wurin raihan ma ta gaishe shi, ya amsa yana washe baki.

Ya ce "Tun da ga yaya salim, akwai kuÉ—i a jikina, sai a É—aura yanzu kawai" hararsa tayi ta samu wuri ta zauna.

Salim ya mayar da hankali a kan wayarsa, kamar bai san suna wurin ba, raihan kuwa ya rasa control ya din ga zuba a gaban Salim, ummi kuma kunya kamar ta nutse.

"Baby me mama take baki ne? Kin ƙara ƙiba, kalli skin ɗinki"

"Ni fa bana son ƙibar nan" ta faɗa a hankali.

"Ni kuma ina so, baki ga kyan da ki ka ƙara ba, kin ji ƙamshin da ki ke yi kuwa? Anya zan iya jiran lokacin nan, Innalillahi kin ganki kuwa? You look take away, ko dai in yi zamana a nan"

Dukan da Salim yayi masa a ƙeyarsa ne, ya sanya shi yin shiru yana sosa kai.

Ummi ta yi masa gwalo, ta ce "Bari na je n yi wa mama magana, mu shiga ku gaisa" ta tashi ta fita.

Tana fita Salim ya ce "Kai dan ubnka a gidan sirikai fa ka ke? Wannan da bamu zo tare ba me zaka yi?"

Raihan ya ce "Bakomai"

Yayi ƙasa da murya ya ce "Zaka ƙara da kuɗin gyaran jikin da ake yi mata, kara fa aka yi maka da duk ba ta tambayeka ba, zaka saki bakin aljihu tun da ɗiyar ƴan maiduguri zaka aura"

Raihan ya ce "To ai duk ba ta gaya mini ba"

Salim ya ce "Ni yanzu na gaya maka, kuma wannan ginin da ka ke yi, ka je ka ce wa Alhaji ya saya ko ka bashi jingina, ka samu gida mai kyau ginanne ka saya"

Raihan ya ce "To ai ina son gidan sosai "

"To ka ce wa Alhaji ya baka gudunmawar bikin, ka ƙarasa"

Raihan ya yi dariya ya ce "Haka za ayi yaya"

Ya É—aga masa gira.

Ummi ta ce "Bisimillah ku shigo"

Suka tashi suka shiga, suka din ga gaisawa da mutanen gidan, ummi tana gabatar musu da kowa.

A É—akin mama suka yi sallama, suka zazzauna, ta din ga murmushi tana amsa musu gaisuwar.

Ta kalli yaya maryam ta ce "Yaya, wannan suwaye?"

"Sirikanki ne, wannan ne zai auri ummi"

Sai tayi dariya ta rausayar da kai ta ce "Ummin za a yi wa aure yanzu? Ai tayi ƙarama da yawa"

Maryam ta ce "Wai ke ummin haryanzu a kan cinyarki take ne tsawon shekaru ba ta girma ba?"

Ta kalli raihan ta ce "To kai ba ka ga munin na ta ba? Iya ta ce mummuna ce babu mai aurenta"

Raihan ya ce "Haba mama, ummi ba mummuna ba ce ba, kalleta fa ki gani tubarkallah masha Allah"

Ta ce "Yauwwa, da ma na faÉ—a, wani zai ce yana son ummi a haka, amma iya ta din ga yi wa ummi ba'a, har sauran yaran gidan, su yi ta ce mata mummuna ko wasa da yara ba ta yi, kuma duk iya ce ta janyo, da ta tsawatar ai ba za su yi mata ba ko?"

Raihan ya ce "Gaskiya ne, amma ummi ai mai kyau ce, ga ilimi da tarbiyya, ta cancanci a so ta"

Yaya maryam ta ce "Dan Allah ki daina zancen nan da ya wuce"

Salim ya ce "Kamar tana jin daɗin hirar, ki ƙyaleta"

Mariya ta sake cewa "Ka san har malaman makarantar su ummi, wai su yi ta ce mata baƙa, na yi ta kuka, ko ace idonta irin na mayu, da ta fita yara su yi ta cin zalinta, shiyasa ni da babanta mu yi ta sonta, ba ka ga yadda yake son ta ba"

Raihan ya ce "Allah sarki, mu ma muna son ta sosai"

Ta kalli Salim ta ce "Ka ga yadda kakarta ba ta son ta ko? Amma bayan mutuwar baban ummi, matar nan ta ƙwace mini ummi, ba fa iya kula da ita take yi ba, an ce sun azabtar mini da ummi sosai da sosai" tayi maganar tana share hawaye.

Salim ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kuka dan Allah".

Ta kalli raihan ta ce "To ka ga dai yarinya ce, dan Allah ka kula da ita sosai, ka din ga ba ta abinci, idan magariba tayi a saka mata kayan sanyi, cikin dare ma a tashe ta tayi fitsari"

Ya ce "Duk za ayi mama, ai ummi yarinya ce kyakkyawa, duk za a din ga kula da ita"

"Eh, to amma ban bar maka ita ba fa, zaka dawo mini da ita"

Mama ta din ga zuba, suna hira da raihan da Salim, duk rashin sakin jikin salim, suka din ga hira da mama, wani abun idan tana gaya musu, sai tayi kuka, wasu abubuwan ma duk ummi ba ta san sun faru ba.

Har da tambayar maryam, wai anya Salim da raihan ba su ne jaririn da suka haifa ba aka ya ce ya mutu.

Gashi dai ba ta da cikakken hankali, amma a nutse take, malam kakan ummi, ya din ga yi musu nasiha, tare da gaya musu muhimmancin riƙe addu'a.

Salim suka ba su kayan da suka zo da su, Malam ya ce ai ba su suka riƙe ummi ba, dan haka babu buƙatar kawo wannan kayan.

Malam akwai kwarjini, ya kasa magana, Salim ne ya tausasa harshe tare da nuna masa cewar ba su takura ba, duk abun da suka yi wa ummi ta cancanta.

Kuɗin turaren wuta da na gyaran jiki, suka danƙawa yaya maryam masu kauri.

Mama har bakin mota ta raka su, suna cigaba da hira.

Ummi ta ji daÉ—in karamcin da suka nuna wa mama, mama har da tambayar yaushe zasu kuma zuwa? Su faÉ—i abun da zata dafa musu.

Yaya É—anlami ya ce "Ban da larura ma, yaushe mutum zai zauna ya yi ta zuba da sirikai"

Su raihan suka koma kano, cikin farinciki da tausaya wa mama da irin abubuwan da ta din ga faÉ—a game da rayuwar ummi.

Har suka je gida ummi na kiransu na jin yaya suka je gida?

Mama sai zancen su raihan take yi, ko sunansu ba ta sani ba, tun da Allah ya sa ta haÉ—u da ummi, bakinta ya buÉ—e tayi ta surutu amma da ummi take yi, sai kuma su Salim da suka zo.

Da daddare bayan su raihan sun sauka kuwa, ya takurawa ummi da waya, dan duk taka tsantsan É—in sa sai da ya kusa kauce hanya, sai dai ummi ta yi masa shiru.

Kwana biyu da komawar raihan kano,  Salim da kansa ya samu Alhaji ya tsutsiye shi, wai me zai bawa raihan na gudunmuwa.

Alhaji ya ji daɗin kulawar da Salim ya bawa raihan a kan aurensa, kuma ya lura raihan ɗin ne bai canza masa daga biyayyar da yake yi masa ba, duk da yana da wani muƙami ba.

Alhaji ya ce "Ni za a yi wa solidarity?"

Ya ce "A'a ginin da saura ne, kuma saura wata guda biki, za a kai mahaifinta ya ga gida, kuma da kai da hajiya bamu ga gudunmawarku ba"

Alhaji ya yi murmushi ya ce "Na tsaya na ga iya gudun ruwan sa ne, kuma yayi ƙoƙari sosai da sosai, kuma babban abun da ya burgeni, duk faɗi tashin da yake yi, bai nemi taimakona ba, bai kuma ci amanar da na bashi ba, ya ɗaukar mini kuɗi babu izinina ba, dan haka za a san abun yi, kar ka damu"

Ya ce "Ok, mun gode, dan Allah a bashi da kauri sosai"

"Za a duba, Salim na ji daɗin ƙoƙarin da ka ke yi masa, ka yi playing role ɗin ka na babban wa, saura kuma kai ma ka nutsu ka yi naka auren"
Chapter 93 · 0% Book details