← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 134

Sashe 35

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama kuɗin motar zuwa islamiyyar ma, idan kawu yahaya yana nan, yana bata ko ya bawa farida ta bata, idan ta ga dama ta bata, ko taƙi bata wanda zai ishe ta shima saboda ta na biyawa ɗaukko su intee daga ta su makarantar islamiyyar, dan Abdul ba lokaci ɗaya suke tashi ba, sai ƙarfe shida, su kuma tun huɗu da rabi ake tashin su.

Dan haka ummi tafiyar ƙafa ta sha, kan ta je makarantar, nan ma da ta je sai da aka daketa dan ta makara.

Zama tayi, tayi shiru a ajin, dan kamar yadda ta saba, bata da ƙawaye, dan ba ta son shiga cikin su su tsokane ta.

Haka kurum ta ɗan shagala da kallon yarinyar da take jin tsoro a ajin, mai suna maryam saboda hantararta da take yi tana kyararta, da nuna mata tsana ƙarara a fili.

Tubarkallah maryam fara ce sol, irin fulnin nan masu dogon hanci, sai azabar iyayi da iya gayu, da yawa Æ´an ajin na tsoronta, saboda azabar masifarta da rashin son rai ni.

Ba tsammani ummi ta ji ta ce "Ke lafiya ki ke kallona kamar zaki cinye ni?"

Da sauri ummi ta ɗauke kanta tare da cewa "Yi haƙuri"

"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ki ka bayar? Bana son kallo"

"Ai na ce kiyi haƙuri" ta faɗa a sanyaye.

A ranta ta ce 'Dama nima fara ce, wataƙila da ba za a tsane ni ba. Amma ai akwai baƙaƙe da yawa da ake son su, ni meyasa ba a sona?' ta tambayi kanta, wasu hawayen na rige-rigen zubowa.

Maryam ta zauna a kusa da ummi, ko a jikinta ganin ummi ta kifa kanta.

Sai da malami ya shigo ajinsu sannan ta É—ago kanta, ya yi musu karatun da zai yi musu, sannan ya basu class work.

Sai dai fa maryam ba ta iya komai ba, ta din ga rarraba ido, ga malamin ya jaddada cewar duk wanda ya faÉ—i sai ya zane shi.

Ganin lokaci ya kusa cika, ya sanya ummi buɗe mata takardarta ta ce "ki kwafa ya kusa karɓa" babu kunya maryam ta kwafe duk abun da ummi ta rubuta.

Lokacin sallar la'asar yayi, ɗalibai na ta ƙoƙarin fita daga ajin, ba tare da tuna alkhairin ummi ba, maryam ta hankaɗeta zata fita, bisa tsautsayi ummi ta faɗi ta fama ƙonuwar da take cikinta.

Ƙara ta saki, tana girgiza kanta, duk ɗaliban suka tsaya suna kallon ummi, ganin jini yana tsatstsafowa a rigar uniform ɗin ta.

Maryam a tsorace ta ce "Na shiga uku" ta durƙusa ta ɗago ummi, a zaton ta ko cikin ummi ne ya ɓule.

Ummi sai yarfe hannu take yi tana kuka, É—alibai suka taru a wurin, malamin da ya fita daga ajin ya dawo ganin É—alibai a wurin yana tambayar meyafaru, aka gaya masa maryam ce ta hankaÉ—eta ta faÉ—i.

Cikin tashin hankali ya ce a kai ummi ofishin malamai, ita ma maryam ta bisu sai an hukunta ta.

Cikin tashin hankali malamai mata suka ɗaga rigar ummi, ana ƙoƙarin gano menene yake jini a cikinta, sai dai ba kyan gani, suka tarar da ƙonuwar ta jagwale, ga ruwa ga jini ya dame da zumar da take sakawa.

Maryam na ganin haka ta fashe da kuka, ta zata duk faÉ—uwar ce ta janyo haka.

Shugaban makarantar ya dubi Maryam ya ce "Wato maryam ba kya ji ko? Zaki gane kuskurenki, sai kin daku yau É—in nan, makauniya ce ke da zaki tureta ta faÉ—i".

Malamin ya dubi ummi ya ce "Ke ya aka yi ki ka zo da wannan ciwon makaranta, meya sameki haka?"

"Ba maryam ce ta ji mini ciwon ba, dama na ƙone a gida"

"Da me ki ka ƙone, kuma an kai ki asibiti?"

Ta ce "Eh an kaini"

"A'a wannan da an kai ki asibiti, da ba ta jagwale haka ba, kuma da ba a bari kin saka kaya ba, ki gaya mini gaskiya da me ki ka ƙone?" Malamin yayi maganar cikin zare ido.

"Da ruwan zafi"

"Mamanki ta san kin ƙone?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Meyasa baki gaya mata ba?"

Cikin kuka ta ce "Ai ban san in da take ba"

"A'a to ina mutanen gidan da ki ka ƙone ɗin, ba ƴar gidan dr. Yahaya bace ne?" Ta ɗaga kai alamar eh.

"Malama zuhra, a nemo abun hawa a kai yarinyar nan asibiti a dubata, ke kuma maryam mu je office É—ina sai na hora ki"

Maryam ta fashe da kuka tana magiya, cikin ƙarfin hali ummi ta ce "Malam dan Allah kayi haƙuri, ba ta san ina da ciwo ba, na yafe mata ai"

Ya ce "To zan duba, tashi a kai ki asibiti, daga nan a mayar da ke gida".

A asibitin ma, ma'aikaitan sun yi faɗa sosai a kan sakaci da lafiyar ummi, dan da ƙunar zata iya zama infected ta taɓa sauran sashin jikinta, bayan ta zama gyambo.

Suka ce lallai a kula da ummi, a samu ƙunar ta warke, kuma a zurfafa bincike dan wannan ƙunar ba tayi kama da ta ruwan zafi ba.

Ummi ta sha kuka, saboda yadda aka dirje ƙunar nan tas, aka saka magani, aka bata magungunan sha.

Sai dai da malama zuhra ta ce ta kwatanta musu gidansu a mayar da ita ta ce "A'a a mayar da ni makaranta, idan aka tashi zan ɗaukko ƙannena daga islamiyya"

"A haka da wannan ciwon" malamar tayi maganar tana kallon ummi.

Ummi ta jinjina mata kai.

"A'a ba zai yiwu ba, mu je gidan naku, a saka wani ya É—aukko su".

Kuka ummi ta fara tana yi wa malamar magiya, a kan ta ƙyaleta a tashi ta ɗaukko su daga makaranta.

Ba ta da zaɓi, suka koma islamiyyar ta gaya wa shugaban makarantar duk abun da ya faru.

Suka yi waya da kawu yahaya, suka tattauna, ya ce a mayar da ummi gida, zai yi waya makarantar yaran, su jira yayansu sai su taho tare.

Da ƙyar ta yadda da hakan, saboda tana tsoron abun da ka iya biyo bayan rashin ɗaukko su daga makarantar.

Cikin sa'a malamar ta fuskanci yanayin da ummi take ciki na tsoro, dan haka a ƙofar gida suka yi sallama ummi ta shiga.

Har ta tafi É—akinta ba wanda ya san ta dawo, saboda ana ta hada-hada a gidan, Æ´an barka na shige da fice.

Ta kasa fitowa daga É—akin, saboda tsoron kar su kuma dukanta.

Sallamar kawu yahaya ta ji a É—akin, ta tashi da sauri, tana gaishe shi.

"Ya jikin naki?"

"Da sauƙi"

"Mu ga ciwon" a hankali ta ɗaga masa cikinta ta ƙonu sosai da sosai, ya zubawa ƙunar ido sannan ya kalleta ya ce "ya aka yi ki ka ƙone?"

"Da ruwan zafi" ta faɗa tana ƙiƙƙifta ido, saboda ta san ƙarya tayi.

"Meyasa baki gaya mini ba?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Wannan ƙunar ba ta yi kama da ta ruwan zafi ba, ki gaya mini gaskiya.

"Da gaske nake..." Ba ta ƙarasa ba ya ce "Shaidar iron tayi, kalli yadda shape ɗin ƙonuwar ya tafi, ki gaya mini gaskiya".

Ta É—an yi jimm sannan ta ce "Idan na gaya maka ba zaka gaya wa maman su Abdul ba?"

"Ba zan gaya mata ba"

"Ina guge Abdul ya ce zai tayani, ya ƙonawa mamansu riga, ta zata nice shi ne anty rahama ta danneni, suka ɗora mini iron. Dan Allah Abba ka gaya musu bani na saka anty farida ta faɗi ba, sun ce ni na kusa kasheta wallahi ba ni ba ce, fitsari na yi da na ji zafi, shi ne ta zame ta faɗi" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.

Ayshercool
08081012143
What's app only please 🙏
                         *CUTARWA*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P16

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI

P16

Ƙurriii kawu yahaya ya yi wa ummi da ido, abun ya girmame shi, bai taɓa zaton mugunta da zaluncim da farida za ta yi wa ummi zai kai haka ba.

Ya sauke numfashi da ƙyar ya ce "Ya isa haka ki share hawayenki, ki daina kukan ya isa ba zan gaya mata ba, kuma na san ba zaki taɓa iya cutar da kowa ba, duk wanda ya cutar da ke, shi ma Allah ba zai bar shi ba, ki yi haƙuri ummi, in sha Allah gobe in Allah ya kaimu zamu koma asibiti, tun da yau an yi dressing ɗin.

Mun yi magana da malaman islamiyyar ku, na biya kuÉ—in maganinki, sannan sun ce ki zauna a gida sai kin warke".

Ummi kamar ta ce masa gara ta cigaba da zuwa a haka, dan ta san zamanta a gidan nan ba hutawa za ta yi ba, amma ta dake ta ce "To kawu na gode sosai"
Chapter 35 · 0% Book details