Sashe 4
Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wani irin mugun sauri zuciyar mariya ke yi, ƙuruciya ga yaron da har ya san, ya toshe mata baki da tsumma, ya keta mata haddi, shi ake kira da ƙuruciya.
Jiki a sanyaye balarabe ya ce "Shikenan iya, duk ba za ayi haka ba, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba, an bar maganar da yardar Allah"
Ta kalli saurayin yaron ta ce "Kai kuma wuce ka bani wuri, wallahi ka sake aikata makamancin haka, da kaina zan ci ubanka na hukuntaka. Wuce ka bar É—akin nan". Ya fice sumi-sumi ya ci bulus.
"Ke kuma ki daina wannan kukan, ki tashi ki dafa ruwa, ki sakata a ciki, kiyi haƙuri, ko ki cigaba da kuka baƙin ciki ya kashe ki" daga haka ta juya ta fice.
Tana fita mariya ta kuma rushewa da kuka ta ce "Yanzu shikenan baban ummi, yaron nan ya ci bulus kenan? An lalata mini rayuwar Æ´a, har iya na cewa wai babu lallai wani ya aureta, wane irin abu ne wannan?"
Zuciyar sa fal takaici da ɓacin rai, saboda kar ya sake karya wa mariya gwiwa ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri mariya, ki kwantar da hankalinki, kin ga iya uwata ce, ba yadda na iya, dan Allah ki yi haƙuri ki tayani yi mata biyayya, mu ɓoye sirrin nan, ko dan mutuncin ummi, kar abun yayi mata yawa. Dan Allah ki yi haƙuri mariya"
Tashi tayi ta kwantar da ummi, ta fita tsakar gida.
Babanta ya rungume ta, jikinta ya É—au zafi, tana jin yadda hawayen sa ke É—iga a hannunta.
"Ummina sannu kin ji? Meye yake miki ciwo?" Tayi shiru ba ta yi magana ba, sai sheshsheƙar kuka.
Mariya ta kawo ruwa a baho, ta fizge ummi daga hannun balarabe, ta saka ta a cikin ruwan É—umin. Sai a lokacin ummi ta zabura ta fashe da kuka, ta ce "Mama zafi".
Tana kuka ummi na kuka, ta yi mata wanka, ta saka mata kaya, ta nemi wuri ta kwanta, ta share balarabe.
Kwana suka yi ummi na koke-koke, ko barci ya ɗan ɗauke ta, sai ta zabura tana turza ƙafarta tana ihu.
Haka mariya ta kwana kuka, da balarabe ya kai hannu zai taɓa ummin, sai ta ɗauke ƴar ta, ta juya masa baya.
Wayewar garin Allah, mariya ta saba zuwa ta gaida Iya, amma a ranar taƙi kula kowa, ta ƙi ɗora girkin gidan.
Yara masu tafiya makaranta, duk sashin ta suke zuwa karɓar kunun safe, su sha su tafi makaranta, ranar shiru ba ta ɗora ba, kowa yazo sai ya koma.
Balarabe ya din ga raragefe, ya rasa me zai cewa mariya, ya san ƙarshen cuta an yi mata, ba ma ita kaɗai ba, har da shi, sai dai ba yadda ya iya sawun giwa ya take na raƙumi, iya mahaifiyarsa ce ba yadda ya iya, dole ya bi umarnin ta.
Yayi shirin sa zai fita kasuwa, jiki a sanyaye ya ce "Mariya, ko asibiti zamu kaita, na ga kamar da zazzaɓi ta kwana".
"Dan Allah ka ƙyale ni da abun da ya dame ni, ka ƙyale ni bashir ka ƙyale mini ƴa ta, duk muninta daga jikina ta fito, ni na damu da ita, tun da a gurin kai da mahaifiyar ka, ba ƴa ba ce. Tun da baban sa yana da kuɗi dole ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta, nayi imani da Allah da ɗan ka ne, yayi laifin nan, kowa sai ya ji" tayi maganar cikin matsanancin kuka.
Lallai mariya ta kai ƙarshe a ɗaukar zafi.
"Ki yi haƙuri mariya, ke kin san ina ƙaunar ƴa ta, ba yadda na iya ne, wallahi mariya ba ki fi ni shiga damuwa da tashin hankali ba, ki yi haƙuri dan Allah"
Ba ta kuma kula shi ba, ta cigaba da shafa kan ummi, da ta É—an samu bacci, tana zubar da hawaye.
Da son ransa ne, ya wuni tare da su, ya cigaba da rarrashin ta, amma ya san idan ya ƙi fita, wani tashin hankalin zasu fuskanta daga Iya.
Gaba ɗaya girkin ma taƙi yi, ummi kawai ta samawa abun da za ta ci, da ta tuna a yadda ta tarar da ummi, sai ta sake fashewa da kuka.
Iya na son yin tijara, amma tana tsoron kar abun da ya faru ya tonu, dan sun haɗu da mariya a tsakar gida,ta hango tsantsar rashin mutunci da tashin hankali a idon mariya, wanda ba ta taɓa gani ba, dan haka ta ƙudurce a kan balarabe za ta juye.
Haka kuwa aka yi, ana idar da sallar magariba, ya dawo, ya je gaishe ta, ta dira masa bala'i, tamkar ba ita ta haife shi ba, tare da jaddada masa muddin ko shi ko matarsa suka bari zancen nan ya fito, sai ta tsine masa kuma babu ita babu shi.
Yayi ta bata haƙuri, sannan ya nufi ɗakin su, ya tarar da mariya tana goye da ummi kamar jaririya, tana jijjigata tayi bacci.
Sallamarsa kawai ta iya amsawa, daga haka ba ta sake kula shi ba.
"Ya jikin ummin?"
"Ba sauƙi" ta faɗa kai tsaye. Ta je ta kwantar da ummi a kan katifarta da ke ƙasa, ta koma falo kan kujerar da ke ɗakin ta zauna. Da yake ɗakin babba ne sosai, suka raba shi biyu da labule ya zama kamar ciki da falo.
"Ba sauƙi fa ki ka ce maman ummi?"
"Ina sauƙin yake bashir? An yi wa ƴa ta rauni na har abada, waye zai auri ummi ya riƙe ta da amana, alhalin an binne gaskiyar abun da ya same ta tun a lokacin da ya faru, ɗan gata ya ci bulus, koda yake dama an ce ba zata auru ba, saboda muninta, da wanne ummi za ta ji? Wallahi ɗaukar ƴa ta zan yi na bar gidan nan, garinmu zan koma, ko kare Allah ya bani ina so, balle ɗan adam" Ta ƙarasa tana sheshsheƙar kuka.
Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta, idon sa ya tara hawaye ya ce "Haba maman ummi, ya zan yi, iya uwata ce, dole na yi mata biyayya, idan ki ka tafi da ummi ku ka bar ni, in zauna da wa? Ina son ku wallahi dan Allah kar ki yi mini haka, ummi kuma ba abun da zai hanata auruwa in sha Allah, dan Allah kar ki tafi ki bar ni"
Kallonsa ta yi, har cikin zuciyarsa yake maganar, wani irin tausayin sa ya kamata, har ga Allah yana iya ƙoƙarin sa a kan su, mahaifiyar sa ce ta hana su zama cikin kwanciyar hankali.
Ta kwanta a jikinsa tana kuka, rarrashinta ya din ga yi, yana yi mata magiyar, ta taya shi ya yi wa iya biyayya, ya san ba zasu taɓe ba, kuma rayuwar ummi ba zata wulaƙanta ba.
Abun ka da mata da miji, haka ya lallaɓata ta janye batun yin yajin, har ya fara ƙoƙarin shiga wani abun daban.
Iya ce ta faɗo ɗakin tana faɗin "Wai balarabe ba ka ji ana kiran salla bane, ka shige ka ƙule a ɗaka da mace" a razane mariya ta yi gefe, tana kare jikinta.
"Eh iya yanzu zan tafi masallacin ma dama, dam..dama... Yanzu aka kira sallar"
Ayshercool.
08081012143
  Â
            *CUTARWA!*
Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube Cool hausa novels
What's app 08081012143
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)
3
Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya.
"Ina jin duk abun da ku ke faɗa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna ɗin mana, ta ƙara gaba, wataƙila dama ita ce ƙashin tsiyar da ta tokare maka ƙofofin arziknka, har ni zan gindaya umarni, ka zo kana lallaɓata? Ki tafin mana waye ya riƙe ki? Ke idan ƴar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da ɗa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ƙabilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ƴaƴana dafa'i, asirinku bai isa ya kama ni ba"
Ba yau iya ta saba yi musu laɓe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba.
Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba.
Baban ummi ne ya yi ta bata haƙuri, mariya kuwa ta haɗe rai, wani abu mai ɗacin gaske na kaiwa da komowa a ƙirjinta, ji take kamar ta tashi ta ɗurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba ɗaya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu ɗaya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuɗi.
Bayan sun samu ta fita, ya leƙa ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa "Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani"
Ya ce "Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ƙoƙarin neman fili a garin nan, na gina mana ko ɗaki ɗaya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci.
Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun duniya, ba zata taɓa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta.
A zahiri kuma ta ce "To Allah ya yassare" ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita.
***
Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daÉ—i wasu marasa daÉ—i, sai dai lokaci ya wuce ba tare da É—aci da raÉ—aÉ—in abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba.
Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance.