← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 134

Sashe 119

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka gaisa, ƴan mazan nan da ba su taɓa zuwa gidan ummi ba, suka din ga mamaki ganin uban gidan da ummi take ciki.

Suka fake da yi wa ummi ya jiki, sannan kawu Ilyasu ya ce "Ummi, dama zuwa muka yi mu nemi afuwarki a kan abubuwan da suka faru a baya, dan Allah ki yi haƙuri, iya ma ta ce a baki haƙuri, sannan dan Allah ki taimaka mana da batun gidan nan, wallahi idan muka tashi bamu san in da muka dosa ba".

Dr. Ya ce "Neman yafiyarta ku ka zo ko kuma neman alfarma?"

"Duka, dan Allah yaron kirki ka saka baki, dan Allah a dube mu mun yi Æ´aÆ´a da jikoki, bamu san ina zamu je ba, a taimaka mana dan girman Allah"

Hashim ya yi murmushi ya sunkuyar da kai, ya tuna lokacin da mariya idan iya ta guma mata tayi kuka, ta ce in Allah ya yarda sai sun nemi alfarmar ummi.

Raihan ya ce "To ai ni bani da ta cewa, ni da na sai gida, ummi na sayawa ba kaina ba, dan haka gida nata ne ba nawa ba, kuma ni ban san me ku ka yi mata ba, ba zan tursasa mata ba"

"Ummana, ki yi magana mana" dr. Yayi maganar yana kallon ta.

Hawaye ya ƙwace mata ta ce "Kawuna duk abun da ka yanke shikenan"

"A'a Ummi, ba zan takura miki ba, ki samu lokaci ki yanke hukuncin da ki ke ganin ya dace sai ki tuntuɓe ni, alfarma ɗaya zan nema musu, a bar su a gidan kan ki yanke hukuncin"

Ta jinjina masa kai, tana share hawaye.

"Ke mai haƙuri ce da juriya, kuma haƙurin ne ya kawo ki wannan matakin, ni shaida ne an zalunce ki ummi, kin fuskanci ƙalubale a rayuwar ki mai tarin yawa, amma ki yi haƙuri, ba a canza tuwo suna, ko ba kya so dangin mahaifinki ne, ki yi haƙuri ko kin ɗauki fansa ba zaki huce ba" ta jinjinawa dr. Kai cike da borin kunya, suma suka cigaba da ba wa ummi haƙuri.

Sun raka su za su tafi, dr. Ya ja ummi gefe, ya ƙara yi mata nasiha sannan ya ce "Mamana zaki iya tuna wata magana da ki ka gaya mini shekarun baya, da zamu tashi daga tsohon gidanmu?"

Ummi ta É—an yi shiru ta ce "Wace maganar kawu?"

"Da ki ka ce ina ma na gyara tsohon gidan, in an ga in da mamanki take ku zauna tare a ciki"

Ummi ta yi murmushi ta ce "Kawu lokacin ai har da ƙuruciya"

Yayi murmushi ya ce "Yanzu fa?"

"An girma" tayi maganar da Æ´ar dariya.

"What if, hakan ta kasance?"

Ummi ta É—an rausayar da kai ta ce "Da na yi murna mara misaltuwa, ni kaina da zai yiwu da na dawo da ita gidana, amma ga yanayin yadda nake zaune da uwar mijina kar na janyo mana gori".

"No ba wannan ba, auren mamanki nake son yi, zan gyara mata tsohon gidana na sakata a ciki"

Ummi ta waro ido tana kallon dr.

"Ya dai mamana, ko baki ji daÉ—i ba?"

"Kawu, amma...Anty fa?"

"Babu ruwanki da ita, abun ne ya faɗo mini na ce bari na ɗan tuntuɓe ki"

Ummi ta faÉ—aÉ—a murmushinta ta zube a kan gwiwoyinta ta ce "Kawu da ka gama yi mini komai, dawo da mama kusa da ni, Na amince É—ari bisa É—ari, Allah ya sanya alkhairi "

Ya ce "Tashi maza, bana son wani ya san me ake ciki, ai lokacin da na ganota ma, na yi niyyar hakan iya ta hana, amma a wannan karon abun da farida tayi miki, ya sanya na ƙara ganin muhimmancin hakan. Na fara magana da baba ma, da kuɗin aure da sadaki da komai rana ɗaya za a kai a ɗaura, ina ga da ita zan tafi Uganda, in ƙarasa karatun tana tare da ni"
Idan ummi ta fahimta dai-dai, kamar da haka dr. Yake son hukunta farida.

"Allah ya ba da iko kawu, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi, na gode sosai da sosai"

Dr. Ya ce "Menene na godiyar kuma? Duk abun da ya dace za a yi wa gidan, zan turo miki kuÉ—i ki yi sayayya a zuba a ciki kan mu dawo, a sati biyun nan da suka rage mini, za'ayi komai da yardar Allah"

Ummi ta din ga murna, take duk wata damuwarta ta ji babu ita, saboda tsabar zumuÉ—i ta iske raihan a bedroom ta rungume shi tana murna.

"Ikon Allah, daga kuka zuwa farinciki bani labari, meyafaru?"
Nan ta kwashe komai ta gaya masa, ya taya ummi murna sosai da sosai.

Yadda Alhaji ya É—auki zafi, yayi fushi da mami, har tsoron tunkararsa take yi, da maganar auren raihan, ya daina kulata ya daina cin abincinta, kuma ya hanata zuwa É—akinsa.

Tana kitchen tana tsiyayar tea, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, kawai ta ga Salim a kitchen ɗin. Sai da ta razana dan bai taɓa yi ba.

"Na ji kin je har gida, kin sake cin mutuncin matar raihan, kina zaton ita ta gaya wa Alhaji kin saka an saketa, to ba ita ba ce ba, ni na gaya masa, dan tun bayan lamarin ya faru na sani.
A yanzun ma ba ita ta gaya mini ba, ina da CID na da ke gaya mini komai, kin san wani abu kuwa, duk kasancewata makakke kamar yadda ki ke faÉ—a duk wanda yake mutunta uwata mutum ne mai kima a idona.
Dan haka ba zan bari É—an uwana ya cutu ba dan kina babarsa, kuma ba zan bari yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba ta cutu.
Kin san wani abu, ina amfani da raihan, wurin rama cin mutuncin da ki ke yi wa uwata, na fuskanci a duniya masoyinki ba ya gaban raihan, kamar yadda yake ji da wanda yake ƙaunar matarsa, dan haka zan taya ɗan uwana son abun da yake so, idan kuma ki ka cigaba da matsawa zaki yi biyu babu, gargaɗi nake yi ba shawara ba" sakin baki mami ta yi tana kallon Salim, me yake nufi da biyu babu.

Kamar ya san me yake zuciyarta ya ce "Zaki rasa soyayyar ɗanki, dan a yanzu yana yi miki kallon wadda ba ta son farincikin sa, kujerar da yake kai ma zaki yi masa dalilinta, dan na san yadda ki ka ƙallafa rai a kanta, raihan ya ɗauki kuɗin Alhaji ya sayawa matarsa gida, idan ki ka cigaba da takura yarinyar nan, za ta yi abun da ba kya zato" ya juya ya fice daga kitchen ɗin.

Jikinta har rawa yake yi, ta fara tunanin da gaske raihan ya É—auki kuÉ—i ya sai wa ummi gida ba tare da izinin Alhaji ba?.

Bazama ta yi sashin Alhaji, yana tare da Hajiya ta shiga babu ko sallama ta ce "Alhaji, da gaske raihan ya É—auki kuÉ—i babu izininka ya sai wa matarsa gida?".

Alhaji ya kalleta ya ce "Eh"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abun da nake gaya maka ko? Shiyasa na ce fa ya rabu da ita"

"Rufe mini baki, ba ke ki ka sanya ya saketa ba, ke ai gashi kin ce ya ƙara aure ya ce ba shi da kuɗi ya sai wa matarsa gida, kuma kuɗi nawa suka ɗauka ba ruwanki da wannan, kuma ban ce ki saka baki a kan maganar ba, tun da ni mai kuɗin ban yi magana a kai ba"

Kawai Hajiya ta kwashe da dariya.

Farida tana ta murna, dr. Bai ce mata komai ba tsawon kwanaki, ya sanya ta saki jiki ta cigaba da sabgoginta, noor kanta ta san zancen auren dr. Amma ta yi shiru ba ta gaya wa farida ba.

Da daddare ta shirya tana jiran dawowarsa, tun safe tana kiran wayarsa shiru bai É—aga ba, tun da ya fita da safe bai dawo ba.

Shigowa yayi cikin manyan kaya, da gani ka san a gajiye yake, ta bishi É—aki tana tambayar sa ko lafiya.

Ya zube mata goro da alawa, ya ce "lafiya ƙalau ga wannan an ɗaura mini aure yau a Maiduguri"

Ayshercool
08081012143

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi 
Man garan gashi 
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702   08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
CUTARWA!

AYSHERCOOL

(BRIGHT PENS)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

46

PAID ADVERT
Chapter 119 · 0% Book details