← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 134

Sashe 77

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manager ya zare ido ya ce "Yayarta ka za a kora? Idan ban koreta ba ni ai yayana ya kore ni, ka san yadda yake yabawa ƙoƙarin ta, da yabawa amanarta"

Raihan ya ce "Dan Allah ka bar wannan maganar, kawai ni dai taimakon da zaka yi mini kenan, ka ce lallai ta dawo aiki.

"Ba zan yi ba, ba kun fi kusa ba"

Raihan ya sassauta murya ya ce "Haba manager, dan Allah ka taimaka Please"

"Da ka ce ba ka ji? Zan yi mata magana, amma ba dan halinka ba, kuma ba zan ce zan wani koreta ba, zan dai yi ƙoƙarin ta dawo ɗin"

Raihan yayi dariya ya ce "Allah ya bar mini manager"

Manager kawai yayi murmushi, ya cigaba da aikin da yakamata ace ummi ce ta yi.

Sai dai manager bai kai ga yin hakan ba, washegari sai ga ummin ta zo aiki, sai dai ta rame sosai, kallo É—aya zaka yi mata ka san akwai tashin hankali a fuskar ta.

Manager ya kira raihan a waya, ya gaya masa ummi ta zo.

Bai ja dogon lokaci ba, ya daidaici lokacin tashin ta ya kusa, sannan ya tafi.

Ta fito daga wurin aikin, yana nesa kaÉ—an da ita yana kallonta, tana tafe a hankali kamar mara lafiya.

Zuwa yayi ya sha gabanta da motar, ta tsaya tana kallon motar, ya sauke glass É—in motar suka haÉ—a ido, sai da ta É—an razana, ya buÉ—e mata motar ba tare da ya ce mata uffan ba.

Jikin ummi ya yi sanyi sosai da ganin raihan, dan ba ta taɓa tsammani ba, kamar mai jin tsoro haka ta ɗosana ta shiga motar.

"Ta tabatta dai ba kya so na ko ummi? Kina iya rabuwa da ni, baki damu da halin da zan shiga ba, kin ce mu rabu, ko nema na baki sake yi ba, rashin muhimmancina har ya kai haka kenan ko Salma?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Shikenan, ni gashi na sake biyo ki ai, ranar lahadi Alhaji zai zo wurin dr."

A razane ta kalleshi, tana ƙifta ido.

"Eh, mun haɗu da dr. Shekaranjiya, na zo wurinki kin ƙi ɗaga wayata, mun yi magana ya ce Alhaji ya zo su yi magana"

"Wai da gaske aurata zaka yi?" Tayi maganar cikin matuƙar rauni.

"Gashi ina gaya miki, kin zata da wasa nake yi? Na san wataƙila ba ni ne irin mijin da ki ke so ba, na san zaki ga na yi miki yarinta da yawa, amma har cikin raina nake jin zan iya aurenki na riƙe ki da kulawa da girmamawa".

"Raihan zaka aureni ina bazawara"

"Kar ki sake kawo mini maganar kin taɓa aure, zuciyata zata fashe, ummi kina wasa da son da nake yi miki kina ganin kamar wasa ko? Hubban shadidan na kira shi, ban taɓa jin damuwa da takura a kan son wani abu ba kamar ke, kawai in ganki a kusa da ni, shi zai kawo mini cikakkiyar nutsuwa"

Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta.

"Meya rabaku da tsohon mijinki?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Kakarmu ce ta haÉ—a auren, ba ya so na, an kai kuÉ—in aurensa aka fasa, shi ne ya aure ni"

Ya ce "Ya yi wa kansa, ni ina so. Ki saka aurenmu a addu'a salma, in sha Allah zai yi albarka, wata nawa ki ke so a saka na ji kin ce a matse ki ke ko?"

"Ai wannan maganar dr. Ba tawa ba"

Ya ce "Haka ne, nima na matsun ne, in ga kin zama tawa" ummi dai ta yi shiru tana tunanin ko dai ba da gaske raihan yake ba.

"Na ga gidan tv nan sun kira screening, manager ya ce mini kin je, ya ku ka yi da su?"

Ta É—an rausayar da kai ta ce "Kyawawa suke so, ba wanda sai an ta saka musu filter ba"

"Kamar yaya kenan?"

"Haka mai wurin ya ce"

Kawai ta ga yayi parking É—in motar, ya kalli ummi ya ce "Ke kuma ki ka ce masa me?"

Tayi shiru tana kallon sa.

"Magana nake yi miki?"

"Ni ban ce komai ba"

Raihan ya ce "Sai ki ka tsaya kina kuka ko? Gwanar kuka"

Ta ce "A'a ai ban yi kukan ba"

Ya danƙo kunnenta ya ce "Wallahi ummi, duk wanda ya kuma kushe mini ke, ki ka tsaya kina kallonsa, baki ɗau wani mataki ba, sai na huce a kan ki, kamar na fi ki jin takaici idan aka kushe mini ke. Ke kina da baki, amma ba zaki iya magana ba? Tun da ba aikin zai ɗauke ki ba, sai ki wanke shi tas ki bar wurin, atleast ai kya ce masa Allah ya sa kyawawan su durƙusar da tashar, ko ki ce masa ya koma islamiyya a karanta masa Allah ne mahalicci"

Sosai ya riƙe mata kunne, ta kai hannu ta riƙe hannunsa da ya riƙe mata kunnen cikin muryarta mai cike da iyayi da shagwaɓa ta ce "Babba ne fa"

Ya sakar mata kunnen ya ce "Babban banza ba, tun da ba shi da hankali"

Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "My wife"

Ta ce 'Na shiga uku"

"A'a ko ɗaya baki shiga ba, ko ba ni ki ke so ba, dan Allah ki yi haƙuri mu karɓi ƙaddara a yadda ta zo mana, bamu san dalilin da Allah ya sa ya haɗa mu ba, kar taurin kanki yayi delaying zuwan wasu bayin Allah duniya" tayi burus kamar ba da ita yake magana ba.

"A haka kamar saliha, nan kuwa taurin kai a cikin ki kamar me".

Ranar lahadi gaba ɗaya dr. Ya manta da batun zai yi baƙi, dan ya faɗi maganar ne dan ya kori raihan, ummi ma ta kasa zaune ta kasa tsaye, dan raihan ya tabattar mata da ranar lahadin Alhajinsu zai zo.

Ƙarfe sha ɗaya na safe, Abdul ya je ya sanarwa dr. Yayi baƙi.

Ya fita ya ga manyan mutane a manyan motoci, suka gaisa, Alhaji Tahir ya ce "Ka manta zaka yi baƙi ne? Kodayake ƴan boko sai kun bawa mutum lokaci yake zuwa, Tahir ne baban sirikinka Muhammad da ka ce kana son ganina".

Dr. Ya ce "Subhanallah, Allah sarki bisimillah ku shigo"  suka bi bayan dr. Zuwa cikin gida.

Har cikin falo, ya fita da sauri ya samu Abdul ya bashi kuÉ—i, ya ce ya sayo musu ruwa da lemuka.

Sun daɗe suna hira da Alhaji Tahir, da wasu mutane su biyu ɗaya ƙaninsa ɗaya abokinsa.

Dr. Ya sha mamakin jin waye raihan, tare da yi wa ummi fatan, Allah ya sa ƙarshen wahalarta ne ya zo.

Nan Alhaji Tahir yake gaya wa dr. Tuni ya saka an gama yi masa bincike a kan ummi, kuma ya ji daÉ—in sakamakon binciken, dan haka ko yanzu aka ce su bayar da kuÉ—in aure dr. Ya yanka za su biya, idan kuma shima zai yi bincike a kan su tukuna shikenan.

Dr. Ya ce "Eh to, ina son a bani damar binciken tukuna, sannan kamar nan da sati biyu zan yi magana, saboda in kira wasu daga ƴan uwana a karɓi kuɗin auren"

Alhaji Tahir ya ce "Babu laifi, Allah ya kaimu"

Ba tare da wata alkunya ba, suka ci abin da dr. Ya gabatar musu, suka yi masa godiya suka tafi.

Farida ta din ga bin sa tana tambayarsa suwaye wannan baƙin, amma yaƙi gaya mata ko suwaye.

Ummi ta sha mamaki, ba ta zaci da gaske ba, sai da ta ga su Alhaji Tahir sun zo.

Alhaji Tahir ya koma gida, ya kira mami sashinsa, Hajiya na tare da shi, sai dai bai gaya mata ba ita ma, sai da Mami ta zo, ta tarar da su ta wani haÉ—e rai tana harare-harare.

Alhaji Tahir ya ce "To ke fa abun arzki ya same mu, ban sani ba ko mun yi laifi"

Mami ta ce "Meyafaru?"

"Babban mutum ya zo mini da magana, ya je zance an ritsa shi an ce in je in gabatar da kaina idan da gaske yake, dan yau ma daga can nake da ni da su Alhaji Hamza, nan da sati biyu zamu koma mu kai kuÉ—in aure"

"Ikon Allah, kuma shi ne ba a saka ni a maganar ba sai yanzu?"

Hajiya ta ce "Masha Allah lallai babban mutum an girma, Ubangiji Allah ya sa abokiyar arziki ce, Alhaji a ina take zan yi shishshigi"

Alhaji Tahir ya ce "Au kema babbar aminiyar ta sa bai gaya miki ba? Wai wata yarinya amm.. ammi ne sunan nata ne ko ummi ne, wai ƙawar maryam ce dai".

Hajiya ta ce "Laaa ko dai Ummi, Ummi dai da suka yi islamiyya tare?"

Ya ce "Yes of course haka ya ce mini"

Cikin tsananin mamaki da takaici mami ta ce "What! Wannan kwazgwamar yarinyar baƙa ƙirin?"

Ayshercool
08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
Chapter 77 · 0% Book details