← Book details Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 134

Sashe 80

Cutarwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce "To, ya gida ya office?" murmushin yayi ya ce "Ita ce hirar da ki ka fi so take yi miki daÉ—i kenan?"

Ta jinjina kai alamar eh.

"Office aiki ya yi yawa ba hutu"

"Ina su Yaya sagir? Kun shirya kuwa?"

Raihan ya ce "Mun shirya, amma ba ya kulani"

"To kai ka din ga kula shi mana ai kai ne ƙarami"

Ya ɗan shafi sajensa ya ce "Gayen nan ɗan wulaƙanci ne fiye da tunaninki, yanzu sai ya yarfa ni, har gara Salim wasu lokutan"

"Ai gani za su yi kamar idan suka sakar maka fuska zaka raina su, ka cigaba da jan su a jiki, kar ka nuna musu ƙyama saboda abun da suke yi watarana sai labari, ka gayyace su cikin ayyukan kamfaninku, ko ba ka sakar musu komai ba, ka ja su a jiki sosai".

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Gaskiya ne, sai ma kin ga hajiya, ta fi bani tausayi wallahi, tana iya yin ta a kansu, amma kullum kamar ana tura su dawa, amma zan yi ƙoƙari in yi abun da ki ka ce in sha Allah"

"To Allah ya baka iko"

Ya amsa da amin, "Bari na je, zani wani wuri zo mu je ki karɓi saƙon ki"

Ya tashi ya yi gaba ta bi bayansa, a jikin babur É—in sa suka tsaya, ya kalleta ya ce "Alhaji ya ce na zo na fara gini, a wace unguwar ki ke son mu zauna? Sannan wane irin gida ki ke so, flat ko mai bene?"

"Kowanne ka yi shikenan, Allah ya yassare"

"Salma kenan, haryanzu kina doubting idan ni zan aure ki, kuma ko zan iya riƙe ki, abun da muke shirin yi ba zunubi bane ba, hasali ma yana da asali a addinin musulunci, dan haka ki manta da batun al'ada da surutun mutane kin ji sweetheart"

Ta jinjina masa kai, tana wasa da hannun babur É—in.

"Salma" ya kira sunanta a hankali, ta É—aga ido ta kalle shi.

"Ina sonki sosai saboda Allah" tsigar jikinta ta tashi, ta kawar da idonta gefe.

"Ko sau ɗaya ki gaya mini wani abu mai daɗi da zai bani ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar neman aurenki, dan nima ina fuskantar ƙalubale"

Jiki a sanyaye ta ce "Dan Allah raihan ka yi abun da zaka zo ka cutu daga baya, ka ƙara tunani a kai".

"Ni na riga na roƙi Allah a kan lamarin nan, kuma shi so baya bayar da ƙofar tunani, ba abu ne da yake bamu damar yin shawara ba, ki tausaya mini ummi" jikinta yayi sanyi, wani irin tausayin su ya kama ta.

"Ban san me zan ce ba, zan yi mana addu'a iya yi na, Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi"

Ya ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum. Gobe in Allah ya kaimu ki yi mini girki dan Allah, zan biyo ta wurinku na ci"

"Me ka ke so" tayi maganar tana murmushi.

"Ke nake so"

Ta yamutsa fuska ta ce "Ina nufin me zaka ci?"

Yayi dariya ya ce "Abinci mana, ko me ki ka dafa zan ci da yardar Allah" yayi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa ya ce "Ki koma gida ki huta, duk da ban gama ganinki ba, zamu yi waya, dan Allah kar ki kashe waya kin ji baby"

Ta karɓi ledar ta juya tana murmushi.

Sabuwar waya dalleliya raihan ya gwangwaje ummi da ita, irin wayar da ba ta taɓa zaton zata riƙe irinta ba, bakinta ya ƙi rufuwa sai da ta kira shi ta yi tayi masa godiya, ya ce shi ba godiya yake so ba, kawai ta ce masa tana son sa shi zai sa ya ji daɗi ya tabbatar da ta ji daɗin kyautar da yayi mata.

Aikuwa ta yi gumm, ta kasa magana.

Da kuɗinta tayi cefane, washegari da safe ta sheƙa masa girki, bai kira ta a waya ba, sai fita tayi ta ganshi a waje yana jiranta.

Suna tafe yana yi mata normal hira, tare da nuna mata yadda za ta yi amfani da wayar da ya saya mata.

A mota ya ci abinci, yana ci yana yi mata hira, ta buÉ—e ruwa ta bashi, ta duba jakarta ta É—aukko tissue, ta warwro masa ta bashi ya goge hannu.

Yayi murmushi ya ce "Ka ga mace ta gari, ta fara aikinta tun yanzu".

Ta haÉ—a kan kwanukan ta ta ce masa "Sai anjima, Allah ya kiyaye"

"Amin ya rabb, yakamata mu koma ayi siyayya, mayukan nan kamar sun karɓe ki, na ga kina ta glowing"

Da sauri ta ce "Fari na yi?"

"A'a kyau ki ka ƙara, ban sani ba ko idona ne"

"Kar ka saka mu makara, sai anjima" ta fice daga motar, ya zuba mata ido, har ta shige shagonsu, sannan ya ja motar ya tafi.

Duk wata hanya da mami za ta bi, ta rusa maganar auren raihan, abu ya gagara ta kaÉ—a ta raya, amma raihan ya dage, ya samu goyon baya É—ari.

Dr. Ya sanar da su kawu Ilyasu, zai karɓi kuɗin auren ummi, dan haka mutum biyu daga cikin su su zo ranar juma'a.
Hatta kayan soye-soye da zai karɓi baƙi, daga waje ya yi order abun sa, dan sai saura ƴan kwanaki, sannan ya gaya wa farida.

Farida ko a jikinta, tana ganinsa yana ta shige da ficensa shikaÉ—ai, ya shirya komai.

Kafin sallar juma'a, su kawu Ilyasu suka zo gidan, bayan sallar juma'a, su Alhaji Tahir suka zo.

Bayan gama tattaunawar da duk yakamata, dr. Ya gabatar da su kawu Ilyasu ga su Alhaji Tahir, tare da gaya musu matakin karatun ummi, tare da tabattar musu da binciken da yayi a kan Raihan, bai samu wata matsala ba.

Alhaji Tahir ya sake gabatar da kansa ga su kawu Ilyasu.

Sannan ya kalli dr. Ya ce "Ban sani ba ko kun yanke kuÉ—in aurenta da sadakin?"

Dr. Ya ce "A'a, duk abun da Allah ya sa ku ka bayar, zamu karɓa fatanmu ubangiji Allah ya sanya alkhairi"

Alhaji Tahir ya jinjina kai, sannan ciro kuÉ—i a aljihunsa ya ajiye kuÉ—i dami guda a tsakiyar falon, ya ce "Ga su nan, dubu É—ari biyar ne, mun saka watanni huÉ—u idan Allah ya sa zamu gani, amma idan kuna ganin mun saka da yawa kuna iya ragewa".

Dr. Yayi murmushi ya ce "Bamu nemi ƙari ba ma nemi ragi? Allah ya nuna mana"

Kawu Ilyasu ya ce "Amma ranka ya daɗe har naira dubu ɗari biyar, kun kuwa san yarinyar nan bazawara ce? Kuma auren da ba a tsauwwala almubazzaranci ba yafi albarka, bazawara ce ta taɓa aure shekarun baya".

Ayshercool
08081012143

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books É—ina, da free pages duk akwai a kan watpad account É—ina. Irinsu
Abduljalal
Wata kissar sai mata
Wuta a masaƙa
Cutarwa
Ƙanwar maza
Gaba da gabanta
Aƙidata
Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata.
08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi.
Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta
Sandal
Halut
Irik
Difur
Gab Gab
Kajiji
Habil
Nabak
Humra
Kulakcha
Dilke da kalta
Kayan
Garan jiki
Muna turara
Kaya
Kujerar garan jiki
Kannada
Madarorin turare masu kamshi
Man garan gashi
Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche
Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!*
*INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*.
*BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAÆŠAÆŠÆŠUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU*
*MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.
                          *CUTARWA*

33
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

33

Tsit suka yi gaba É—aya, suna jiran abun da Alhaji Tahir zai ce, dr. tamkar ya nutse saboda takaicin abun da kawu Ilyasu ya yi.

Alhaji Tahir ya yi murmushi ya ce "Ɗan uwa, ita bazawara ba mutum ba ce ba da ba za a kyautata mata ba? Shi ya ga yana son ta ai, ni mutum ne mai matuƙar ƙaunar ƴaƴana duk abun da suke so, sai ya saɓa wa addini ne zan ce a'a, amma dan bazawara ce ba shi yake nufin a aureta a wulaƙance ba"
Chapter 80 · 0% Book details