← Book details Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 124

Sashe 96

Ali Dan Tsoho Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

manneta a ƙirjinshi, ya nufi ciki. Ko ina jama'a tamkar ba shabiyun dare, ba samari da ƴan mata harma da matan auren ƴaƴan turawa sai cashewarsu sukeyi, baƙar fatar batata yawa sosai. Tinda Kamal ya nufo wajan da Mubina rungume jikinsa, maza da mata suka zuba masu idanu cike burgewa. Daga cikin mazan turawan kuwa sosai ƴar balarabiyar yarinyar ya burgesu, yanda ta narke jikin Kamal yatsarshi a cikin bakinta tana cicizawa, idanunta a rufe. Kamal babu wanda ya kalla a cikin mutanan harda masu tafa masu. Yana isowa kofar room ɗinsu, Makel dake tsaye ya buɗe masa kofa ya shige. Makel yace"Good night sir friend."Kamal yace"Night thanks so much."ya faɗi yana murzawa kofar key ya zare, ya nufi kujerun parlon. Sai lokacin Mubina ta buɗe idanuna, ta sauke kan Kamal wanda yay tsaye yana kallonta. Yatsar ta cire daga bakinta, ta zumburo baki ta fara ƙoƙarin sauka daga jikinsa, tana cewa "Ni saukeni nayi abinda ya kawoni na wuce."Kamal bai musaba ya sauketa ƙasa. Tako nufi bedroom ɗinsa, da kallo ya bita. Table ɗin falon ya kalla yaga yanda Makel ya jera masa kome, kama daga kajin amarcin drinks frech milk yoghourt da sauransu. Mubina kuwa tana sanyo kanta cikin bedroom ɗin wani fitinannan ƙamshi me sanyaya zuciya ya kaima hancinta farmaki, ta lumshe idanunta ta buɗe, tana kallon yanda gadon ya ƙawatu da shimfiɗa, ga wasu mahaukatan riguna nan na bacci. Shiga dube² tayi babu inda bata leƙaba har bathroom ƙasan gado ba kowa a ɗakin, ajiyar zuciya ta sauke, ta fito. Kamal na tsaye ya harɗe hannunsa saman ƙirjinsa, kai ta kauda ta nufi kofar fita. Kamal ya ƙira sunanta cikin wata irin shigeyar murya. Cak ta tsaya cikin tsiwa tace. "Meye to muje ka ajiyeni gida." isowa yay ya rungumeta ta bayanta yace"Ok amman ki temaka min na ciyar dake kema ki ciyar dani sai na muje na ajiyeki."Baki ta turo tace"Banaci naci indomie ai juyota yayi suna face ɗin juna."Hannunta ya kamo yana murzawa ya tsareta da shegun idanunsa, cikin shagwaɓa ya mareeece yace"Sweetie don Allah fa nace, wlh inada yunwa zo ki temakamin naci abunci sai na maiyar dake."Mubina duk tsikar jikinta ke mimmiƙewa, saboda yanda yake murza mata tafin hannunta da yanda yake magana, sai wani irin abu takeji yana ratsa duk wata gaba ta jikinta. Ƙwace hannunta tayi tace"To muje."Cikin farin ciki ya isa gun table ɗin, ya zauna. Mubina ma zama tayi nesa dashi, tana kallon kayan, matsowa yayi dabda ita ya yago ƙatuwar cinya ya bata yace. To cinyeta bari nima naci."Ya faɗi yana yagar cinyar kazar. Mubina kin ci tayi ta ajiye. Kamal ya ɗauki cinyar da ta ajiye ya rungumota yace"Wallahi Sweetie idan baki cinye wannan ciyar ba zaki kwana ana fa." Fuska ta ƙwaƙwaɓa tace"Kamal" yace"Na'am haaaa bakinki."Dole ta buɗe bakinta ya shiga bata naman kazar ya rungumeta tsam ƙirjinsa, yana mata wayo saida tacinye katuwar cinyar nan tas ba tare da ta ankare ba. Robar yoghourt guda ya bata cikin siyaya tasha fiye da rabi, ya buɗe fresh milk itama ya dura mata, drinks ne da zai bata ta fashe masa da kuka tace"Kamal amai zanyi na ƙoshi."Manneta yayi yace. "Ok Sweetienah sorry bari kukan bana son kukanki, bari nima naci nawa kafin naki ya ratsaki sai na mayar dake gida ko?" A shagwaɓe ta ɗaga masa kanta, ta ɓoye kanta cikin ƙirjinshi, tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Ɗago da kanta yay a hankali ya kirata" Sweetienah". Bata amsaba ta turo baki idanunta a lumshe gazar² ɗin gira idanunta ta kwanta luf saman idanun nata. Kamal murmushi yay ya fito da harshensa ya ɗora saman bakinta yana lashe mata bakinta da duk inda maiƙon kaza da yoghourt da suka ɓata mata bakinta. Mubina tayi luf abinta bata hanashi ba saima sanyin harshensa dake ratsa mata sassan jikinta. Kamal ya cire harshen nasa ya dauki kazarsa yanaci, yana shan yoghourt. Sosai yaci naman kazar yasha fresh milk ga yoghourt da yasha yayi gyatsa yace. "Alhamdulillah"! Ya faɗi yana ƙoƙarin mikewa da Mubina ta zame ta koma gefe,tace"To muje ka kaini gida."ta faɗi tana gyatsa dan ba ƙaramin dura Kamal ya mataba. Kamal yace"Ok Sanyin idaniyata kinyi sallar isha kuwa?" hararasa tayi tace"Eh tin yaushe ko cemaka akayi bana salla kan lokaci ne?" Kamal yaje ya wanko hannunsa ya dawo ya kama hannunta tana tirjewa ya nufi bedroom da ita. Kuka ta saka masa tace"Ban gane me kake nufi daniba kalli ƙarfe ɗaya ne saura na dare, amman kana so ka maidani ƴar iska ace har yanzu ina waje..." Kamal yace"Wlh matata ba ƴar iskaba ce nine sheda, narigada nacema ummi fa kin tafi gidansu Kausar can zaki kwana, kalli ma wayarki tace abaki idan zaki ƙira Majeed yazo ya maidaki, kawai muyi kwanciyarmu, kinga da safe sai na kaiki gidansu Kausar ɗin sai ki ƙira Majeed ɗin yazo ya maidake gida." Mubina tace "Nashiga uku wayyo ni dai bazan kwana ba da ƙato." Kamal ya kama hannunta yace"Eh daman gadon zan barmiki ni sai na koma parlo ya kuwa xan kwana d aƙatuwa nima, kin yarda?" Hararasa tayi cikin tsiwa tace"To wacece ƙatuwar ni ba matarka ba ce yo"Ta faɗi a sangarce. Kamal ya danne dariyarsa yace"Ok kin yarda ni mijinki ne? Amman kike so na koma parlo?" Kai ta ɗaga tana ƙwace hannunta. Kamal yace to naji muyi sallah sai na koma falon nayi kwanciyata, zanfi ma sakewa, jeki dauro alwalla muyi sallah mu kori shaiɗan." Bata musaba ta shiga toilet wanke bakinta tayi da brush ɗin Kamal ta ɗauro alwalla, ta fito. Kamal bai mata magana ba ya shiga ya ɗauro alwalla bayan yayi brush ya fito. Ya shimfuɗa masu darduma. Yace"Oya zo nan." tana turo baki ta iso ta hau kan darduma ta tsaya. Murmushi yayi ya tayar da kabbara sallah. Raka biyu ya jasu, suna gamawa ya fara kwararo Addu'o'i na godiyar Allah ya kuma basu zaman lafiya shida matarsa. Ya kamata kanta ya mata Addu'a fur taki ta miƙe tana cewa. "Yo aljannai gareni? Tashi kawai ka fita malam bacci zanyi." ta faɗi tana nufar saman gadon ta cire hijabin jikinta. Kamal kusan suman zaune yayi ganin yanda rigar tayi mugun kamata hips ɗinta da ƙirjinta kama zasuyi magana, gata dai ƴar siririya amman akwai kyan halitta. A zabure ya miƙe yace"Sweetie kiyi wanka mana kiji daɗin bacci." Banza ta masa ta haye gadon ta shige cikin blanket ɗin da take bada wani irin sansanyan ƙamshi. Kamal toilet ya shige ya sheƙo wanka, ya fito ɗaure da towel. Mubina kuwa baccin har ya fara dukanta bata ma san ya fito ba. Ganin haka yasa Kamal yayi shirin baccinsa cikin sanɗa, bayan ya shafe jikinsa da lotion masu ƙamshi da taushi, ya gyara sumar kansa, ya dauki kayan baccinsa ya saka ya feshe jikinsa da turaruka masu daɗin gaske. Ya fice parlon ya kwashe yoghiurt ɗin da frech milk da drinks ya saka a fridge,ya kashe wutar parlon ya dauko kwalin drinks ya buɗe yasha sosai ya mayar ya ajiye ya nufi bedroom. Cikin sanɗa ya iso bakin bed ɗin ya kashe wutar ɗakin ya hauro saman bed ɗin ya kwanta a hankali, matswa yayi dab da ita yace.
Chapter 96 · 0% Book details